✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin cire tallafin man fetur zai bunkasa tattalin arzikin kasa?

A wani taro kan ci gaban tattalin arziki da aka gudanar a Kano, a kwanakin baya, Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi 11 ya…

A wani taro kan ci gaban tattalin arziki da aka gudanar a Kano, a kwanakin baya, Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi 11 ya bai wa Gwamnatin Tarayya shawarar ta cire tallafin da take bai wa harkar man fetur a kasar nan, in ba haka ba tattalin arzikin kasar nan zai ruguje. Wannan shawara ta Sarki ta haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya. Hakan ya sa wakilanmu suka jiyo mana ra’ayoyin al’ummar kasar nan a kan shin cire tallafin man fetur zai iya bunkasa tattalin arzikin kasa?

Bai kamata a cire tallafin ba–Aminu Muhd Gofai Limawa

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

Mu da muke yin bumburuntun mai idan Gwamnatin Tarayya ta cire tallafin man fetur kasuwarmu ta mutu, abin da muke samu zai ragu, kuma tattalin arzikinmu zai gurgunce. Saboda haka ba na goyon bayan a cire tallafin saboda haka kamata ya yi Gwamnatin Tarayya ta kara ninka tallafin saboda rayuwarmu da ta iyayen gidanmu ta yi kyau.

Ba zai bunkasa tattalin arziki ba – Malam Umar Ibrahim

Daga Tijjani Usman Bello, Maiduguri

Cire tallafin man fetur, ba zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan ba, kuma cire tallafin man fetur daga Gwamnatin Tarayya ba alheri ba ne ga talaka. Domin hakan zai wargaza tattalin arziki ne da samun nakasu a harkar ilimi da hauhawar farashin kayayyakin masarufi da sufuri, saboda gwamnati ita ce uwa ma-ba-da-mama ga kowane dan kasa.  A duk lokacin da aka ce gwamnati ta cire tallafi to talaka ne kawai zai ji a jikinsa, Don haka bai dace gwamnati ta cire tallafin da take bai wa bangaren man fetur ba.

Babu wani tallafi damfara ce –Tope Bello

Daga Abbas Dalibi, Legas

Ni a nawa ra’ayin a kuma iya sanina maganar tallafin mai damfara ce kawai da kuma tsabar yaudara. Domin ta yaya za a ce kasarmu da take samar da man  fetur sannan a yi maganar wani tallafin mai, wannan ai ka ga damfara ce kurum don haka cire shi ko kyale shi ba zai yi wani tasiri wajen rage radadin talauci ko kara talauci ba. Abin da kasarmu ke bukata shi ne jagoranci nagari, kyakyawan jagoranci da shugabannin nagari su ne za su yi tsare- tsaren da za a samu raguwar talauci a tsakanin al’umma amma cire tallafin mai ko bari ba zai yi wani tasiri ba domin damfara ce kawai .

Zai jawo hauhawar farashin kaya–Rasheed Bolarinwa

Daga Abbas Dalibi, Legas

Cire tallafin mai  zai  janyo hauhawar farashin kayayyakin masarufi kuma ya kara kuncin talaucin da ake fama da shi. Saboda tattalin arzikin kasarmu ya dogara ne kacokan kan albarkatun man fetur, idan farashinsa ya hau dole ne ya janyo hauhawar farashin sufuri da kayayyakin masarufi na yau da kullum da suka hada da abinci da kayayyakin da matsakaita da kananan masana’antu ke sarrafawa da sauransu. Hakan zai sa a samu karuwar talauci a tsakanin jama’a domin dole wasu masana’antu su rufe, dimbin mutane su rasa ayyukan yi a koma rayuwar nan ta hannu baka hannu kwarya. Don haka a ganina ba da tallafin man fetur yana da amfanin ga al’ummarmu, kuma cire shi zai kara janyo talauci a tsakanin al’ummar kasarmu.

Kada a cire tallafin mai a yanzu – Isa Babayo

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

A ganina koda cire tallafin man fetur zai taimaka wajen bai wa jama’ar kasa hanyoyin habaka tattalin arziki kuma ita kanta gwamnati ta samu karin hanyoyin kudaden shiga, tunda wannan gwamnati ce mai son talakawa, shawarata kada ta cire tallafin a yanzu saboda cire shi zai iya jefa Najeriya cikin wani mugun hali. Domin in aka dubi yanayin rayuwa da talakawa suke ciki idan aka cire shi a yanzu, komai zai yi tsada. Kamata ya yi gwamnati ta samar da ayyuka ga matasa da sana’o’i da za su dogaro da kai, ta bunkasa harkokin N-Power ya zama mutanen karkara sun samu aikin dogaro da kansu saboda mafiya yawan talakawa mazauna karkara ne. Idan mutanen kauye suka wadata arziki zai yalwata, kuma kaifin talauci zai ragu. Saboda haka a wannan yanayin sai gwamnati ta yi amfanin da wannan damar ta cire tallafin saboda talakawa ba sa cikin damuwa.

’Yan kasuwa ne za su ci moriyar haka  ba  talaka ba –Malam Manu Usman

Daga Tijjani Usman, Maiduguri

Cire tallafin man fetur ba zai kawo wani bunkasar tattalin arzikin kasa ba. Saboda za a bar ma ’yan kasuwa dama ne su kuma sai abin da suka yi, alhali kuma za su yi son ransu ne su tsawwala komai ta yadda talaka ba zai iya saya ba. A daidai wannan lokacin da talaka ke neman sauki daga gwamnati shi kenan sai kayyakin masarufi su yi tashin gwauron zabo, talaka ya ji a jikinsa. Domin janye tallafin nan ba zai sanya a ce darajar kudinmu ta karu ba, sai dai ma ta yi kasa, to duk inda ta yi kasa shi kuma talaka zai ji a jikinsa, saboda rage darajar kudi na kawo kuncin tattalin arziki, don haka ba na goyon bayan janye wannan tallafi.