✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 20 da Rasuwar Shata: Waiwaye kan tasirin tauhidi da mu’amula a rayuwarsa (2)

Da Allah bai kawo wa Shata dauki da Jarman Kano Muhammadu Adamu Dankabo ba da ya samu nakasu da wulakanci daga maroka a shekara 10…

Da Allah bai kawo wa Shata dauki da Jarman Kano Muhammadu Adamu Dankabo ba da ya samu nakasu da wulakanci daga maroka a shekara 10 na karshen rayuwarsa. Da sun yi masa dariya, kan yadda karshensa zai kasance.

Saboda ba ya da lafiya a 1998 a Kazaure a lokacin bikin sabon Sarki Alhaji Najib Husaini Adamu, Shata na kwance a masauki da safe sai Abdu Wazirin Danduna ya yi masa sallama don samun na cefane. Ko da jin muryar Danduna, sai Shata ya yi karfin hali ya yi wuf ya tashi daga kwance ya fizgo babbar riga ya sanya cikin hanzari, sannan ya zauna bisa kujera kamar ba abin da ke damunsa. Ya ce a ce masa ya shigo. Ya shigo, suka gana, har ya ba shi babbar riga mai asake da Naira dubu biyar.

Shata ya yi ta fama da maroka munafukai kuma mahassadansa. A gabansa su nuna su masoyansa ne, amma ba su kaunarsa a boye. Abin nan da Hausawa ke cewa ‘ka ga mutum a fuska Annabi Musa amma a zuci Fir’auna.’ Tauhidi da yawan nuna ikon Allah da yarda da Allah su suka ceci Shata daga hannun makiyansa maroka.

Tun daga farkon zamaninsa da maroka suka lura da irin baiwar da Allah Ya yi masa ta musamman ce, suka shiga yi masa asirrai da sammu iri-iri don kada ya yi tashin gwauron zabon da ya yi. Daga karshen rayuwa kuma abokan gaba da Shatan ya faskare su suka zura idanu su ga yaya rayuwarsa za ta kare. Shin zai mutu cikin halin wulakanci ko cikin rufin asiri? To sai ga shi Allah Ya ba su kunya, ba su samu yadda suke so ba.

Kafin rasuwar Shata, duk wani ubangidansa sai da ya halarci Sallar gawarsu. Ma’ana, duk kusan iyayen gidansa sai da suka rasu sannan shi ya rasu daga baya. Ga su nan birjik, kamar su Usman Liman Sarkin Musawa (1939), Sule Musawa (1936), Isan Torobi (1940), Magajiyar Musawa (1940), Inuwa Mammada Ketare (1940), Sulen Jebu Jos (1959), Sheriff Mamuda Kano (1955), Sheriff Sidi Kano (1955), Jabbi Danfulani Jos (1960) (ba na Kaura Namoda ba), Doki Dankaroni Guru (1954), Sule Jikan Korau (1948), Makaman Katsina Idris Nadabo (1943), Sardauna Gamji Dankwarai (1962), Sulen Garo (1960), Balan Gwaggo (1965), Iro Mai ’Yankunne Sakkwato (1965), Waziri Ibrahim (Shugaban GNPP; 1978), Sarkin Fawa Dan Gawan Kano (1957), Kwasau Kaura (Kakan Sahabi Liman Kaura) (1952), Alin Katako Maiduguri (1960), Abu Dan Lagai-Lagai (1956), Haruna Kasim Kano (1955), Maude Tabako (1962) da sauransu.

Marigayi Alhaji Adamu Dankabo sutura ce babba, kuma uba ne ga zakin mawaka Shata. Duk addu’o’in da makadin ya yi ta yi a cikin wakokinsa da nuna tauhidin da ya yi ta yi (ba ma dai a cikin wakokin Bakandamiya wadda take uwar wakokinsa): ‘Allah don Allah Allah’ da kuma ‘…ya ji ya yarda…’. Ko kuma da ya ce: ‘…da yadda na ce Mai Jallah.’ Bugu da kari, akwai wurare a Bakandamiya kuma da yakan ce: ‘Ka raba mu da mahassada Allah, don girman zati.’ Yakan kuma ce: ‘Da kanKa na hada Ka Allah, ban hada Ka da kowa ba Allah, Ka yi mani don girman zati.’ Yakan kuma ce: ‘Na dai gane maroka tsorona suke ji, to ku tafi na yafe ku, na daina batunku ’yan tselen uwan nan.’ Duk a cikin tauhidi yakan ambaci: ‘…don yau da gobe ta Allah ce, jibi, gata fa, Mamman ta uban wace ce, fada masu duk ta Allah ce, har citta, na san haka, sai yaya?’ A ci gaba ne yakan ce: ‘….ya zo man ya sa baki, ya ci durin uwa shi…’ da sauransu.

Gaba dayan Bakandamiya waka ce ta tauhidi da neman Allah Ya raba Shata da sauran mawaka lafiya, kada fitinar sammace-sammace da asiransu su iso gare shi ko kuma idan sun iso kada su yi tasiri ko aiki a kansa. Su mawaka sun san haka, shi ma Dodo ya san dalilan da suka sanya ya rika nuna tauhidi ga Allah, don ya gama lafiya.

Muna iya cewa saboda Shata ya fi sauran mawakan kasar Hausa nuna tauhidi da tsananin nuna godiya ga Allah a cikin wakokinsa ya sanya Allah Ya dada fifita shi a tsakanin sauran ’yan uwansa mawaka. Muna da labari, a wasu lokutan kuma a kan idanunmu ta faru cewa wadansu mawaka ko maroka sun karasa rayuwarsu cikin halin kaico. Wadansu sun rasu ba sutura, wadansu sun rasu ba rigar kirki, wadansu sun karasa rayuwarsu ba su da gida, wadansu sun gama rayuwa a gidajen haya, wadansu sun gama rayuwarsu ba su da lafiya – ba magani ba kudin magani kuma babu wani mataimaki wanda zai tallafi rayuwarsu su gama lafiya. Addu’ar Shata a wakokinsa ce Allah Ya karba Ya turo masa Dankabo domin ya taimaka masa. Dankabo ne ya yi ta daukar dawainiyar Shata har zuwa karshe.

