✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shigo da shinkafa ya hana ta gida kasuwa – Murmushin Amarya  

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Karamar Hukumar Dutsinma Alhaji Aminu Ibrahim wanda aka fi sani da Murmushin Amarya ya ce suna samun nakasu a wajen sayar…

Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Karamar Hukumar Dutsinma Alhaji Aminu Ibrahim wanda aka fi sani da Murmushin Amarya ya ce suna samun nakasu a wajen sayar da shinkafar gida da manoman Jihar Katsina ke nomawa.

Alhaji Aminu ya ce, “Shigo da shinkafar waje ta iyakarmu da Jamhuriyar Nijar ya sa ba mu samun cinikin shinkafar da muke nomawa a nan jihar. Hakika manoman wannan jiha sun amsa kiran da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi na a koma gona, musamman na shinkafar don hana shigo da ta waje, amma saboda yadda masu fasakwauri ke shigo da ita ya sa mu masu saye daga manoman mu saffara ta a injinan cashewa tare da sanyawa a cikin buhunna domin tafiya da zamani muke fuskantar rashin kasuwa. Hakan na shafar manoman ta yadda dole suke rage nomanta.”

Shugaban ya kara da cewa shi kansa tsarin noman shinkafar an samu wadansu batagari da suka gurbata shirin. “Mafi yawan manoman suna yi mana korafi idan mun je saye cewa irin shinkafar da ake ba su ba irin wadda aka ce ba ce. Wani irin yana iya yin watanni a tsaye ba ’ya’ya, sabanin irin da ake nomawa sau biyu ko sau uku wani lokaci ma har sau hudu a kasashen Indiya da Thailand. Ka ga ke nan ko a nan sai gwamnati ta kara sa ido ga jami’an da take bai wa nauyi. Mu mun yi kishi mun sayo injina mun kafa kamfanoni domin gyara da tsabtacewa amma kuma ba ya ga karanci da rashin samunta a kan lokaci ga halin ko in kula ko rashin kishi ga mutanenmu musamman jihohin da ke iyaka da Nijar suke nunawa saboda shigowa da ta waje da ake yi ba bisa doka ba duk da cewa su jami’an hana fasakaurin suna iyakar kokarinsu na ganin sun hana. Kuma manoman ga irin matsalolin da suke fuskanta na rashin samun iri mai kyau ballantana batun taki da sauransu.”

Daga karshe Alhaji Aminu ya yi kira ga jama’a a kowane lokaci su rika kishin kayan cikin gida wanda hakan a cewarsa zai bayar da damar bunkasa tattalin arzikin jama’a domin za a wayi gari namu ake fitarwa ba shigowa da wani daga waje ba.