Search
Subscribe
Shekara biyu rabonmu da Ahmadu Chanchangi

Shekara biyu rabonmu da Ahmadu Chanchangi

Yau juma’a 19 ga watan Afrilu shekara biyu ke nan cur rabonmu da Alhaji Ahmadu Chanchangi fitaccen attajirin nan da ke garin Kaduna wanda Allah Ya yi wa rasuwa ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2017.

Marigayi Alhaji Ahmadu Chanchangi ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya, hasali ma dai ana kan hanyar zuwa da shi asibiti a Abuja ne Allah Ya yi masa cikawa aka juyo aka dawo da shi gida Kaduna.

A lokacin da marigayi Chanchangi yake raye ya taimaka wa al’umma a fannoni da dama na rayuwa, musamman a fagen samar wa jama’a da ilimin addini da na zamani.

Saboda haka ne ma ya bude shahararriyar kwalejin nan ta Sheikh Abubukar Gumi da ke Tudun Wadan Kaduna inda ake koyar da ilimin zamani da na addinin Musulunci.

Kodayake makarantar ta kudi ce amma bambancinta da ta gwamnati kadan ne, domin marigayi Chanchangi ya dauke wa mafi yawan iyayen da ke da ’ya’ya a makarantar kudin makaranta, inda ’ya’yansu ke karkashin wani fayil mai suna Alhaji Ahmadu Chanchangi (AAC).

Bayanin da na samu ya nuna cewa, wannan fayil na AAC iri biyu ne, akwai AAC cikakke da AAC rabi. AAC cikakke shi ne wanda yake dauke da sunayen daliban da aka dauke musu komai, wato wadanda aka dauke musu kudin makaranta kuma ake ba su littattafan karatu da sauran abubuwa, shi kuma AAC rabi shi ne wanda aka dauke musu kudin makaranta kawai.

Duk wani na kusa da marigayi Chanchangi idan ’ya’yansa suna karatu a makarantar nan to yana karkashin AAC ne, walau ’yan uwan Chachangi ne ko makwabta ne ko ma’aikatan kamfaninsa ne ko malaman makarantar tasa ce ko direbobin motocinsa ne ko kanikawan da ke gyaran motocinsa ne, duk wani aiki kowane iri ne mutum yake yi wa Chanchangi idan ya kai dansa wannan makaranta zai yi karatu kyauta ne. Shi ya sanya mutanen Tudun Wada da kewaye da dama suka ci moriyar wannan makaranta da Ahmadu Chanchangi ya bude. Wannan makaranta ta samar da kwararru da dama a fannoni daban-daban na ilimi da yanzu suke aiki a wurare daban-daban na kasar nan.

Na taba tambayarsa game da wata jita-jita da ake bazawa cewa wai an hana gina masallaci a kwalejin da ya gina, da na nemi sanin dalili sai ya dauke mu ya kai mu wurin da aka fara ginin masallacin ya nuna mana, na ce masa ‘me ya sa aka daina aikin?’ Sai ya ce ‘muna son mu fara gina masu Sallah ne tukun.’

Sannan ta fuskar ilimin addini wannan makaranta tana koyar da ilimin addinin Musulunci, wanda ya sanya da yamma idan mata suka taso daga makarantar wanda bai sani ba saboda yawansu sai ya dauka duk matan da ke garin Kaduna a nan suke karatu.

Marigayi Chanchangi ya yi kokari sosai wajen ganin al’ummomin da ke kusa da shi sun samu nagartaccen ilimi, shi ya sanya baya ga wannan kwalejin na Abubukar Gumi da ya bude, ya kuma bude wata makarantar a kofar gidansa inda ake koyar da matan aure da sauran wadanda suka manyanta karatun addini da na zamani.

Sannan kuma shi ne na farko da ya rika daukar nauyin sanya karatun tafsirin marigayi Sheikh Abubukar Mahmud Gumi a gidajen rediyo, wanda aka dauki tsawon shekaru ana yi.

Marigayi Chanchangi ya taimaka wa jama’a a fannonin rayuwa da dama domin inganta rayuwarsu, domin bayan taimakawa wajen samar da ilimi ya kuma himmatu wajen ganin mutane sun mallaki muhalli na kashin kansu, inda ya raba filaye ga dimbin mutane. Hasali ma dai albarkacin marigayi Chanchangi ne garin Rigasa ya bunkasa, domin shi ne ya rika raba wa mutane filaye kyauta domin su gina gidajensu, kuma shi ne ya fara samar da gadar shiga garin Rigasa daga Bakin Ruwa, kafin wannan lokacin gadar katako ce  a wurin wanda ke yawan samun matsala, daga baya ne Kantoman Mulkin Soja na Jihar Kaduna, Birgediya Janar Lawal Ja’afaru Isa ya ga cewa bai dace garin mai dimbin jama’a irin Rigasa ba a bar shi babu gada kwakkwara, sai mutum daya ne yake taimakawa, domin haka gwamnatin Jihar Kaduna ta gina gada ingantacciyya a Rigasa, hakan ya kara bunkasa garin.

Baya ga ilimi da muhalli da Chanchangi ya taimaka wajen samarwa, ya kuma kasance mutum ne mai kyauta kamar ruwan sama, domin duk inda ya je sai ya raba wa mutane kudi, haka kuma yana rabon sutura da abinci, musamman a lokacin azumi da lokacin bikin Sallah.

Haka kuma Chanchangi ya taimaka wajen samar wa mutane da dama aikin yi ta hanyar kamfaninsa na jirgin sama na Chanchangi da kuma makarantun da ya bude.

Saboda dimbin taimakon da marigayi Chanchangi ya yi wa al’umma ne ya sanya da ya rasu dimbin mutane suka taru domin yin Sallar Jana’izarsa, kuma da za a kai shi makabarta dubban mutane suka yi masa rakiya, hatta matan aure da ke cikin gidaje sun rika fitowa domin ban-kwana da Chanchangi, inda suka rika yi masa addu’ar samun rahama. Wani limamin masallacin Jumu’a a Tudun Wadan Kaduna ya bayyana cewa a lokacin da aka dauki gawar Chanchangi zuwa makabarta ya ji wata mata da ke kusa tana cewa, ‘Alhaji sai Aljanna,’ saboda sanin abubuwan alherin da ta san ya shuka a lokacin rayuwarsa.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin