✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin ya dace a rika sanya siyasa a harkokin tsaro?

A daida lokacin da kasar nan ke ci gaba da fuskantar barazanar tsaro a wasu bangarori, duk da ana samun ci gaba da sauki a…

A daida lokacin da kasar nan ke ci gaba da fuskantar barazanar tsaro a wasu bangarori, duk da ana samun ci gaba da sauki a wasu sassan, wadansu na amfani da matsalolin tsaro wajen farfaganda da siyasa. Wannan ne ya sa wakilan Aminiya suka zagaya domin ta bakin mutane, a kan shin ya yi daidai mutane su rika sanya siyasa a lamarin da ya shafi tsaro? kuma ga abin da suke fada:

 

Akwai hadari hada siyasa da tsaro – Ustaz Ahmad Muhammad

Kabir Yayo Ali, Ibadan

Ustaz Ahmad Muhammad Amin Babban Limamin Sakandaren Sojoji na Apata: “A ra’ayina ba daidai ba ne Shugaban Kasa ya bari a rika sanya siyasa cikin harkokin tsaron lafiya da dukiyar jama’ar da yake jagoranta. Shugaban Kasa, uba ne ga kowa da wanda ya zabe shi da wanda bai zabe shi ba duka ’ya’yansa ne da hakkin lura da tsaron lafiyarsu ya rataya a wuyansa. Akwai hadari ga cakuda siyasa da tsaro. Ya kamata a yi hattara a kan wannan al’amari domin sam bai dace a hada siyasa da tsaro ba.”

 

Bai dace siyasa ta shiga harkar tsaro a Najeriya ba – Al-Kassim Haruna Tahir

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Al-Kassim Haruna Tahir: “Daya daga cikin romon dimokuradiyya shi ne bai wa ’yan kasa ’yancin zaben wadanda suke tunanin za su samar wa al’umma ingantaccen shugabanci mussamman fannin tsaro. Shi ya sa a kasashen da suka ci gaba kamar Amurka, kafin zabe masana kan harkar tsaro ke mayar da hankali matuka wajen nazarin ’yan takara a kan yadda za su dauki harkar kare iyakoki da al’umma da dagantakarta da kasashen waje ta harkar tsaro da kuma duk wata tarzoma da za ta kawo wa kasar tashin-tashina, sai su bai wa mutanen kasa shawarwari a kan yadda za su tafiyar da yanayin yin zaben. Ka ga hakan na nuni da cewar siyasa da harkar tsaro suna tafiya hannu da hannu ne. A Najeriya, matsalar bambancin addini da kabilanci, sa’annan cin hanci da rashawa sun sa hada harkar siyasa tare da tsaro ke munana.

Abin takaici shi ne yadda ’yan siyasa a Najeriya ke wasa ko kalubalantar juna a kan rayukan ’yan kasa nawa aka kashe a lokacin da kuke kan karagar mulki’? Wannan ba karamin tashin hankali ba ne. Akwai misalai da dama da ke nuni da cewa matsalolin kasar nan kamar fada tsakanin makiyaya da manoma da fashi da makami da Boko Haram, ko garkuwa da mutane duk babu ’yan siyasar ba su da niyyar ganin an shawo kansu. Kabilanci da cin hanci da rashawa ke ja kwata-kwata bai dace siyasa ta shiga harkar tsaro ba.”

 

Gaskiya bai daceba – Isa Muhammed Dalibi

Kabir Yayo Ali, Ibadan

Isa Muhammed dalibi ne a Poly ta Ibadan: “A Gaskiya bai dace siyasa ta shiga cikin harkokin tsaron kasa ba. Kamata ya yi kowane bangare ya ci gashin kansa domin harkar siyasa daban harkar tsaro daban. Idan aka yi kuskuren hada su waje daya a Najeriya to za mu yi da-na-sani domin bayanan da muke samu a baya da ma yanzu shi ne cewa wadansu ’yan siyasa sun shiga cikin harkokin tsaro dumu-dumu, inda suke yin amfani da wannan dama suna cin mutuncin mutane. Kuma hakan ne ya haifar da gurbacewar tsaro a Najeriya.”

 

Shigar da siyasa cikin lamarin tsaro kuskure ne – Sabi’u Yunusa

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Sabi’u Yunusa: “Idan har aka ce shugabanni suna sanya siyasa cikin harkar tsaro to suna aikata abu da kai-tsaye bai dace ba. Ba zai yiwu a matsayinka na shugaba ka san cewa ana fama da wata matsalar tsaro a wani yanki ko kabilar da ba taka ba, amma ka dauke kanka daga kan abin har sai lamarin ya baci. Wannan ba daidai ba ne. Sha’anin tsaro shi ne abin da kowane shugaba ya kamata ya fi ba muhimmaci, duk abu mai muhimmanci kuma dole ne a cire siyasa daga cikinsa.”

 

Bai dace ba–Kabiru Yusuf

Daga Lubabatu I. Garba, Kano

Kabir Yusuf: “A gaskiya bai dace a rika sanya siyasa cikin lamarin da ya shafi tsaro ba, saboda idan ana maganar tsaro ana batun kare rayukan jama’a baki daya ne. Duk shugaban da ya hau mulki bai kamata ya yi wasa da sha’anin tsaro ba ko ya shafi yankin da ya fito ko bai shafa ba. Shugaba ya yi duk mai yiyuwa wajen tabbatar da cewa an samu cikakken tsaro a ko’ina ta hanyar wadata jami’an tsaro da kayan aiki na zamani da kuma kula da walwalarsu.”

 

Sanya siyasa a harkar tsaro bai dace Ba – Tukur Suleiman Bello

Daga Ahmed Ali, Kafanchan

Tukur Bello Sulaiman: “Gaskiya a tawa fahimtar bai kamata ba domin kuwa ita siyasa tana dauke da ra’ayi, harkar tsaro ta kunshi siyasa da ’yan siyasar da ma wanda ba ya siyasa. Amma kasancewa akwai mutane wadanda suke amfani da wannan damar domin neman abin duniya ko kuma neman gazawar gwamnatin da take da alhakin kulawa da wannan tsaro sai su yi ta nuna wa al’umma gazawar gwamnati, ko da kuwa ana iya kokari. Daga wani bangaren kuwa za ka ga cewa jami’an tsaro su kuma suna amfani da ita matsalar tsaro domin samun abin da za su sa a aljihunsu kasancewar matukar matsalar tsaron ta kare, to su kuma kudin da ake ba su ya tsaya, to sai ka ga suna sa siyasa a ciki. Don harkar tsaro ba ta bukatar saka siyasa a ciki domin rayuwar kowa na bukatar tsaro da kulawa.”