✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Muhideen ya nemi a mara wa Buhari

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhideen Bello ya yi kira ga al’ummar Najeriya su sake zabar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na Musulmi a zabe…

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhideen Bello ya yi kira ga al’ummar Najeriya su sake zabar Shugaba Muhammadu Buhari a matsayinsa na Musulmi a zabe mai zuwa ,kamar yadda suka yi wa tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo a matsayinsa na Kirista a wancan lokaci.

Shaihin malamin ya ce Shugaba Buhari ya cancanci a sake zabensa domin cike sauran shekaru 4 a Ofis. “Wani Shugaba Kirista (Cif Olusegun Obasanjo) ya yi shekaru 8 a Ofis. Yanzu ya kasance Buhari Musulmi ne ya kamata dukkanmu mu yi masa irin yadda muka yi wa Obasanjo domin shi ma ya yi shekaru 8 a Ofis.”

Sheikh Muhideen Bello ya yi wannan hasashe ne a ranar Talata a cikin Lakcar da ya gabatar a wajen bikin Maulidin Annabi na bana da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Oyo dake Agodi a birnin Ibadan.

“Dukkan surutai da bangaren masu hamayya suke yi masa, shugaban yana yin iya kokarinsa kuma ya cancanci a sake zabensa ya zarce,” inji Malamin. Da yake magana dangane da dan takarar kujerar Gwamna da Jam’iyyar APC ta tsayar a Jihar Oyo wato Cif Adebayo Adelabu, sai Shaihin Malamin ya ce “tabbas ya kamata al’ummar Jihar Oyo su zabi wannan mutumi a zabe mai zuwa domin ya kammala kyawawan ayyukan cigaban kasa da Gwamna Abiola Ajimobi ya fara.”

A game da kalaman rashin sanin addinin da dan takarar yake yi dake bazuwa a Jihar, sai Sheikh Bello ya tabbatar da cewa Adelabu musulmi ne. Tun da farko cikin jawabinsa Gwamna Abiola Ajimobi roko ya yi ga al’ummar jihar su yi koyi da karantarwar da Fiyayyen Talikai Annabi Muhammadu (SAW) ya yi wajen soyayya da kaunar juna da zama lafiya. Ya yi kira ga ‘yan siyasa su daina yin bakaken kalamai a tsakaninsu musamman a daidai wannan lokaci da aka kada gangar fara yakin neman zaben 2019 dake gabatowa.

Gwamnan ya tunatar cewa cigaban al’umma yana samuwa ne idan akwai zama lafiya a tsakaninsu. A nan sai ya ce “kafin ayi zaben fidda gwani na APC a Jihar Oyo na yi ta rokon Allah Ya fitar mana mutumin kwarai mai tsoron Ubangiji (TWT) a matsayin dan takarar Gwamna kuma ga shi Allah Ya amsa rokon ya samar mana irin wanda muke so da muke fatan zai yi nasara a zabe mai zuwa,” a cewarsa.