✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin mukan ci sinadaran roba a abinicinmu?

Shin ko za mu iya cin kananan sinadarai na roba (plastic) a abincinmu? Wadanne irin matsalolin lafiya mutum zai iya samu idan yana yawan cin…

Shin ko za mu iya cin kananan sinadarai na roba (plastic) a abincinmu? Wadanne irin matsalolin lafiya mutum zai iya samu idan yana yawan cin abinci ko abin sha a cikin kayan roba ko leda da ma takarda? 

Amsa: Eh, kwarai kuwa, mutane kan iya cin sinadaran roba a abinci da abin sha ba tare da sun sani ba. Ka san ita ainihin roba a jikin itaciya ake tatso ruwanta a kara wasu sinadarai, sa’annan a malkwayata zuwa irin siffar da ake so, walau kofi ko faranti ko jarka ko baho ko takalma ko ma leda da sauransu. Ban da roba ta jikin itaciya, a yanzu har daga danyen man fetur ma ana iya kera roba wadda aka fi sani da plastic. To ita kanta robar da sauran sinadaran da akan kara mata yayin wannan aiki takan iya narkewa idan ta sha zafi ko ta sha ajiya, kananan sinadaranta wadanda watakila ido ba ya ganinsu, su fara barbasa haka nan ko kuma a cikin abinci ko abin sha. To ka ga ke nan idan ta fetur ce idan ta narke sinadaran fetur ne zai barbasa, haka nan idan ma ta robar jikin itaciya ce ita ma dai za ta iya barbashewa.

Hukumomin lafiya irin su Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Hukumar Kiyaye Yaduwar Cututtuka (CDC) ba su ba da tabbacin cewa sinadaran roba da plastic da ma na soyoyon Styrofoam da ke barbasa cikin abincinmu ko abin shanmu suna da wata illa ta kai-tsaye ga lafiyarmu ba. Idan ma akwai illar to sai dai idan sinadaran masu dimbin yawa ne suka shiga abinci ko abin sha. Misali, akwai wani sinadari da akan kara a robobi wai shi Bisphenol A, ko BPA wanda gwajin dakin bincike ya tabbatar yana yi wa dabbobi illa ta hanyar gurbata wasu kwayoyin halittunsu, wanda hakan ke nufin zai iya gurbata kananan halittun dan Adam. Wannan ne ya sa akan dauki matakin cewa duk robobin abinci ko na abin sha ba za a yi su da sinadarin BPA ba. Haka nan masana sun ce yawan dafa abinci da cin sa a wani faifan leda na alminiyum shi ma zai iya sa mana sinadarin alminiyum da yawa a jini, har ya wuce misali. 

To ala-ayyi-halin dai wannan matsaya za ta iya samun goyon baya daga nazarin cewa babu wani ciwo guda da za a iya nunawa a jikin dan Adam a ce sinadaran roba da plastic ne suka jawo masa. Amma dai duk da haka yana da kyau a ce a rika taka-tsantsan.

Hanyoyin taka-tsantsan din kuwa sun hada da daina amfani da robobi wajen ajiyar abinci ko abin sha, domin zafin abincin ko abin sha irin su kunu zai iya narkar da sinadaran robar da kuma barin ajiye ruwan roba da na leda a rana domin kada rana ta narkar da sinadaran robar su shiga cikin ruwan. Yana kuma da kyau a rika duba irin sinadaran da ake sarrafa wadannan robobi da su domin guje musu idan za a yi amfani da su wajen saka abinci. Misalai su ne, idan aka sayi roba ko plastic aka duba bayanta aka ga alamun sinadarai masu illa sai a daina zuba abinci ko cin abinci a cikinsu. Wadannan sindarai su ne kamar yadda muka fada a sama alamun haruffan BPA, wato idan aka ga haruffan BPA to kada a sa abinci ko abin sha a ciki. Sauran robobin da za a kaurace wa zuba abin sha su ne masu haruffan PET, sai na PbC. Akwai masu haruffan HDPE da LDPE da aka ce su ne ba matsala ko da an zuba abinci ko abin sha a ciki.

Ko ma gaba daya a koma yadda ake yi da. A da can a akushi da languna da tasa da tangaraye aka san muna cin abinci, amma yanzu zamani ya zo ya kawo mana abubuwan da muke da shakku a kansu.

 

Me ke sa mutum ya rika jin jiri idan ya tashi lokaci guda bayan ya dade a zaune?

Daga Saminu Yelwan Shendam

Amsa: Wannan na faruwa ne saboda bugun jini na sauka idan mutum ya tashi daga zaune zuwa tsaye farat-daya lokaci guda. Wadansu mutane masu lafiya na iya samun irin wannan jefi-jefi, amma idan ya zama mutum kullum sai ya ji wannan alama ce ta cewa yana bukatar binciken lafiyarsa.

 

Ni kuma matsalata yawan zufa. Ko hakan matsala ce?

Daga Sani Ali

Amsa: Ya danganta da irin lokacin da kake zufar. Idan yanayin zafi ake kuma kuma kowa na kusa da kai yana korafi ko yana jin zafi ko yana zufa ai ba komai. Amma idan yanayin ba na zafi ba ne, kuma kowa daidai yake ji, kai kadai kake jin zafi da zufa to akwai matsala, sai ka je an binciki mene ne dalili.

 

Da gaske ne yawan cin kankana yana maganin ciwon koda? Ko kuwa rage kaifin ciwon yake?

Daga Anti Husna, Bakori da Muhammad Tsara, Lafiya

Amsa: A’a yana da kyau dai a kowane lokaci ga mai lafiya ya rika yawan shan ruwa da wani abu mai ruwa-ruwa kamar kankana. Sai dai idan mutum likitansa ne ya hana shi saboda wani ciwo, kamar ciwon koda. Wato ke nan idan mutum yana da ciwon koda a likitance kamar idan ta doso mutuwa rage masa shan ruwa da abubuwa masu ruwa ma ake.

 

Mene ne amfanin goge dattin kunne da wasu suke yi da tsinke mai auduga?

Daga Aminu Yakubu

Amsa: A’a ba wani amfani domin masana lafiyar kunne a yanzu sun ce maimakon a sa tsinke a kunne gara a sayi maganin digawa a kunnen domin narkar da dattin kunnen. Domin ana samun hadarin tura dattin can ciki da tsinke, ko ma a je a ji ciwo. Idan da hali ma an fi so shi likitan kunnen a gan shi ya leka ya gani shin datti ne ko kuwa wani abu daban ne a cikin kunnen. Sai dai irin susar  nan idan kunne na kaikayi an ce ba matsala in dai ba da abu mai tsini ba ne.