✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 46 ina da almajirai amma ba sa yin bara – Sheikh Abubakar Bafulatani

Sheikh Abubakar Bafulatani shi ne ya kafa makarantar allon nan ta Sa’adatul Abadiya a garin Jos, shekara 46 da suka gabata.  A tattaunawa da wakilinmu,…

Sheikh Abubakar Bafulatani shi ne ya kafa makarantar allon nan ta Sa’adatul Abadiya a garin Jos, shekara 46 da suka gabata.  A tattaunawa da wakilinmu, ya ce tunda ya bude makarantar, almajiransa ba su taba yin bara ba. Kuma ya ce malamai za su iya karantar da almajiransu ba tare da suna yin bara ba:

 

Aminiya: Mene ne tarihin wannan makaranta ta allo ta Sa’adatul Abadiya da ka bude a nan Jos?

To, wannan makaranta na fara bude ta ce shekara 46 da suka gabata. Kuma na bude makarantar ce a lokacin da na zo wannan gari ina yin almajiranci. Sai na ga tunda na iya Alkur’ani Mai girma, me zai sanya ba zan bude makaranta ba? Shi ne mutumin da nake haya a gidansa ya ba ni daki kyauta na bude makarantar. Na sayo wa yarana guda biyu alluna, muka zauna a kofar gida ina karantar da su. Kafin kwana 10 an kawo mini yara sun kai 20.

Kasancewar na yi yawo a wurare daban-daban na Najeriya duk inda aka san ni sai mutane suka yi ta kawo yaransu, daga wuraren. Wurare kamar Legas da Ibadan da yankin Mambila da kasar Kamaru da sauran wurare duk mutane sun yi ta kawo yaransu wannan makaranta.

A  takaice kafin a yi rikicin Jos, na lokacin tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye, almajiraina sun kai 500. Amma sakamakon wannan rikici, makarantar ta watse. Amma yanzu da zaman lafiya ya dawo, an sake kawo mana al’amajirai daga wurare daban-daban, kamar daga jihohin Nasarawa da Kaduna wadanda sun kai mutum 90, kuma dukkansu Fulanin daji ne zalla. Kuma akwai Hausawa almajirai da aka kawo mini daga Jihar Kaduna. A yanzu dai muna da almajirai, sama da 300 a makarantar.

Yaya za ka kwatanta yanayin yadda kake karantar da almajiranka a da, da kuma yanzu?

Gaskiya yanzu mun canja salon yadda muke karantar da almajiranmu. Domin a da muna karantarwa ne ba tare da hadda ba. Amma yanzu mun surka da Hadisan Manzon Allah da sauran littattafan koyar da addinin Musulunci.Wato bayan yaro ya yi karatun Alkur’ani yakan karanci littattafan addinin Musulunci, domin ya san yadda zai yi ibada. Kuma mun dauko malaman boko, mun sanya su a cikin makarantar. A yanzu mun sayi wani babban gida da za mu mayar da shi makaranta, mu sanya wadannan almajirai da muke karantarwa.

Kuma yanzu mun dauko mahaddata Alkur’ani mutum 12 daga Maiduguri, domin su taimaka mana wajen karantar da almajiran.  Kuma mun dauki masu karantar da ilimin kwanfuta da za su rika karantarwa a makarantar.

Yaya maganar bara ga almajiran makarantar?

Ni tunda na bude wannan makaranta ban taba kasa ciyar da su ba, da zai sanya har su tafi bara a waje. Don haka almajiraina ba su taba yin bara ba, tunda na bude wannan makaranta. Tun a baya, bare yanzu da zamani ya canja. Kuma na sani kowane malami zai iya zama da almajiransa ba tare da sun yi bara ba. Yanzu a ce almajirai suna bara abin kunya ne ga malaminsu da iyayen yaran.

A ka’idar addinin Musulunci barin almajiranmu suna bara kuskure ne. Domin Ubangiji Shi ne Yake ciyarwa. Idan mutum ya tsaya a haka, zai gani. Tunda na bude wannan makaranta ban taba kukan abinci ba.

To wadanne hanyoyi kake bi wajen ciyar da almajiran?

Wadansu iyayen yaran sukan kawo  buhunan masara, amma wadanda suke zo daga nesa ba sa kawo komai, amma haka Allah Yake rufa mana asiri, muna ciyar da su sau uku a kowace rana. Wato muna ba su abinci da safe da rana da daddare. Kuma idan suka yi rashin lafiya mu ne muke daukar nauyin jinyarsu, ba sai an aika wa iyayensu ba. Kuma kowane yaro yana da wajen kwanciya.

Za a iya karantar da almajirai ba tare da sun yi bara ba. Domin kamar ni na yi shekara 46 ina karantar da almajiraina, ba tare da suna yin bara ba. Don haka sauran malamai masu karantar da almajirai a tsagayoyi, za su iya karantar da almajiransu, ba tare da sun yi bara ba. Barin almajirai suna bara karayar zuciya ce kawai. Domin kowane malami zai iya tsayawa ya jajirce ya sanya amajiransa a gaba, kuma Allah zai taimake shi. Amma bai kamata  a ce karatun Alkur’ani sai an yi bara ba.

Mene ne ra’ayinka game da matakin da wasu jihohin kasar nan suka dauka, na hana bara?

A ra’ayina gwamnatocin jihohin da suka dauki matakin hana bara, sun yi daidai. Kowane malami ya dauki iyakar almajiran da zai iya ciyarwa, ba tare da barin almajiransa suna zuwa bara ba. Idan malami ba zai iya ciyar da almajiransa ba, ya bar malaman da za su iya  su yi.

Kuma kai uba da ka haifi yara ka dibi kamar guda 10 ka ba malami ya tafi wani gari da su. Kuma malami kai da matarka da yaran sai sun je sun yiwo bara, abin da suka ci suka rage maka ka ci da matarka. wannan akwai wulakanta kai a ciki. Manzon Allah (SAW) ya ce bai kamata mutum ya wulakanta kansa ba.

Don haka idan aka hana barar nan, za a tafi daidai kowane malami idan bai zai iya ba, ya bari. Yanzu ni da na ajiye almajiran nan da ba sa yin bara, ba ni nake ciyar da su ba, Allah ne Yake ciyar da su.

Wane kira ne kake da shi ga gwamnati dangane da almajiranci da hana bara?

Kira na ga gwamnatocin jihohin da suka hana bara,  shi ne su taimaki almajiran. Kuma ina kira ga gwamnatoci su kafa doka kan dole ne yara su yi karatu. A hukunta duk uban da ya haifi yara, ya ki ya kai su makaranta.