✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shigowar sanyi: SEMA ta raba wa almajirai 200 kayan sanyi da barguna a Yobe

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Yobe SEMA, ta ziyarci wasu tsangayoyi biyu na almajirai a jihar don raba musu kayan sanyi. Sakataren Hukumar a…

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Yobe SEMA, ta ziyarci wasu tsangayoyi biyu na almajirai a jihar don raba musu kayan sanyi.

Sakataren Hukumar a Jihar Yobe Dokta Muhammad Mai Goje, ya ce tsangayoyin suna unguwannin Goniri da Mandunari ne a Karamar Hukumar Gujuba.

Ya ce makarantun tsangayar da hukumar ta ziyarta dukkansu suna da almajirai fiye da 100 kowace.

Dokta Goje ya ce Hukumar SEMA ta raba musu wannan kayan sanyi da barguna ne don taimaka musu ne saboda kasancewarsu almajirai da ba su da mai yi musu a irin wannan lokaci na sanyi da ya kunnno kai saboda kare su daga tsananin sanyin.

Almajiran da malamansu sun gode wa Gwamnatin Yobe da Hukumar SEMA bisa wannan tallafi da aka yi musu.