✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 20 na mulkin dimokaradiyya: Ci gaba aka samu ko koma baya?

Najeriya ta cika shekara 20 ana mulkin dimokaradiyya babu yankewa, kuma an yi gwamnatoci da dama da suka shude wajen mulkar kasar bayan dawowarta kan…

Najeriya ta cika shekara 20 ana mulkin dimokaradiyya babu yankewa, kuma an yi gwamnatoci da dama da suka shude wajen mulkar kasar bayan dawowarta kan tafarkin mulkin farar hula a 1999. Wakilanmu sun jiwo mana ra’ayoyin jama’a kan ci gaba aka samu ko koma bayan hakan:

Babu wani ci gaba da aka samu – Habibu Mai Kifi Wudil

Daga Muhammad Aminu Ahmad

“Babu wani ci gaban da aka samu, idan aka kwatanta da yawan asarar rayukan bayin Allah da aka rika yi a kasar nan, tun shigowar mulkin dimokuradiyya har zuwa yau da ta cika shekara 20 ana yin ta a wannan kasa tamu. Domin komai ci gaban da aka samu, ai ba ci gaba ba ne, muddin al’umma na cikin jimamin yadda rayuwarsu take, saboda babu tsaro, wanda kuma shi ne ginshikin ci gaban kowace kasa.”

An samu ci gaba – Munkaila Muhammad

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

“An samu ci gaba sai dai akwai kura-kurai da ya kamata a gyara. Ci gaban da aka samu shi ne kowane dan kasa ya samu ’yancin fadin albarkacin bakinsa, amma a wani lokaci kuma hakan na jawo matsala da sai an kiyaye. Kura-kuran da za a gyara su ne ’yan Najeriya su kula da irin mutanen da za su zaba idan zabe ya zo don su ne za su kawo ci gaban idan ba haka ba ci gaban zai zama ba ya da amfani. Sannan a rika yi wa shugabanin addu’a, maimakon suka da zagi.”

Ba wani ci gaba da aka samu – Babangida Usman Mai Atamfa

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

“Ba a samu wani ci gaba a shekara 20 na dimokuradiyya ba, saboda babu wadataccen ruwan sha, ba wutar lantarki ba asibitoci kuma babu hanyoyi.

Gaskiya ba a cimma burin da ake bukata ba, domin kasashe da yawa da aka ba mu ’yancin kai tare kuma muka fara siyasa tare sun yi gaba sun bar mu a baya.

Sai shugabanni sun sa tsoron Allah a ransu kafin a samu ci gaban da ake nema amma yanzu kam babu, domin ana bukatar kamfanonin da za su samar wa da jama’a ayyukan yi.”

An samu walwala da fadin albarkacin baki –Tasi’u Danlami

Daga Adam Umar, Abuja

“Talaka ya samu ci gaban walwala da fadin albarkacin baki a mulkin dimokuradiyya. Mutane da yawa sun samu abin hannu saboda kudi na yawo a tsakanin jama’a fiye da na da. Abubuwan hawa ko kayan daki a da sai wane da wane, ga sauran abubuwan ci gaba irinsu wayar salula. Sannan a yanzu idan wata al’umma tana da wani korafi za ta iya zuwa har wajen shugabanninsu su koka musu kai-tsaye, ga kuma wakilai da suke da su a majalisun jihohi da na tarayya. Sabanin lokacin soja da sai yadda aka yi da ku.”

An samu ci gaba kwarai da gaske – Alhaji Yahya Dauda

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

“A gaskiya ina ganin tsarin dimokuradiyya ya samu ci gaba kwarai da gaske a cikin shekara 20 da farawa. Wayewar jama’a a kan siyasa baki daya da ’yancin fadin albarkacin baki da ’yancin zaben dan takara suna daga cikin ci gaban dimokuradiyya a Najeriya wanda babu irin haka a baya. Damar fadin albarkar baki ta yi tasiri kwarai a cikin tsarin dimukradiya.” a Najeriya.

An hada duka biyu – Abdullahi Sulaiman

Daga Adam Umar, Abuja

“A ganina an samu ci gaba a wasu al’amuran da kuma koma baya a wasu. A fuskar ci gaba an samu bunkasa a abubuwa irin su tituna da makarantu da filayen saukar jiragen sama da sauransu a wasu wurare, sakamakon kamfe da ’yan siyasa suka yi da wadannan abubuwan a lokacin neman a zabe su da  neman wani wa’adi.  Sai dai fa an samu koma-baya a bangaren tsaro idan aka kamanta da zamanin soja ga kuma almubazzaranci da dukiyar gwamnati maimakon a yi aiki da duk abin da aka samun kasancewar mai ya kara daraja ga kuma wasu sababbin hanyoyin kudin shiga.”