✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin taron da Buhari ya yi da gwamnoni zai magance matsalar tsaro?

Matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan ta zama ruwan dare, inda a kusan kullum sai ka ji an kai hari wani gari ko a sace…

Matsalar tabarbarewar tsaro a kasar nan ta zama ruwan dare, inda a kusan kullum sai ka ji an kai hari wani gari ko a sace mutane domin neman kudin fansa, baya ga rikicin Boko Haram da dai sauran matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan. Wakilanmu sun jiyo mana ra’ayoyin wadansu jama’a kan shin taron da Shugaba Buhari ya yi da gwamnonin jihohi 36 da kuma shugabannin tsaro kan tabarbarewar tsaro zai iya magance  matsalar?

Babu wani amfani da taron zai yi – Bolori Muhammad M Lantewa

Muhammad Aminu Ahmad

Ba yau aka fara irin wannan taro ba, amma me ya haifar? Mun dade muna jin ana irin yin tarurruka makamacin haka, babu wani abu da muka ga ya canja kullum a gidan jiya muke a harkar tsaro a wannan kasa. Sai  dai tunda wannan taro shi ne irinsa na farko a shigowar wannan gwamnati muna fata za a dauki wani mataki da zai kawo karshen wannan matsala ta rashin tsaro da kasar nan take fama da ita.”

 

Ba zai sauya komai ba – Umar Ahmad Abubakar Gombe

Dalhatu Liman

Ba tun yau  aka saba kiran irin wannan taro na masu ruwa-da-tsaki ba, a fadar Shugaban Kasa domin tattauna matsalar tsaro a kasar nan.

Ganawar da aka yi  da gwamnoni da kuma hafsoshin tsaro ba za ta sauya komai ba, muddin ba a fito an dauki kwararan matakan da za su yi wa tufkar hanci ba. Dole gwamnati ta tashi tsaye wajen inganta  jami’an tsaro, ta ba su kayan aiki  na zamani, a rika ba su duk wasu hakkokinsu da kudaden alawus. Wadannan matsaloli ne da ba sa bukatar kiran taro a fadar Shugaban Kasa kafin a magance su.”

Lallai hakan zai bunkasa tsaro – Zainab Yusuf (Zee ’Yar Mamanta)

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Kwarai kuwa, hakan zai kawo ko ya rage aukuwar kai hare-hare da yin garkuwa da mutane a sassan kasar nan.  Idan Shugaban Kasa ya samu hadin kan wadannan shugabanni wato gwamnoni da shugabannin hukumomin tsaro, to za a yi wa tufkar hanci, kuma yin hakan shi ne daidai.”

Zai Taimaka wajen Magance Matsalar – Auwal Rabi’u Abdullahi Jos

Dalhatu Liman

Hausawa suna cewa da dan gari ake cin gari. Wannan taron  zai bayar da gudunmawa kwarai wurin magance matsalolin tsaro da suke addabar jihohin Najeriya. Su kuma gwamnonin, Allah Ya ba su ikon ba da gudunmawa 100 bisa 100 wurin tona asirin ’yan ta’adda a jihohin da ake fama da rashin tsaro. Ga, jami’an tsaron Najeriya, mun sani kuma tarihi ya nuna cewa kwararru ne wurin magance matsalolin tsaro. Muna rokon Allah Ya kara musu basira da karfin gwiwa wurin tabbatar da zaman lafiya a jihohinmu. Muna rokon Allah Ya ba mu zaman lafiya a jihohinmu da Najeriya baki daya.”

Babu abin da zai canja –Ummulsalma Ibrahim

Ahmed Garba Mohammed a Kaduna

Sau nawa aka yi irin wannan taro amma babu abin da ya canja? Saboda haka ina da shakku duk da Shugaban Kasa ya gana da su babu wani abu da zai canja domin ai ba yau aka fara irin wannan taron ba, a can baya da aka yi me ya haifar babu sai dai kawai mu ci gaba da taya su da addu’a.”

Hakika zai taimaka wajen shawo kan matsalar – Sani Kawu Muhammad  Wudil

Muhammad Aminu Ahmad

Ni dai a ra’ayina, taron insha Allahu zai taimaka wajen kawo zaman lafiya, domin idan an ce an zauna hakan babu tautaunawa a tsakanin manya, to ba za a gano hanyoyin da za a kare wadannan matsaloli da suke tafiya a cikin wannan kasa tamu ba. Yin hakan yakan iya sa wa daga ciki akwai wadanda za su iya zuwa kananan hukumomi ko kauyukansu da za su iya ba da bayanai na wasu batagari da ke zama a tsakanin al’umma. Don haka yin wannan taro zai taimaka sosai wajen dakile matsalar tsaron da muke fama da ita.”