✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara ta arce

Masu fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada, watanni karamin lauje da suka zurare kuka shiga Hijiriyya. To muna fatan kun yi kaura daga tafka…

Shugaba Jatau na duba watsattsaken Baba-Ojo da ya aiko masaMasu fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada, watanni karamin lauje da suka zurare kuka shiga Hijiriyya. To muna fatan kun yi kaura daga tafka ta’asa a kwnaon tasa. Ku kuwa masu addu’a da gicciye, kwananan za ku shiga cikin miladiyya; fatanmu dai ku gicciye mugun aikin shagabannin Haurobiya.
Da fatan Mai-duka zai sanya mu dace. A matsayina na direbann alli wannan farfajiya, ina fatan darasussanmu za su amfani al’umma. Gaisuwar Hijiriyya da Midiladiyya ga Shagaba Jatau Mai sa-in-sa da Dauda Mai maki da Tumbin-wulli da Akuyar-maman-daudu da sauran manyan Haurobiya. Muna fatan a shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya za ku daina tafka ta’asa, kuma ku himmatu wajen tabbatar da adala a kan kasa.
Ku kuwa talakawan Haurobiya, ku himmatu wajen bin doka da oda, har Mai-duka ya kawo agaji, ya akwar muku da mugun aiki irin na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Kowa ya gaji da sakaci da sakarci Baba-Ojo mai gonakin Ottawa da tabargazar yaran Gudun-loko, wadanda suka hada da Rubabben Abban titi da mai karanta Labaran mako a fadar Asosa da ke tsaunin Bila.

Sakonnin
makaranta

Ga Ja-gaban  zabin sonka na kasar Haurobiya
Assalam, da fatan direban alli, kuma mai jan ragamar makaranta da masu karatu ya shigo haurobiya lami lafiya bayan kallon buga gangar Abzinawa da ya je can Agadez.
 A zahiri, mutan Hauurobiya ba su ji dadin kalaman da malamin zabe ya yi baje kolinsu ba, dangane da rashin yin zabe a jihohin da suke karkashin dokar ta baci, don haka nake shawartarsa tun da lullumi, gwanda ya sha gwanda, watakan ya lallaba wajen masu hayagagar labarai ya janye wanga batu, ta yadda al’umma za su yi masa kyakkyawan zato, zai kuma fita daga azargagiyar zargi!
Daga Saddik Tukur Gwarzo 08060869978.

Ka cika alkawari Gogel
Direban alli ka tuna wa Gogel alkawarin da ya yi cewa lallai ya cika shi, a mako mai karotowa. Sannan na ga mutanen Arlit a cikin shafin baje na-mujiya a Amintattar Jaridar kasar Haurobiya. Daga Bokan-Turai na Tagadas, Dokta Murtala. Zagaye da madambaci da kofar hanci da kwanciyar magirbi da kwanciyar magirbi da zagaye da da kwanciyar magirbi da babban lauje da karamin lauje.

Alkawarin Gogel
Assalamu alaikum, warahamatullahi. Bayan gaisuwa irin ta masu fuskantar alkibla don kadaita Mahalicci da ibada, ina yi wa ’yan uwana dalibai barka da sake saduwa a karshen darasinmu, wadand na dauki alkawari a makon da ya arce. Na samu sakonni a makon da ya arce a kalla karamin lauje da kofar hanci ta cikin kurtun magana. Wanda ya fara turowa, shi ne Bokan Turanmu, wanda muka yi balaguro da shi zuwa Tagadas, haka zakalika Indoriya daga Jihar yawon-Bebe, ta kira ta ce a nusar da ita yadda za ta rika murguda baki, in za ta yi batu a cikin yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa. Idan kun ari takalmin Malam Tunau, mun tsaya ne a darasinmu na tafiya Tagadas, kamar yadda na tsegunta muku, mun tafi da direban alli, ni ne lamba manuniyar kasansa duk da cewa suna shorido guda da Koguna, ba su samu matsala. Mu kuwa tun ba yi tattakin tazarar kofar hanci da zagaye shoridonmu ta turje; muna wuce garin da za ka iya zaurewa sai kafar shorido ta kara tumbudi irin na ’yan dugwi-dugwi. Kai a garin Daurama sai dda kanikawa suka kanannadeta, sai muka yi gaba
Wasu kuwa batu suke nema a kan Jam’iyya Mai dan boto da sanda jirge. To mu hadu a gaba. Daga Gogel.

Arewatawa mu fadaka
Mu kara azama wurin rokon Mai duka, Assalamu alaikum ya ku daliban wannan makaranta mai albarka ta Dodorido, da fatan  uban gayya uban tafiya abin koyi,Ferfesa malam DODO uban dodanni yana  sumul. ‘yar dugwin Dodanniya Nana Asma’u dama sauran dukkan shagabannin suna garau, musamman P.R.O na kasa Aliyu Mukhtar Sa’idu. Ina bada uziri kusan watanni kofar hanci da suka arce ban ce ufan ba,  saboda haka nake bada na damo.
Daga karshe ina kara jan hankalin dukkan al’umma, musamman masu kallon alkibla  sau babban lauje a rana su dage da rokon mai duka, musamman haliin da Arewatawa suka samu kawun su a ciki dare da rana. Da fatan mai duka ya ye mana.  dalibi mai biyayya, Abu Ja’afar Usman Ibrahim Nadabo, Babban lauje da manuniyar kasa. 07068353836.