✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 4 da mutuwar Jackson: Masoyansa sun yi bikin tunawa da shi

A ranar Talatar da ta gabata ce shahararren mawakin zamani, Michael Jackson ya cika shekara hudu cur da mutuwa, inda masoyansa da dama suka yi…

A ranar Talatar da ta gabata ce shahararren mawakin zamani, Michael Jackson ya cika shekara hudu cur da mutuwa, inda masoyansa da dama suka yi bikin tunawa da shi ta hanyoyi daban-daban.
A kasashe da dama, masoyan Michael sun yi ta sauraren wakokinsa, musamman ma dai ‘Thriller’ wakar da wasu ke ganin ita ce bakandamiyarsa. Wasu kuma sun yi ta kallon wasanninsa ta akwatunan talabijin, kamar yadda wasu kulob-kulob kuwa suka yi ta sanya wakokinsa, a yayin da matasa ke nanata salon rawarsa.
Ga masu tu’ammali da intanet kuwa, a ranar ta Talata, cikin awanni goma na farkon ranar, an samu maziyarta shafinsa na musamman, sama da mutum miliyan hamsin; kamar kuma yadda aka samu fiye da wannan adadi, da suka nuna sha’awarsu ga wasu daga cikin wakokinsa da ke Youtube da sauransu.
A yayin da masoyan marigayin ke ta wadannan bukukuwa na tunawa da gwarzon nasu, ita kuwa mahaifiyarsa Katherine Jackson, an same ta tana cikin alhini, inda take jin takaicin yadda wasu suka mayar da mutuwar dan nata wata kafa ta samun abin duniya. Haka kuma an ruwaito yadda take takaicin yanayin da dan nata ya mutu, wanda haka ya sanya ake ta tufka shari’a da likitansa Dokta Conrad Murray.
Ta bangaren ’yan uwansa da danginsa kuwa, tun bayan mutuwarsa, ba su samu sukuni ko natsuwa ba. Mutuwar tasa ta hada wasu daga cikinsu rigima kan dukiyar da ya bari. Sai dai ana jin cewa ’yan uwansa hudu, Jackie, Jermaine, Marlon da Tito, wadanda su ne tun farko suka kafa kungiyar ‘Jackson 5’ tare da marigayin a farkon kuruciyarsa, za su gabatar da wani wasa na musamman a jibi Lahadi, domin tunawa da shi.
Ya zuwa yanzu dai, an yi ittifakin cewa faifan marigayi Michael Jackson mai taken ‘Thriller’ wanda ya fitar tun a 1982, shi ne faifan da ya fi kowane sayuwa a fadin duniya. A kullum kara cinikinsa ake yi miliyan bayan miliyan.
Kafin rasuwarsa a ranar 25 ga Yuni, 2009, Michael Jackson dai ya samu lakanin ‘Sarki,’ abin da ke nuni da cewa kamar shi ne sarkin mawakan duniya. Irin yadda masoyansa suka yi ta alhininsa da kuma yadda suka yi ta sauraren faya-fayaensa, wannan ya nuna yadda za a dade ana tunawa da shi a duniyar mawaka.