Da Dumi Dumi

Shekara 59 Na Najeriya: Me ake ciki (3)

Illustration of a map with a flag of Nigeria

Bari mu bi abin daki-daki. Na farko me ya sa ko lokacin da Najeriya take cikin kangin bauta a zamanin mulkin mallaka, kuka da damuwar ’yan Najeriya ba wai na rashin kulawa ba ne, sai dai na rashin ’yanci? A wancan zamani ne aka adanta Najeriya da noman zamani da shigo da kayayyakin alatu da jin dadin rayuwa daga kasashen da suke mulkar Najeriyar, ta yadda mota da basukur da babur da gine-ginen zamani da tsabta da kiwon lafiya da tsarin siyasa da mulki suka kasance abin kwaliyance Najeriya. Eh, wani zai ce ai wadannan abubuwa Turawa sun kawo su ne domin son kansu da taimakon kansu kawai. Haka ne, amma abin tuni a nan shi ne Najeriya ba ta shiga tasku da wahalhalu irin yadda take ciki a halin yanzu ba. Idan muka ce wannan shi ne ya hana Najeriyar ta tsine wa Turawa da ’ya’yanta har Turawan suka ba ta ’yanci, ba abin mamaki ba ne. Rayuwa a daidai wancan lokaci ta kasance cikin bauta ga Najeriya da ’ya’yanta, amma bakin kasar alaikum, domin ba ta tsine wa kowa ba.

Haka kuma ko da Turawa suka mika mana ’yanci cikin ruwan sanyi daga 1960, al’amurra ba su canja sosai ba, ’ya’yan da suka gaji Turawa, wato ’yan kasa, sun bauta wa Najeriya da gumi da jininsu, shi ya sa har yau ’ya’yan yanzu ke tunawa da su. Duk wani ci gaba da Najeriya ta samu daga 1960 zuwa 1966 ya kasance ci gaba ne da ’ya’yanta suka assasa ba tare da son rai ko bambancin addini ko kabilanci ba. Aiki tukuru kurum ’ya’yan suka sa gaba. Don arzikin da kasar ta fara samu an ririta shi, an kuma tabbata ya zagaye tsakanin sauran ’ya’yan kasa. Shi ya sa har kasa ta nade ’ya’yan Najeriya irin su Tafawa Balewa da Azikiwe da Awolowo da Sardauna Ahmadu Bello da wadansu irinsu, ba za a taba mantawa da su a cikin tarihin ginuwar kasar nan ba. A dinke Najeriya ta kasance, ba a farke ba. Shi ya sa ma ake jin cewa barakar da ta jawo Yakin Basasa tsakanin ’ya’yan Najeriya daga 1966, ba daga cikin gidan ta fito ba, daga makwabta na kusa ne da kuma na nesa. Idan da ba a sa baki daga waje ba, idan da gulma ba ta shigo cikin rayuwar ba, an tabbata da ’ya’yan Najeriya ba su nemi su wargaza kasar ba.

Saboda haka muna iya cewa munafuncin mutanen waje shi ya kawo barakar da ta kunno kai daga 1966, wadda ita ta kara wagewa har zuwa 1967 da kuma tashin-tashinar tsakanin 1968 zuwa 1970, wanda kuma tabon wannan tashin-rashina shi ya haifar da lalacewar da Najeriya ta samu kanta a ciki. Idan muka ce kila tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970 ne Najeriya ta fara Allah-wadai da ’ya’yanta da suka fandare, suka yaki juna, suka tarwatsa zumunci da son juna tsakanin ’ya’ya da jikoki ba za mu yi kuskure ba. Domin kuwa a daidai wancan lokaci ne aka gane cewa ashe Najeriyar daya ce, amma wai kowa ya san gidan ubansa. Daga wancan lokaci kuwa bakin Najeriya ya hau kan ’ya’yanta, da alama kuma daga wancan lokaci ne ’ya’yan suka fara lalacewa da balbalcewa.

Mu dubi abin da ya faru daga shekarun 1970 zuwa 1983, a daidai wancan lokaci ne za a ce Najeriya ta samu dukkan arzikin da take tinkaho da shi, shi ya sa wadansu daga cikin ’ya’yan nata suke fadar matsalar Najeriya a lokacin ba ta rashin tarin dukiya ko arziki ba ce, abin da za a yi da tarin dukiyar ko arzikin shi ne matsala. Daga jin irin wadannan kalamai daga bakunan wadansu daga ciki ’ya’yan nata, za mu fahimci cewa ko dai ’ya’yan sun fara sonsomin hauka ko kuma dadin arzikin Najeriya ya bibiye musu kai, ba su gane gabas, bare yamma. Wannan wuji-wuji ina gabas da aka yi wa wadansu daga cikin ’ya’yan Najeriya ya sa suka yi watsi da uwar tasu Najeriya.

A maimakon ’ya’yan su samar da abubuwan da za su faranta wa uwar tasu rai, sai suka shiga facaka da dukiyarta. Su ne shirya bukukuwan al’adu na ba gaira ba dalili, giggina otel-otel na alfarmar da bai agaza wa Najeriya, sa’annan ga bayar da kwangilar ayyuka da ba su da wani tasiri ga ci gaban kasar. Ina kuma jin ganin irin yadda ’ya’yan nata suka kasance a lokacin ya sa Najeriya ta fara kuka da shessheka, ga tsufa ya kamata, amma ’ya’yan nata suka kasance tamkar Wowo dan Malam, ka ki halin Malam, rago da wutsiyar kare! Ina kuma jin daga lokacin ta shiga fitowa fili ta fara tsine wa ’ya’yan nata, kuma daga lokacin ne al’amurra suka fara dagulewa.

ADVERTISEMENT

Shi ya sa daga 1983 aka fara ganin alamun ’yan Najeriya na cikin tsaka-mai- wuya. Ba kuma wani abu ya jawo haka ba sai ganin Najeriya ta dai tsine wa wadansu daga cikin ’ya’yan nata, saboda haka wahala da damuwa da kunci sun fara zama ruwan dare, duk da cewa an samu wadansu da suka nemi su dinka wa Najeriya sabuwar riga ko zane, amma ba a bar su suka kai labari ba, haka al’amurra suka ci gaba da gudana har zuwa 1985. Shi ya sa aka shiga watangaririya da Najeriya, wannan mai karfin hali ya kashe wancan da ya ki goya masa baya.

 

Za mu ci gaba