✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin kun gamsu da ministocin da Buhari zai nada?

Bayan shafe kusan wata biyu da rantsar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi ta shan suka daga ’yan adawa kan rashin nada ministoci. A…

Bayan shafe kusan wata biyu da rantsar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi ta shan suka daga ’yan adawa kan rashin nada ministoci. A makon jiya ne ya mika sunayen ministoci ga Majalisar Dattawa inda hakan ya ja hankalin al’ummar kasar nan game da jerin sunayen mutanen da ya mika don tantance su a ba su mukamin ministocin. Wakilanmu sun ji yo ta bakin al’umma a kan nadin inda suka rika bayyana mabambantan ra’ayoyi kamar haka:

Wadannan ministoci sun yi daidai – Ibrahim Musa Kadewa

Daga Lubabatu Garba kano

Ni a ra’ayina ministocin nan sun yi domin idan aka duba mutanen da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zabo mutane ne nagartatatu kuma hazikai.  Mafi yawancinsu an gwada su an ga irin ayyukan da suka yi a baya domin ci gaban kasar nan. Fatarmu Allah Ya taya su riko.

Ban ji dadi ba, ban kuma yaba ba –Abdulkadir Muhammad

Daga Tijjani Usman Bello, Maiduguri

A gaskiya mun yi zaton Shugaba Buhari zai zakulo fitattu kuma nagartattun mutanen da za su tallafa masa a yi aiki tukuru cikin gaskiya da rikon amana. To amma yanzu na fahimci cewa kamar jiya-i-yau ce, domin ba ta canja zane ba, saboda mafi yawan ministocin da ya yi aiki  da su ne a baya, ya kamata ya canja a samu sauyi abubuwa su yi  kyau. Ni ban ga bambancin da, da yanzu ba. A gaskiya ni dai ban yaba ba, akwai gyare-gyaren da ya kamata Shugaba Buhari ya yi a miKa wadannan Ministoci, saboda wadansu ba sa ziyartar jama’arsu ballantana mu san su har ma su kai ga taimaka mana. To ka ga ke nan kamar an yi ba a yi ba  ke nan, a don haka ban ji dadi ba ban kuma yaba ba.’

Ba yabo ba fallasa – Adamu Haruna

Daga Tijjani Usman Bello Maiduguri

Eh to a gaskiya ni ban ji dadin nada wadannan ministoci da Shugaba Buhari ya yi ba, saboda muna bukatar sabon zubi. Idan aka ce sabon zubi ne to ya zama sabo ne ba a sake maimaita na baya ba. Kamar mu a nan Borno ministanmu ya yi a baya amma ba mu ga abin da ya kulla a ofishinsa ba ballantana ya kawo gare mu nan. Ai ana bukatar ci gaba ne to shi ke nan sai aka sake dauko wadanda ba su tabuka komai ba, munanan a gidan jiya ke nan.  Ya kamata a ce Shugaba Buhari ya dauko wadansu sababbi ful tunda akwai su ba wai babu su ba ne, kuma su ma wadannan din ba suke nan ba kuma ba sun fi kowa kwarewa ba ne a aiki. Duk da cewa akwai sababbin da ya dauka, ya kamata a ce sababbin sun fi haka yawa. Kuma in aka duba babu matasa a cikinsu, kuma mu matasa muna bukatar wakilci a Majalisar Zartarwa ta Kasa. Duk da cewa ba mu san nufin Shugaba Buhari ba, amma ya kamata a ce an dauko wadansu sababbi ne su ma a ga tasu kwarewar. Don haka zan ce ba yabo ba fallasa.

Nadin ya yi daidai – Haruna Mai Agogo

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Ra’ayina a kan nadin wadannan ministocin shi ne, ya yi daidai musamman ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada su saboda irin gudunmawar da suka bayar ta fannin nuna hazaka da kwazo da kishin kasa wajen gudanar da ayyukan da suka yi a baya. Ina ganin su kuma sababbin mutanen da Shugaba Buhari yake son ya yi tafiya tare da su sun cancanta ne shi ya sa ya ambaci sunayensu inda nake fatar jama’ar kasa baki daya za mu bayar da tamu gudunmawa da fatan alheri gare su domin ci gaban kasarmu Najeriya.”

An yi abu mai kyau – Zubairu

Daga Kabir Yayo Ali, Ibadan

Alhamdulillahi domin ina ganin alal hakika an yi abu mai kyau wajen nadin sababbin ministocin da muke kyautata zaton alheri ne zai biyo bayan nadin nasu. Saboda ga dukkan alamu an zakulo mutanen kwarai da muke fata da yardar Allah za su ba Shugaba Buhari shawara mai kyau da taya shi jagorantar kasar nan zuwa ga ci gaba. Ina shawartar sababbin ministocin su sani cewa an zabo su ne daga cikin miliyoyin jama’a bayan an tankade da rairaya aka ba su wannan amana, ya kamata su rike amanar tsakani da Allah su yi aikin da zai haifar da da mai ido.

Akwai kura-kurai a jerin ministocin – Muhammad Nasir Muhammad

Daga Lubabatu Garba kano

Ni ina ganin akwai kura-kurai a cikin jerin ministocin da aka nada domin babu matashi ko daya a cikinsu. Idan aka duba za a ga cewa tunda aka fara dimokuradiyya a kasar nan a koyaushe tsofaffi ake ba wa ministoci, kuma ba sa yin wani abin a zo a gani. Ya kamata a gwada matasa a ga irin rawar da za su taka. Kowa ya san abin da matashi zai yi tsoho ba zai iya ba. Ban da wannan, idan muka duba za mu ga cewa matasa ne suka yi ruwa suka yi tsaki wajen tabbatar da nasarar Gwamnatin Buhari. Ina ganin ya kamata su ma a saka musu.