✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ya dace a rage yawan ’yan Majalisar Kasa?

A kwanakin baya Sanata Rochas Okorocha ya bada shawarar a rage yawan ’yan majalisar da ake da su a kasar nan, ya zama kowace jiha…

A kwanakin baya Sanata Rochas Okorocha ya bada shawarar a rage yawan ’yan majalisar da ake da su a kasar nan, ya zama kowace jiha tana da Sanata daya da ’yan Majalisar Wakilai uku. Sanatan ya ce kamata ya yi a hanzarta rage yawansu, don rage barnatar da makudan kudi a kansu. Wannan magana ta sa jama’a da dama har da ’yan siyasa sun tofa albarkacin bakinsu. Wakilanmu sun jiyo ra’ayoyin jama’a a kan wannan lamari kamar haka:

Ya dace a rage yawansu – Alhaji Suleiman Gaya Musa Kutama, Kalaba

Gaskiya ya dace Shugaban Kasa ya rage yawan ’yan majalisa domin kudaden da ake kashe musu sun yi yawa ga shi kuma wadansu ma daga ciki ko mazabunsu ba sa ziyarta. Wadannan kudade da ake kashe wa ’yan majalisa gara a yi amfani da su wajen yi wa kasa aiki.

Ya kamata a rushe majalisun gaba daya –Rashida Hassan Nuhu

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

Rushe majalisun biyu ma ya fi, domin da su da babu duk uwarsu guda, rashinsu ya fi amfani saboda idan babu su bilyoyin kudin da ake kashe musu za a iya amfani da su a gina hanya daga Legas zuwa Maiduguri ko daga Ribas zuwa Sakkwato. Kuma sun  isa a gina manyan asibitoci a kowace jiha da samar musu da magani kyauta. Ba mu ga amfaninsu ba, Shugaban Karamar Hukuma ma ya fi su amfani ga talakawa.

Kuma suke hana wa Shugaban Kasa aiki, ya zo da niyyar abin kwarai, amma komai sai an kai majalisa wai, a ce sai sun yarda.

Rushe su ya fi amfani – Malam Umar Goni

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya ni a nawa ra’ayin ’yan majalisarmu ta Dattawa da ta Wakilai duk ba su da wani amfani. Mene ne suke yi mana in ban da kawo wa Shugaban Kasa cikas wajen tafiyar da ayyukan raya kasa. Don haka ba wai a rage yawansu muke bukata ba, a’a idan da hali a rushe majalisun gaba dayansu, zai fi mana zama alheri. Maimakon tarin kudaden da ake ba su da sunan yin ayyuka a mazabunsu da albashi da alawus gara a hada wadannan kudade a gyara makarantu da asibitoci domin amfanin talakawa. Lokacin su Sardauna ai ba haka muke ba.

Ragewar za ta yi alfanu ga kasa – Alhaji Danbaba Ali Zariya

Musa Kutama, Kalaba

Rage yawan ’yan majalisa tabbas yana da kyau dama ai wani daga cikin tsofaffin shugabannin kasar nan, an ce ya taba cewa kuskurensa ne da ya ba majalisa karfi, ina ga ragewar za ta yi alfanu ga kasa da kuma al’ummarta.

Don ka ga kudin da suke kashewa wajen kasafin kudi da alawu-alawus na zama da na kwamitotci da suke samu ya ragu kudin sai a karkata su wajen yi wa kasa da jama’arta aiki.

Rage yawan kudin da ake kashe musu ya fi – Alhaji Sani Ragada Motors

Daga Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi

A  ra’ayina bai kamata a rage yawan ’yan majalisa ba, abin da ya kamata shi ne a rage yawan kudin da ake kashe musu, saboda ba su da amfani ga jama’ar da suke wakilta. Sun ce su iyakarsu yin doka ba su ba da kwangila to tunda haka ne mene ne amfanin a yi ta zuba musu kudi daga su sai matansu da ’ya’yansu. Domin in an ce za a rage su kila na kwarai za a rage a bar ruwa-ruwa, ka ga an koma baya ke nan maimakon a samu ci gaba.

Ina goyon bayan a rage – Bello Abubakar Garwa

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Rage yawansu din shi ne zai kawo mana ci gaba a kasar nan. Hujjata ita ce irin kudaden da ake ba su sun yi yawa, kuma mu talakawa ba ma gani a kasa. Domin babu wani aiki da za ka gani, wai a ce dan majalisa ne ya zo ya aiwatar don amfanin al’ummarsa. Kuma duk wanda ya zo ya nemi al’umma suka ba shi kuri’unsu, kuma suka amince suka zabe shi, kamata ya yi idan ya je majalisar nan ya tabbatar ya aiwatar da wani abu domin amfanin wadannan jama’a tasa. Amma sai ’yan kadan ne daga cikinsu, suke da kishin yin haka. Don haka ina goyon baya dari bisa dari idan hakan zai zama alheri ga kasarmu, to a rage yawansu.