✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shigo da masara Najeriya: Cikin manoma ya duri ruwa

A tsakiyar wannan makon ne manoman Najeriya suka nuna damuwarsu game da bai wa wasu kamfanoni izinin shigo da masara zuwa Najeriya daga waje, lamarin…

A tsakiyar wannan makon ne manoman Najeriya suka nuna damuwarsu game da bai wa wasu kamfanoni izinin shigo da masara zuwa Najeriya daga waje, lamarin da manoman ke ganin zai karya farashin hatsin ta yadda za su rasa ribar noman nasu baki daya.

Manoman sun bayyana haka ne sakamakon daga murya da Gwamnan Jihar Katsina da kuma Sanata Adamu Aliero suka yi game da tabbatar da rahotan cewa manyan jiragen ruwa shake da masara kimanin tan dubu 50 sun iso Najeriya.

Manyan kusoshin biyu, sun zargi Ministar Kudi, Kemi Adeosun da kuma Ministan Gona, Cif Audu Ogbeh bisa amincewa tare kuma da bayar da lasisin shigo da masarar ga wasu manyan ‘yan kasuwa zuwa Najeriya daga Kasar Brazil.

Wannan korafi ya fara tasowa ne tun a lokacin ziyarar gwamnonin APC karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha a Jihar Kebbi. Inda Gwamna Masari ya bayyana cewa Audu Ogbeh da Adeosun ne ke da hannu wajen shigo da wannan hatsi daga Brazil.

Haka kuma tsohon gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Adamu Aliero ya ce “Mun samu wannan labari daga ingantacce tushe cewa ma’aikatunku ne suka bayar da lasisi gare su. Kuma wannan yunkuri ba zai taimaki manomanmu ba. Sannan mun riga mun amince cewa babu maganar shiga da hatsi kasar nan daga waje,” a cewarsa. Amma ministocin biyu sun musanta wannan zargi.

Daya daga cikin shugabannin Kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN) reshen Jihar Kaduna, Alhaji Nuhu Aminu ya bayyan awa wakilinmu cewa wannan abin takaici ya faru ne bayan da manoma suka amsa kiran Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari na komawa zuwa noma, sannan kuma suka zuba jarinsu baki daya cikin harkar ba tare da tallafi (subsidy) daga gwamnati ba. Inda ya ce sayar da buhun masara akan farashi kasa da dubu 8 zai iya sanyaya gwiwar manoma game da noman anan gaba.

Haka zalika Shugaban Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Alhaji Kabiru Ibrahim ya yi nuni da cewa wannan mataki zai sanya manoma cikin garari. Ya ce domin manufar wannan gwamnatin shi ne kange shigo da dukkan abinda za a iya samar da shi a cikin kasa. Idan muka bude kofofinmu don shigo da dukkan abinda zamu iya samarwa a kasar nan, to lallai hakan ba zai haifar da da mai ido ba in ji shi.

Tun da farko Gwamnatin Shugaba Buhari ta aza hasashenta bisa samar da kimanin tan miliyan 15 da rabi daga cikin tan miliyan 20 na abinci da kasar nan ke bukata. Haka kuma Ma’aikatar Noma da raya karkara ta kasa ta bayyana cewa asalin abinda kasar nan ke bukata na masara ya kai kimanin tan miliyan 15, sannan a halin yanzu ana noma masarar da yawanta ya kai kimanin tan milyan 10 da rabi a duk shekara.

A wani bincike da Jaridar Daily Trust ta yi, ta gano cewa a yanzu haka ana sayar da buhun masara akan farashin naira dubu 15 zuwa dubu 19 a mafi yawan kasuwannin kasar nan.