✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekarar 2019: Abubuwa 6 da suka jawo cece-kuce a Kannywood

Masana’antar Kannywood na cikin manyan bangarori da ke samar da ayyuka ga dimbin matasan Najeriya, musamman mazauna Arewa. Sannan kamar sauran masa’antun fina-finai a duniya,…

Masana’antar Kannywood na cikin manyan bangarori da ke samar da ayyuka ga dimbin matasan Najeriya, musamman mazauna Arewa.

Sannan kamar sauran masa’antun fina-finai a duniya, ita ma ta Kannywood takan tsinci kanta cikin rudani da fadace-fadace, baya ga kuma nishadantarwa da suke yi.

A lokaci da dama, sukan yi kokari wajen danne rikicin, ta yadda duniya ba za ta san abin da suke ciki ba, amma kasancewar jaruman masu masoya da yawa, wani lokacin abu kadan, sai duniya ta dauka.

Wannan ne ya sa muka rairayo muku manyan abubuwa 6 da suka faru a shekarar 2019 a Masana’antar Kannywood da suka fi jawo wa masana’antar cece-kuce.

Ali Nuhu ya maka Adam Zango kotu

A watan Afrilu na shekarar 2019 ne jarumi Ali Nuhu ya maka jarumi Adam Zango a kotu saboda zagin mahaifiyarsa.

An dade ana sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango saboda yawan rikici da suke yi, wanda ake zargin magoya bayansu da hadawa, amma wanda suka na watan Afrilun wannan shekarar ya dauki sabon salo, inda karon farko ya kai ga kai kara kotu.

An ta kai-komo a kan rikicin, amma daga bisani aka samu nasarar sake yi musu sulhu, inda daga baya Adam A. Zango ya bayyana cewa ya ji kunya lokacin da ya ji Ali Nuhu ya kai shi kara.

Takardar sammacin da kotu ta aiko wa Adam A. Zango

Amina Amal ta maka Hadiza Gabon a kotu zan zargin madigo

A watan nan dai na Afrilu, jim kadan bayan an gama hatsaniyar sulhunta Ali Nuhu da Adam A. Zango, kwatsam sai wani rikicin ya sake barkewa, inda jaruma Amina da Hadiza Gabon suka yi kaca-kaca.

Rikicin ya fara ne bayan Amina Amal ta sanya wasu hutuna a shafinta na Instagram da ke nuna wani sashen jikinta, wanda ya jawo cece-kuce daga mutane da dama ciki har da Hadiza Gabon da wasu jaruman kannywood.

Sai Amina Amal ta mayar da martani, inda ta ce ita hutuna kawai take sakawa, amma ita ba ta madigo. Bayan nan ita kuma Hadiza Gabon ta saki wasu bayanai da suka wakana tsakaninsu na sirri, sannan kuma daga baya aka ga wani faifan bidiyo inda Hadiza Gabon ke dokan Amina Amal.

Saboda wannan ne Amina Amal ta maka Hadiza Gabon a kotu bisa zargin cin zarafi da wulakanta ta, inda ta bukaci a biya ta Naira miliyan 50.

Shi ma wannan daga baya aka yi sulhu magana ta wuce.

Takardar sammacin da kotu ta aika wa Hadiza Gabon

Adam A. Zango ya bar Kannywood

A watan Agusta ne jarumi Adam A. Zango ya sanar da ficewarsa daga Masana’antar Kannywood.

Zango ya bayyana rashin adalci da ya ce ana masa a matsayin daya daga cikin dalilansa na ficewa daga masana’antar.

Sannan ya bayyana cewa ya zama mashiryin fim mai zaman kansa, inda daga baya ya sanar da cewa zai dauki wani sabon fim yana bukatar jarumai. Hakan ya jawo cece-kuce, inda wasu suke cewa Adam Zango zai dauki ’yan mata kanana fim domin a bata su, ciki har da wani malami. Wanda shi kuma Adam A. Zango ya fito ya yi bayani a kai, inda ya ce ba haka yake nufi ba.

Adam A. Zango                                       Hoto: BBC

Adam Zango ya kashe miliyan 46 don daukar nauyin karatun dalibai 101

A watan Oktoba ne kuma aka samu labarin jarumi Adam A. Zango ya kashe Naira miliyan 46 domin daukar nauyin karatun dalibai 101 a Makarantar Farfesa Ango Abdullahi International da ke Zariya.

Zango ne ya wallafa a shafinsa na Instagram, sannan daga bisani Jaridar Aminiya ta bibbiya makarantar, inda ta tabbatar mata cewa Zango ya biya kudin.

Labarin ya haifar da cece-kuce da dama a ciki da wajen Najeriya, inda wasu suke cewa Adam Zango bai da kudi, duk da cewa ya bayyana cewa da gidauniya ya yi amfani. Sannan kuma wasu suka rika yabanshi suna sanya masa albarka.

Rasit na biyan kudin dalibai da Zango ya biya Hoto: Instagram na Zango

Sheikh Fantami ya yaba wa Hadiza Gabon

A watan Nuwamba, an karrama jaruma Fati Washa da Ali Nuhu a Landan, inda aka sanar da Fati Washe a matsayin Gwarzuwar Jaruma, inda ta samu rakiyar Hadiza Gabon da Rahama Sadau.

Bayan ta karbi kyautar, sai suka saki wasu hutuna su uku a tare da suka jawo cece-kuce.

Wasu masu martani a kan hutanan sun musu zargin zina da madigo, wanda hakan bai musu dadi ba wanda hakan ya sa Hadiza Gabon ta mayar da martani da kakkausar magana.

Jim kadan kuma sai ta share martanin, sannan ta roki gafarar Allah. Wannan abin da ta yi ne ya jawo mata yabo daga wajen Minista, Sheikh Isa Ali Fantami.

Daga hagu: Fati Washa, Rahama Sadau sai Hadiza Gabon    Hoto: Instagram na Rahama Sadau

Bude katafaren wajen shakata na Rahama Sadau ya jawo cece-ku-ce

A watan Disamba ce kuma jaruma Rahama Sadau ta bude katafaren wajen hutu mai suna Sadau Home a Kaduna.

Wannan wajen hutu, wanda ke kan Titin Rabah a Unguwar Sarki a Kaduna ya kunshi wajen cin abinci da na wanke kai na mata da wajen aski da wajen shan shisha da sauransu.

Bikin bude wajen shakawatawan ya zo ne kwanaki kadan bayan bikin cikarta shekara 26 da haihuwa.

Tun bikin ranar haihuwar ne ya fara jawo cece-kuce, inda aka rika martani a kan yanayin shigar da ta yi. Sannan kuma wasu suke ganin bai kamata ba bude wajen shan shisha ba.

Wannan lamarin ya jawo cece-kuce da dama, inda har ita kanta Rahama Sadau din ta rika mayar da martani ga duk wanda ya zage ta.

Shigar Rahama Sadau da ta jawo cece-kuce Hoto: Instagram na Rahama Sadau