Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Shekara 20 na dimokuradiyya a Najeriya:  Kuka ’yan Najeriya za su yi ko dariya?

Shekara 20 na dimokuradiyya a Najeriya:  Kuka ’yan Najeriya za su yi ko dariya?

A shekaranjiya Laraba, 12 ga Yuni aka gudanar da bikin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya, wacce a  shekara 20 da suka gabata daga 1999 ake gudanar da ita a ranar 29 ga Mayu na kowacce shekara.

Wannan babban biki da aka yi a Babban Birnin Tarayya, Abuja, ya zo daidai da shekara 20 da komowa ga mulkin farar hula, bayan sojoji sun rike madafun iko na shekara 16 daga 1983 zuwa 1999, in ban da wasu watanni uku da Cif Ernest Shonekan ya yi rikon kwarya daga ranar 26 ga Agusta zuwa 17 ga Nuwamban 1993; lokacin da tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha ya sake kwace madafun iko, kuma ya yi mulki daga ranar 17 ga Nuwamban 1993, zuwa ranar 8 ga Yuni, 1998, lokacin da rai ya yi halinsa.

Bayan rasuwar Janar Abacha ne, Janar Abdulsalami Abubakar ya dare kujerar shugabancin kasa, sa’annan ya shirya zabubbuka cikin kankanen lokaci, ya kuma mika madafun iko ga ’yan siyasa.

A ranar 29 ga Mayu, 1999, Jamhuriyya ta Hudu ta fara aiki, bayan Shugaban Soji na lokacin, Janar Abdulsalami Abubakar ya mika mulki ga Cif Olusegun Obasanjo, wanda a baya ya taba shugabancin Najeriya a karkashin mulkin soji.

Bayan kammala mulkinsa kashi na farko a shekarar 2003, a karkashin Jam’iyyar PDP, Shugaba Obasanjo ya kara takara a karo na biyu kuma ya samu nasara bayan da ya kayar da abokin hamayyarsa, Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), wanda ya yi takara a karkashin tsohuwar Jam’iyyar APP, don haka ya zarce da mulki har zuwa shekarar 2007.

A lokacin da zai kammala mulkinsa ne bayan shekara takwas, Cif Obasanjo ya so ya yi tazarce karo na uku, amma hakan bai yiwu ba, bayan ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa tare da wadansu manyan ’yan siyasa irin su Atiku Abubakar, suka yi fatali da wani kudiri da aka so a yi amfani da shi wajen canja tsarin mulki don cimma waccan bukata.

Ganin haka ne sai Shugaba Obasanjo ya tsayar da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa a matsayin dan takarar Jam’iyyar PDP a zaben 2007, inda ya ci zaben, bayan ya kayar da Buhari a zaben da aka yi zargin tafka magudi.

Shugaba ’Yar’aduwa ya rasu bayan wata doguwar jinya, kwanakin kadan ya cika shekara uku a kan karagar mulki, wato daga ranar 29 ga Mayu, 2007 zuwa 5 ga Mayu, 2010.

Daga nan ne Mataimakinsa, Dokta Goodluck Jonathan daga yankin Neja-Delta ya haye kujerar mulki, ya kammala sauran shekara daya da ta rage, ya sake takara a shekarar 2011 ya ci zabe, sa’annan a shekarar 2015 ya nemi ya sake takara amma Shugaba Muhammadu Buhari mai ci yanzu, wanda ya yi takara a karkashin Jam’iyyar APC, ya kayar da shi.

Shugaba Buhari ya sake samun nasara a karo na biyu, bayan ya kayar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda ya yi takara a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga Fabrairun bana.

To amma maimakon Shugaba Buhari ya gabatar da kudirorinsa a ranar 29 ga Mayu, wato ranar da aka rantsar da shi karo na biyu, sai ya ce ba zai yi hakan ba sai ranar 12 ga watan Yuni, wato shekaranjiya Laraba.

