✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shigowar bakin manoma ke haddasa rigimar manoma da makiyaya – Miyetti-Allah

Shugaban Kungiyar Miyetti-Allah Cattle Breeders na Jihar Nasarawa, Alhaji Huseini Mohammed ya koka game da yawan shigowar manoma baki jihar, inda ya ce hakan ya…

Shugaban Kungiyar Miyetti-Allah Cattle Breeders na Jihar Nasarawa, Alhaji Huseini Mohammed ya koka game da yawan shigowar manoma baki jihar, inda ya ce hakan ya na gurguntar da kokorin da kungiyar ke yi na magance rigingimu tsakanin al’ummarsa ta Fulani makiyaya da manoma a fadin jihar.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishin kungiyar na jihar dake Lafia. Ya ce akwai manoma baki da dama dake fitowa daga wasu jihohi dake makwabtaka da jihar da suka hada da Filato da Benuwai da Taraba da Kwara da Kogi da sauransu don yin noma, wadanda a cewarsa sau da yawa su suke yawan samun sabani da Fulani makiyaya a jihar.

“Kungiyar Miyetti-Allah tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar suna iya kokarinsu wajen kawo karshen rigingimu tsakanin manoma da fulani makiyaya a jihar, amma sai shigowar wadannan baki manoma a bana ya na kawo mana cikas ga wannan kokori.

“To sau da yawa wadannan manoma baki ne ke jawo mana fitina a jihar nan, don manomanmu da Fulani makiyaya a jihar nan kungiyarmu mun sulhunta kanmu bayan mun gano bakin zaren sabanin dake tsakaninmu, kuma da yardar Allah ana samun zaman lafiya. Saboda haka ina kira ga wadannan manoma baki cewa su rika tsayawa su yi nomansu a jihohinsu, don zuwansu jihar nan ba alheri ba ne ga zaman lafiya da cigaban al’ummarmu ba.

“Kuma ina so in yi amfani da wannan dama in yi kira ta musamman ga gwamnatoti a duka matakai tare da hadin kan hukumomin tsaro da su tashi haikan don hana wadannan mutane shigowa jihar nan da sunan yin noma, don tabbatar da dorewar zaman lafiya dake dawowa jihar nan, musammman tsakanin Fulani makiyaya da takwarorinsu manoma,” in ji shi.