✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 45 a gadon sarauta: Sarkin Zazzau ya roki gafarar al’umma

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya roki jama’a su yafe masa idan ya saba musu ko ta hanyar aiki ko hulda da saninsa…

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya roki jama’a su yafe masa idan ya saba musu ko ta hanyar aiki ko hulda da saninsa ko cikin rashin sani.

Mai martaba Sarkin Zazzau ya yi wannan roko ne a wajen taron bikin cikarsa shekara 45 a gadon sarautar Zazzau.

Sarkin ya kuma roki jama’a su taya su addu’a ga sarakunan Zazzau da suka rasu tun daga Malam Musa har zuwa kan wanda ya gada Alhaji Muhammadu Aminu.

Sarkin, ya kara  yaba wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan gyaran hanyoyi daga Abuja zuwa Kano da gwamnatinsa ke yi.

Mai martabar ya yi amfani da wannan dama ya kara tuna wa Shugaban Kasar halin da  Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya wanda ke fama da rashin na’urori na zamani da rashin isassun kudi don gudanar da ayyukan kula da lafiyar jama’a.

A sakon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a wajen bikin, wanda ya samu wakilcin Ministan Kula da Muhalli Alhaji Mahmoud Abubakar, ya ce Sarkin Zazzau dan kishin kasa ne kuma jagoran zaman lafiya, don haka ya shawarci Sarkin ya kara tabbata a kan kyawawan halayen da aka sanshi da su na kasancewa mai kaunar al’ummar suka fito daga bangarorin kasar nan.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i, ya yaba ne da irin shawarar da Sarkin ya ke ba su, tare da shan alwashin cewa in Allah Ya so zai kawo ziyara shi da abokan aikinsa domin  gani da kuma tantance duk wata bukata da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello ke da ita don mika wa Shugaban Kasa bukatun Sarki kasncewar asibitin shi ne jagoran duk wani asibitin da ke Arewacin kasar nan.

 

Rasuwar Sarki Aminu a 1975

A 1975 ne Allah Ya yi wa Sarkin zazzau Alhaji Muhammadu Aminu rasuwa a Ingila, inda bayan gama juyayin rasuwarsa, sai aka umarci masu zaben Sarki su gaggauta zabe don fito da sabon Sarkin Zazzau. An samu mutane daga kowane gidan sarauta da ake da su a masarsutar da  suma nemi wannan sarauta a lokacin.

Sarki Shehu Idris, shi ne mutum na karshe da ya fito neman sarautar kuma shi ne mafi karancin shekaru a cikin ’yan takarar wanda hakan ya jawo jayayya a tsakanin masu zaben Sarki dangane da shekarunsa.

 

Yadda aka zabe shi Sarki

A wancan lokacin an sanya Malam Muhammadu Jumare a matsayin wakilin gwamnati don gudanar da wannan zabe, kuma ya zo da ka’idoji da gwamnati ta tsara a kan masu zaben Sarki wadanda suka hada da Wazirin Zazzau Alhaji Nuhu Yahaya da Fagacin Zazzau Alhaji Muhammadu da Makaman Zazzau Alhaji Haliru da Limamin Juma’a Malam Muhammadu da kuma Limamin Kona Malam Balarabe. Kuma ka’idojin da aka mika wa masu zaben Sarkin, sun hada da:

Na farko duk wanda za a zaba Sarki, sai ya kasance bai taba yin wani laifi wanda hukuma ta hukunta shi ba.

Na biyu; ya kasance ya taba rike, ko yana rike da matsayi na sarauta ko hakimci.

Na uku; ya kasance yana da ilimin zamani gwargwado.

Na hudu; ya kasance ba mai yawan shekaru ba ne.

Na biyar; kuma a tabbatar da ya fito daga daya daga cikin gidajen sarautar Zazzau.

Bayan sun gamsu da wadannan ka’idoji ne sai aka ci gaba da tattaunawa a kan maganar zabe, inda kowa ke kawo nasa gwanin ana ba shi dama ya yi bayani a kansa game da irin ayyukan da ya yi da irin iliminsa da kuma halayya na rashin saba doka.

Haka kuma akan ba da dama ga wani ya soki ra’ayin wani dangane da wani abu na aibi da ke tare da wannan mutum da ya zaba.

Haka dai aka yi har aka kawo kan Alhaji Shehu Idris, inda daya daga cikin masu zaben Sarkin, ya tashi ya fadi irin abubuwan da ya yi wadanda suka kunshi iliminsa zuwa mukaman da ya rike ba tare da wani laifi ba, kuma shekarunsa sun kai yadda ake bukata, kuma ga shi ya goge a kan sha’anin mulkin jama’a. Daga nan sai wakilin gwamnati ya tambaya ko akwai jayayya a kan wannan bayani da wannan mutum ya yi? Nan aka samu ’yar jayayya kadan wadda ba ta yi tasiri ba.

A cikin wurin zaben sai aka samu wani ya ce ya goyi bayan mutum na farko a kan bayanin da ya yi a kan Mai martaba Sarkin Zazzau. Daga nan sai aka sake samun goyon bayan wani, har saura suka yarda a kan haka.

Bayan gama zabe, sai wakilin gwamnati ya shaida wa masu zaben Sarki cewa an tanadi horo na musamma ga duk mai zaben Sarki da ya fadi abin da aka tattauna game da zaben ko ya fada wa wadanda aka zaba har sai gwamnati ta fada wa jama’a sunan sabon Sarkin da aka zaba.

Har ila yau akwai Majalisar Sarakuna wadda ta ke karkashin gwamnatin Arewa ta Tsakiya a lokacin inda (Mai martaba Sarkin Katsina) ke rike da shugabancinta a lokacin.

Wannan majalisa ta kunshi sarakunan Katsina da Daura da Zazzau da Jama’a da Kagoro da Jaba da Marwa da Kwai. Dukkansu sun ba da goyon baya a kan zaben da aka gudanar a Masarautar Zazzau, kuma sun yi na’am da zaben da aka yi wa Alhaji Shehu Idris.