Dankabo ya bugi kirji ya dauki nauyin zuwansa waje don neman magani a tsakanin Nuwamba 1998 zuwa Maris 1999. Kafin wannan lokacin kuma da makadin ya kwanta rashin lafiya, shi ya sanya aka kai shi wani asibiti na alfarma a Kano, ya dauki nauyin komai har ya warware, cikin 1998 ke nan.

Hakazalika da kuma ciwon ya dada ta’azzara, Kabo ya aiko ya ce a kai shi Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. A nan, har Galadiman Kano ya aika a kau da Shatan a kai shi wani asibiti na musamman a nan dai Kano, sai Kabo ya ce ai kasar waje ma za a mayar da shi. A ranar Juma’a da ake sa ran biza za ta fito kuma a tafi da Shata waje, a ranar sai Allah Ya yi naSa iko, Allah Ya yi masa rasuwa.

Ka ga a nan, babu rufin asirin da ya wuce wannan. A dauki nauyin makadi kamar wani Shugaban Kasa, a yi ta tarairayarsa, in ban da Shata babu mai wannan gatancin. Kafin rasuwarsa da shekara 7, duk fadin Funtuwa ba mai irin motarsa. A lokacin, duk fadin Jihar Katsina babu wanda ya mallaki mota kirar bambalasta. Daga Shata sai Garba Ja Abdulkadir. Ba wani abu ba ne duk arzikin Dankabo ne, tunda shi ya ba da ta. Bayan ma ita cikin Fabrairun 1999 ya ba da karin wata motar, mai suna C-Class.

Tun Kabo na ba Shata kujerun Makka duk shekara, kama daga kujera 15, 35, ko abin da ya gaza ko dara hakan, sai da ta kai ga Dankabo ya ajiye jirgi a wata shekara, ya ce wa Shata ‘duk ma wanda kake da shi ka kawo shi ya shiga a tafi da shi.’ Ka ko san ko a masu kudi a kasar nan, yana da wahalar gaske mutum ya samu wannan gatanci. To shi Shata ya samu daga wajen Jarma. Zamanin da Kabo ke ba Shata kujerun Makka masu yawa (1989 zuwa 1998), dududu kudin kujera guda, babbar kujera ba ta wuce Naira dubu 45 ba. Wa ke da ita? Sai dai wane da wane, ko da a birnin Kanon Dabo.

Duk wanda ya rika ya samu daukaka a duniya ba inda yake son zuwa bayan Makka da Madina sai Amurka. To karshe dai har Amurka Kabo ya kai zakin mawaka. Tun a tsakiyar zamaninsa, Shata ke son zuwa Amurka amma iyayen gidansa na baya ba za su iya daukar nauyinsa ba, irin su Wili Dan Tijjani (1968) sai daga karshe Kabo ya zo ya kai shi.

Idan muka koma ta fuskar wakoki, yau shekara 20 daidai da barinsa duniya amma kamar ma bai rasu ba. Kullum ga wakokinsa nan ana ji ana kuma bincike a kansu. Har yanzu ruwa na wankin dauda, wakokinsa sun kasance gurabe na bincike a kan al’adar Malam Bahaushe har gobe. Alhamdu lillahi, ga inuwoyi nan barkatai a kan Mamman Shata domin ciyar da al’amuransa da wakokinsa gaba.

Mu’amullarsa da mutanensa mai kyau ce. Mutane da yawa sun tabbatar Shata karimi ne, kuma duk wata sabga ta duniya, a yi ta da shi saboda yana da halin dattaku kuma yana girmama manya. Mutane irin su Alhaji Sani Bello Dagacin Falgore kuma surukin makadin sun tabbatar da hakan. Yana matukar girmama na gaba da shi. Ba ya raina mai ba shi. Sani Gadagau Madawakin Magana na Sarkin Zazzau (Ba-ka-toshi) ya ce wanda duk ka ga ya bata da Shata har ta kai Shatan ya yi fushi da shi, to laifin na wancan ne, ba na Shatan ba. Kuma haka maganar take. Duk wanda ya zama ubangidan makadin, to in dai Allah Ya ja kwana da mutum ya samu karayar arziki, za ka tarar Shatan ke taimaka masa. Ya taimaka masa da abinci, abin jan jari, ya kuma ba shi mota ko motoci na hawa ko na neman arziki. Ko bai yi maka ba, idan ma mutum ya rasu to zai yi wa dan da mutum ya haifa. Shata na da wannan hali.

Ya dace a kafa wata cibiya da za ta tattara ko adana dukkan abubuwan da suka shafi Shata. Don kada sha’anin makadin ya bace a cikin tarihi. Hakika, a yau waka ta kare, ko kuma ta shiga cikin maraici, tunda mawaka masu hikima da azanci sun kare. Ko wane ne kai kuma ko daga wane bangare na duniya ka fito, ba ka yin waka ko ka yi wakoki masu yawa kamar na Shata. Bilhasali ma, a cikin wakokin Shatan mawakan duniya ke diba suna gina nasu wakokin. Kashi 95 na mawakan Najeriya a kasar Hausa duk dibar wakokin Shata suke yi suna gina nasu, suna karawa da tasu basirar.

Dokta Kankara malami ne Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma

za a iya samunsa ta:

imel:[email protected] (07030797630)