✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekarau ya yi mana butulci – Sani Fema

Maganganun da tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi cewa bai dace a gudanar da zaben shekarar 2015 a jihohin Borno da Yobe…

Maganganun da tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya yi cewa bai dace a gudanar da zaben shekarar 2015 a jihohin Borno da Yobe da Adamawa ba in har ba a samu kyautatuwar tsaro ba, tamkar butulci ne da cin zarafin yankinsa na asali.
Wani kusa a Jam’iyyar APC a Jihar Yobe Alhaji Muhammad Sani Fema ne ya bayyana haka a hirarsa da Aminiya, inda ya ce kalaman da Sardaunan Kano ya yi ba su yi wa al’ummar jihohin da abin ya shafa dadi ba.
Alhaji Sani Fema ya ce bai yi mamaki da wannan magana ta Shekarau ba, saboda ya yi haka ne domin ya gyara miyarsa ganin ya yi maganar ce don burge ubangidansa Shugaba Jonathan.
Ya ce irin wadanan maganganu na Shekarau Jam’iyyar PDP ke son ji saboda suna da wasu boyayyun manufofi ga jihohin uku da Jam’iyyar adawa ta APC ke mulki a kokarinsu na kauce wa salwantar madafun ikonsu a zaben badi.
Alhaji Sani ya ce maganganun Shekarau ba ra’ayinsa na shi kadai ba ne a’a ra’ayi ne na iyayen gidansa da suke so ko ta halin kaka su dakile ’yan cin talakawan jihohin Yobe da Borno da Adamawa, “dama su muke zargi da kara ingiza rikita-rikitar da ake yawan samu a jihohin,” inji shi.
Ya ce in za a gudanar da zabe a kasashe irin su Afghanistan da Somaliya da Iraki, babu abin da zai hana a gudanar da zabe a jihohin uku cikin nasara.