✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 6 da kashe Albani: Har yau  babu wanda ya tuntube mu kan makasansa – Iyalansa

A ranar 2 ga Fabrairun nan ne aka cika shekara shida da kashe Sheikh Muhammad Awwal Albani wanda wadansu ’yan bindiga suka kashe a hanyarsa…

A ranar 2 ga Fabrairun nan ne aka cika shekara shida da kashe Sheikh Muhammad Awwal Albani wanda wadansu ’yan bindiga suka kashe a hanyarsa ta zuwa gida daga makarantarsa a Zariya. Yaya iyalansa suke ciki a yanzu? Aminiya ta ziyarci gidan marigayin, inda ta tattauna da wadansu daga cikin iyalansa kamar haka:

 

Ko za ka fada mana sunanka da dangantakarka da marigayi Sheikh Albani?

Assalamu alaikum. Sunana Abdurrahman Auwal Adam Albani kuma ni ne dansa na farri, shekarata 27 a bana. Kafin rasuwarsa yana da mata 4 da ’ya’ya 23, sai dai a lokacin da aka kai masa harin da ya yi sanadiyar rasa ransa; an kashe matarsa daya da kanena wanda ke bi na mai suna Abdullahi Auwal. Don haka ya rasu ya bar mata 3 da ’ya’ya 22 da muke raye.

Ko za ka bayyana halin da kuka samu kanku a ciki bayan rasa mahaifinku?

To, kamar yadda ka sani ne cewa a daren Juma’a  Malam yana kan hanyar dawowa gida, bayan kammala karatu tare da dalibansa a daya daga cikin makarantun da yake karantarwa a Tudun Wada a cikin mota shi da matarsa mai suna Umma Abdulbari da kuma wadansu daga cikin ’ya’yansa, masu suna Abdullahi da Abdulbari da Abdulhalim da Faruk da Abdulhakam da dalibinsa mai suna Bello, sai wadansu ’yan ta’adda suka bude musu wata da bindigogi; inda suka kashe shi tare da matarsa da dansa. Kuma suka samu wadansu daga cikin dalibansa da suke tare a motar. Sai dai wadansu daga cikinsu sun rayu.

To, daga nan bayan rasuwar Malam, kusan duk rayuwarmu ta ta’allaka ce a makarantar da ya kafa, domin makarantar ita ce take daukar duk wata hidima ta yau da kullum na kannena da iyayena. Don haka alhamdu lillahi, abubuwa suna tafiya ba wata matsala ko damuwa. Kamar yadda ka sani, cewa Malam ya yi niyyar bunkasa wasu cibiyoyin ilimi kamar yadda ya fara, to sai kuma Allah Ya karbi rayuwarsa. Ka yi tambayar cewa ko akwai wata matsala, to matsalar ba wata wadda ba za ta iya gyaruwa ba ce, domin matsala ce ta cikin almajiran Malam, ta wane ne zai gaje shi? Wannan ita ce kawai matsalar da take dan kawo tarnaki a cikin tafiyar da ake ciki zuwa yanzu amma in ban da wannan babu wata matsala, domin dukkan kannena suna samun kulawa dangane da karatu.

Jami’an tsaro sun ce sun kama wadansu mutum biyar da suke zargin su ne suka kashe Malam. Shin ko jami’an tsaron sun neme ku domin wani bayani?

To, kamar yadda kowa ya ji a kafafen watsa labarai, mu ma haka muka ji rade-radin cewa wai an kama wadansu da ake zargin sun kashe Malam. To, kuma kamar yadda ka sake tambayar cewa ko su jami’an tsaro sun neme mu a kan maganar, ina iya cewa a’a. Ni dai a sanina har zuwa yau babu wani wanda ya neme mu a kan cewa mu zo an kama wadanda ake zargin cewa su ne suka kashe Malam. To, kuma tun daga lokacin muka sa ido domin mu ji cewa ga shi za a kai su kotu amma har zuwa yanzu ba mu ji komai ba. Don haka mu daga bangaren hukuma babu wani wanda ya neme mu.

Wadannan cibiyoyin ilimi da Malam ya bari, ko yaya kake ganin ci gabansu?

To, ana samun ci gaba sai dai matsalar da ake samu ita ce wajen yadda su daliban Malam da suke kula da duk wasu harkoki da marigayin ya kafa ko ya yi niyyar kafawa Allah bai nufa ba, suka bari. Yanzu ka ga kamar ginin masallaci, kusan shekara daya ke nan yana tsaye ba wani ci gaba da aka yi a kai. Saboda almajiran Malam sun bari Shaidan na neman ya yi wasa da hankalinsu wajen jefa musu sabani a kan neman mulki ko dukiya; domin mu yadda muke hangen abu, su kamar ya sha bamban. Mu ba wai kudi muke hange ba, a’a alheran da cibiyar za ta samar ne. Don haka muke sa baki ba tare da wani abu ba. Koda suke ganin kamar mu yara ne, ai ba haka ba ne. Gani muka yi bai dace a ce ana fada a kan mulki ko kudi ba. Don haka mu fatarmu ita ce, duk wani aikin alheri da Malam ya assasa ya dore cikin taimakon Allah, fatarmu ke nan.

‘An yi kokarin magana da makaranta’

Daya daga cikin yaran da Malam ya rike a lokacin da yake raye mai sana Mahmoud Shu’aib Auwal ya yi karin bayani kan yadda rade-radin cewa an kama wadanda ake zargin su ne suka kashe Malama a tattauawarsa da wakilinmu kamar haka:

Ko akwai bayanin da za ka yi kan kame makasan Malam?

To ni dai kanwar marigayi Malam ce ta haife ni amma na taso ne a gidansa. Don haka karin bayanin da zan yi shi ne, a daidai lokacin da gwamnati ta ce ta kama mutane shida ko biyar wadanda ake zargin su suka kashe Malam, kamar yadda Daraktan Makarantar ya ce sun yi kokarin magana da makaranta amma tun daga wancan lokacin babu wata magana kwaya daya, ko wani abu da ya kara bayyana daga gwamnati. Ba mu sani ba shin wadannan mutanen su ne suka kashe Malam ko a’a.

Abu na biyu, ai ya kamata zuwa yanzu mu iyalan Malam mu san shin su din ne suka aikata hakan kuma su wane ne suka sa su, sannan wace kotu aka kai su, kuma wane hukunci aka yanke musu? To, duk wadannan suna daga cikin abubuwan da mu iyalan Malam ya kamata mu sani.

Kasancewa kuna da hakki a kai kuma an ce an kama wadanda ake zargi, ko akwai wani mataki da za ku dauka ganin cewa an yi wa wadanda aka kama hukunci, ko kuwa kamar yadda dan uwaka ya ce, ku kun bar wa Allah?

Ai kamar yadda Malam yake fadi ne a kullum, lokacin yana raye cewa mu dama ba masu son tashin hakali ba ne. Mu mutane ne musu son zama lafiya. Shi dai Malam muna masa fatar alheri, ita kuma gwamnati yanzu ya rage nata, duk irin yadda ta yi, mu ba mu da ja.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige kan halin da ake ciki game da batun wadanda aka kama bisa zargin hannunsu a kashe Sheikh Muhammad Albani  ya ce, zai bincika ya ji domin shi bai dade da karbar aiki a jihar ba.