An samu canjin Ranar Dimokuradiyya ce saboda kudirin da Shugaba Buhari ya mika ga Majalisar Dattawa, inda ya nemi a rika gudanar da Bikin Ranar Dimokuradiyya a ranar 12 ga Yunin kowace shekara, domin tunawa da soke zaben da aka yi a 1993, wanda aka ce marigayi Cif MKO Abiola tare da Ambasada Babagana Kingibe ne suka yi nasara amma tsohon Shugaban Soji, Janar Ibrahim Babangida ya soke.

’Yan majalisar daga bisani sun amince da kudirin, shi kuma Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kai. Kuma a ranar 12 ga watan Yunin, Shugaba Buhari ya yi bayanai da dama a gaban Mataimakinsa Yemi Osinbajo da sabon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan da sabon Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila.

Shugabannin kasashe da dama ciki har da na Rwanda da Saliyo da Ghana da Namibiya da Nijar da Kongo da Laberiya da Gambiya da Gini Bissau duk sun halarci bikin. Mataimakan shugabannin kasashen Sudan ta Kudu da Uganda da Zimbabuwe da Masar da wakilan shugabannin kasashen Jamhuriyyar Binin da Ikwatoriyal Gini da Gabon da Jamhuriyyar Chek da Faransa da Ireland da Japan da Mali da Kenya da Moroko da Malawi da Baljiyem da sauransu, duk sun halarci bikin.

Sai dai kuma babu wani tsohon Shugaban Najeriya da ya halarci taron, in baya ga jiga-jigan jam’iyya mai mulki ta APC, kamar Sanata Bola Tinubu da gwamnonin jihohin Kano da Kogi da Yobe da Kwara da Kebbi da Ekiti da Kaduna da na Jihar Anambra, wanda dan jam’iyyar hamayya ta APGA ne.

Ra’ayi ya bambanta kan yanayin tafiyar

A bayanin da ya gabatar a wurin bikin, Shugaba Buhari ya bayyana cewa hakika an samu ci gaba a Najeriya, ta hanyoyi da dama, kamar yaki da cin hanci da rashawa da dakile ta’addanci da kuma daukar matakai domin farfado da tattalin arziki. Ya yi alkawarin bayar da mukamai ga sababbin jini a zangon mulkinsa na biyu da daukar mataki a kan wadansu ’yan siyasa da shugabannin kabilu da na addinai, wadanda ya ce su ne kanwa uwar gamin fitinun da ake fama da su a kasar nan.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin samar da miliyoyin ayyuka ga jama’a kuma ya ce za a kammala sama da kilomita 2,000 na hanyoyi da ake ginawa a fadin kasar nan, tare da samun hanyoyin da za su bude karkara da makarantun firamare da sakandare; haka ya ce za a kara bayar da kudade domin fadada hanyoyin jirgin kasa da gyara hanyar sufurin jirgin ruwa da sauransu.

Sai dai kuma mutane da dama sun shaida wa Aminiya cewa lallai akwai sauran aiki a gaba. Sun ce akwai abubuwan alheri da dama da aka samu a shekara 20 da suka gabata na mulkin dimokuradiyya.

Masanin shari’a, Ibrahim Yusuf ya bayyana cewa Najeriya ta samu kudade masu dimbin yawa a shekara 20 da suka gabata. “Kwarai, an yi facaka da arzikin kasa a karkashin Jam’iyyar PDP, wacce ta rike madafun iko na tsawon shekara 16, to amma akwai abubuwa da dama da suka yi,” inji shi. “Ka ga an kara samun jami’o’in karatu, kusan kowacce jiha tana da Jami’ar Gwamnatin Tarayya kuma ga wayar tafi-da-gidanka, da sauransu. Sai dai abin da ke sosa mini rai shi ne, ’yan siyasa sun gurbata tarbiyyar al’umma, domin kusan komai za a yi yanzu sai an hada da maganar addini ko kabilanci; kuma miliyoyin matasa ba su da aikin yi. Dalilin da ya sa laifuffuka irin su ta’addanci da rikicin Fulani makiyaya da manoma da Boko Haram da garkuwa da mutane da sauransu, suka yi yawa a cikin al’umma,” inji shi.

