Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Shekara 8 ba a tura masu horar da ’yan wasa kwas a Gombe ba – Adamu Soye

Malam Hamza Adamu Soye

Shekara 8 ba a tura masu horar da ’yan wasa kwas a Gombe ba – Adamu Soye

Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Gombe, Malam Hamza Adamu Soye, ya  ce shekara takwas rabon a tura masu horar da ’yan wasa kwas a Jihar Gombe, sai yanzu da suka zo suka fara.

Malam Hamza Adamu Soye, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa, inda ya ce karfin gwiwar da suka samu daga Gwamna Inuwa Yahaya, ya sa yanzu suke ganin za su iya tunkarar kowane kulob a babbar gasar wasanni da za a gudanar a Jihar Borno daga ranar 21 ga watan Janairun nan.

Ya ce akwai ’yan kwallon kafa da kwallon raga da kwallon kwando da kwallon gora da tsalle-tsalle da tsere da kwallon mata da  sauran bangarorin wasannin 18 da za a fafata da suke ganin samun nasara.

Ya ce yanzu sun yi zama da masu horar da ’yan wasan da shugabaninnsu don ba su kwarin gwiwa kan yadda za su rika horar da ’yan wasan.

Adamu Soye, ya ce za su ga Gwamna kan wasu kudi da suke sa ran a ba su don gudanar da wasu aikace-aikace kafin su tafi. Don yin hakan zai sa ’yan wasa su tafi cikin walwala su saki jiki don yin wasan da zai kai su ga samun nasara.

Ya ce dukkan daraktocin hukumar tsofaffin ’yan wasa ne da suke ba shi hadin kai don ganin wannan wasa na Shiyyar Arewa maso Gabas da za a yi a Maiduguri sun ciwo wa jihar kyaututtuka.

Ya ce da izinin Allah bi sa hadin kan da Gwamna ke ba su za su ciro wa Jihar Gombe kitse a wuta.

Sai ya yi kira ga magoya baya da ’yan wasa su zama masu biyayya kamar yadda aka san mutanen Gombe da bin doka da oda a lokacin gudanar da wasannin don wadansu su yi koyi da su ba tare da sun zubar wa Gombe mutunci a idon duniya ba.