✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekarau ba zai iya kawo wa Jonathan Kano ba –Tsohon Kwamishina

Tsohon Kwamishina a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau Alhaji Ibrahim Garba ya ce komawar tsohon ubangidan nasa zuwa Jam’iyyar PDP ba zai sa Shugaba Goodluck…

Tsohon Kwamishina a zamanin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau Alhaji Ibrahim Garba ya ce komawar tsohon ubangidan nasa zuwa Jam’iyyar PDP ba zai sa Shugaba Goodluck Jonathan ya ci zabe a Jihar Kano ba.
Alhaji Ibrahim Garba ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano inda ya ce shi da sauran magoya bayan tsohon Gwamnan sun yanke shawarar ci gaba da zama a Jam’iyyar APC saboda su kwato mulki daga hannun PDP a shekarar 2015.
“Lokacin da muke a gwamnati a shekarar 2003 zuwa 20011 Shekarau ya gargade mu kan mu guji Jam’kiyyar PDP, domin jami’iyyar shaidanu ce, don haka muka ki komawa PDP, domin har yanzu ban ga abin da ya canja a cikin PDP ba. Mu da muka fito daga tsohuwar Jam’iyyar ANPP mun san hanyoyin da muka bi muka kafa gwamnati, don haka a yanzu ma za mu bi wannan hanyar mu sake cinye Kano a zaben shekarar 2015,” inji shi.
A martanin kakakin tsohon Gwamna Shekarau Malam Sule Ya’u Sule ya ce bai yi mamakin jin wadannan kalamai daga bakin tsohon kwamishinan nasu ba, idan aka yi la’akari da cewa mutumin ba cikakken dan siyasa ba ne. “Ibrahim Garba ba cikakken dan siyasar Jihar Kano ba ne, saboda ba dan asalin Jihar Kano ba ne, haka kuma bai san komai game da siyasar jihar ba. Saboda ba ya iya yawo a Kano ballantana ya kafa wata siyasa shi ya sa ma ya yi kaura zuwa Jihar Kaduna,” inji shi.
Malam Sule Ya’u Sule ya ce kowace jam’iyya akwai mutanen kirki cikinta akwai kuma na  banza, ya danganta da irin mutanen da mutum zai yi mu’amala da su. A cewarsa “Shekarau zai zauna a PDP ne tare da mutanen kirkin da ke cikinta wajen kokarin ciyar da kasa gaba,” inji shi.