Shi kuma Injiniya Yabagi Yusuf Sani, wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP), kuma dan takarar Shugaban Kasa a zaben da ya gabata, ya bayyana wa wakilinmu cewa an samu ci gaba sosai a Najeriya a cikin shekara ashirin da suka gabata.

“Babban kuskure ne a ce mulkin siyasa bai haifar da komai ba. “Babu wani sha’ani na dan Adam da za a ce ba za a samu matsala ba. Sai dai ni na so a ce siyasar Najeriya ta samu gindin zama sosai bayan shekara ashirin amma kuma hakan bai samu ba. Har yanzu idan ka kula akwai abin da Hausawa ke kira ‘ungulu da kan zabo,’ domin tun daga kan Obasanjo, marigayi Umaru ’Yar’aduwa (saboda yayansa Shehu Musa) da Buhari, duk suna da alaka da mulkin soji. Jonathan ne kadai dan siyasa, shi kuma ya tsinci mulki ne a kasa. Don haka ina fata nan ba da dadewa ba za a samu cikakkun ’yan siyasa su dare kan madafun iko,” inji shi.

A wani babban taro domin nazarin shekara 20 na mulkin dimokuradiyya a Najeriya da Cibiyar Nazarin Ci Gaban Dimokuradiyya (CDD) ta gabatar a Abuja, tsohuwar Ministar Ilimi kuma ’yar takarar Shugabar Kasa, Dokta Oby Ezekwesili ta bayyana cewa tilas a yi maganin kashe-kashen da ake yi in har ana so siyasa ta ci gaba.

“Hakika abin tir ne ganin yadda har yanzu jihohi da kananan hukumomi ba su iya tabuka komai domin samar da abubuwan more rayuwa ga miliyoyin al’ummarsu, sai dai kowane karshen wata su taho Abuja su karbi kasonsu na kudaden da Gwamnatin Tarayya ke rabawa, su koma gida su yi kashe-mu-raba,” inji ta.

Shi ma Mataimakin Babban Editan Jaridar Daily Trust, Malam Mahmud Jega, wanda ya yi bayani a wajen wannan taro, ya ce idan har aka bar masu garkuwa da mutane da masu kwanton bauna da ’yan ta’adda suka ci gaba da kashe mutane babu gaira babu dalili, to miliyoyin ’yan Najeriya za su yi tofin Allah-tsine ga mulkin siyasa.

Ita kuwa Shugabar Cibiyar CDD, Idayat Hassan cewa ta yi duk da an samu kalubale a shekara ashirin da suka gabata, ya kamata ’yan Najeriya su yi sam barka. “Ni ina da yakinin cewa za mu iya gyara Najeriya. Binciken da muka gabatar ya nuna cewa ’yan Najeriya suna so a ci gaba da yaki da ta’addanci da cin hanci da rashawa, kuma suna so a gyara tattalin arziki. Haka yawancin mutanen da suka kai shekara 60 a duniya suna bukatar a samar da hanyoyin kiwon lafiya masu inganci,” inji ta.

A wani taro da aka gudanar kan ‘Al’amarin 12 ga Yuni’ a Legas,’ Sanata Shehu Sani ya yi kiran a yi kwaskwarima ga tsarin dimokuradiyya a Najeriya. Ya ce dole a gyara tsarin tafiyar da ake yi, domin a samu ci gaba mai dorewa. “Lallai ya kamata mu daina kau da kai a kan abubuwan da suke faruwa; tilas mu zauna mu ga wane irin gyara za a yi domin abin kunya ne a ce jihohi da kananan hukumomi sai sun je Abuja a karshen kowane wata sun yi maula.

Duk da haka Sanata Sani ya yi kira ga ’yan Najeriya su jinjina wa Shugaba Buhari, wanda shi ne ya mayar da 12 ga Yuni ta zamanto Ranar Dimokuradiyya, bayan shekaru da dama.