Da Dumi Dumi

Shin ya dace gwamnati ta ba ‘yan ta’adda kudi domin daina garkuwa da mutane?

Daga Tijjani Usman Bello, a Maiduguri.
Daga Tijjani Usman Bello, a Maiduguri.

Ban yarda a ba su Kudi ba – Kabiru Iliyasu

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Bai kamata ayi haka ba, saboda idan an basu zai kara musu,karfi kuma ba zasu daina ba, kudin da zuke karba ma, yaya suke dasu,kuma bayin Allah suna cikin wani hali, gara a taimaki jama’a wanda basu dashi, wannan zai sa Allah ya sauwake ma abin da suke yi mana, saboda idan ma, an basu ai an karawa azzalumai karfi ne, da a basu kudin gara a bawa bayin Allah da suke bukatar taimako, domin ganin irin halin da muke ciki, watakila Allah ya kawo mana sauki akan lamarin.

 

Ban goyi bayan a ba su kudi ba – Rabi Muhammad Jama’are

ADVERTISEMENT

Daga Ahmad Muhammad Bauchi.

A gaskiya bai kamata a rika baiwa yan ta’adda da sauran masu aikata laifi makudan kudade ba, don a rarrashesu su daina ta’addancin da suke yi, don kuwa basu kudin zai kara musu karfi  ne kawai su sayo sabbin makamai don su ci gaba da uzurawa jama’a kuma tunda gwamnatin take yin haka me ya ragu babu, kullum wadanda ake kashewa suke fadawa cikin wannan bala’i sune suke kara yawa.maimakon haka a fito da tsari kawai da zai magancesu, ya inganta tsaro.

 

Bai kamata a ba su kudi ba – Malam Sadik Abubakar

Daga Tijjani Usman Bello, a Maiduguri.

Ai wannan bai kamata ba, ace an baiwa wani mai aikata barna kudi, saboda idan an basu to kamar an kara masu karfin gwiwar ci gaba da aikata wannan mummunan aiki ne, domin ko da an jawo ra’ayinsu dasu, daina ga Kudi ambasu, to ba’a da tabbacin zasu yi yayi abin da aka basu suyi, zasu iya gudu su sake komawa can Jeji su ci gaba da aikata abin da suke so ba tare da wani yace masu uffan ba, kuma karka manta kafin su koma zai iya zuwa  su sayi Makamai da kayayyakin aikin nasu na ta’addanci, to kaga an yi ba a yi ba, to ni bana goyon bayan gwamnati ta bawa wadannan Mutanen Kudi, don basu Kudi da nufin hana su abin da suke yi ba shi da wani amfani, don haka gara ayi ta farautarsu ana kame su, a nuna masu illan halayennasu, amma da zarar an basu Kudi to zasu rika jin dadin yadda suke yi sai su ci gaba da mummunan halayensu. Saboda haka ni bana goyon bayan a basu Kudi don su bari, idan ana so su bari ko dai a bisu ta lalama su bari ko kuma a nuna masu karfin Hukuma wannan shine kawai.

 

Idan za su daina ai sai a ba su kudin – Malam Yahaya Amadu

Daga Tijjani Usman Bello, a Maiduguri.

Idan basu wannan Kudin zai Iya zama sanadiyyar sa su, su daina abin da suke, ai sai a basu domin, abin da suke nema kenan to idan aka basu za’a iya sa ran cewar zasu bari, don kaga idan ba’a basu ba to ta iya yiwuwa barnan da suke yi tafi haka, sai ya kasance ba ma hanya suke tarewa ba a’a hatta gidaje zasu rika shiga suna kwashe Mutane suna garkuwa dasu, to amma don dadile haka din sai a basu Kudin da nufin jawo hankalinsu su bar abin da suke yi, idan kuma an basu kudin sai a jawo hankalinsu dasu bar abin da sukeyi don babu kyau, kuma sai ayi kokarin samar masu da aikin yi don kada a barsu haka nan, ganin cewar wai an basu kudi shike  nan ba zasu sake koma wa wancan barnan ba, a’a ai kudin zai kare sabo da haka sai a samar masu da aikin yi don kaga shi rashin yi  shike haifar da dabi’o’i ire-iren wadannan to a samarwa da Matasa aikinyi shine kawai zai magance wannan mummunan dabi’a, to ni ina mai goyon bayan basu kudin tun da ai kudin suke nema sai gashi an basu to ai kuma babu sauran wani kama Mutum din da zasu yi .

 

Bai kamata a ba ’yan ta’adda kudi ba – Tijjani Kolo

Daga Ahmad Muhammad Bauchi.

Gaskiya ya kamata gwamnati ta rika nazari wajen baiwa ‘yan ta’adda kudi, duk da cewa an ce yin sulhu alherine, a cikin alkur’ani, amma da mutumin kirki mai tsoron Allah ne, wanda aka tabbatar tabatatciyar tuba zai yi, maimakon ba su kudi, ayi musu shiri irin yadda Marigayi ‘Yar adua ya yiwa tsagerun Neja Delta.

 

A ba su idan zai zama mafita – Ramat Muhammad Gaddafi Bolori

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya a nawa ra’ayin idan har an basu kudin zasu daina yin wannan ta’addanci, gara a basu, domin idan ka duba irin halin da alumma suke ciki a kasar nan, yana daya daga cikin dalilan da yasa wasu suka faba cikn wannan hali. Ba wai hakan da suke yi abu ne mai kyau, ba amma bada kudin zai kawo mashala gara a basu, su daina abun da suke yi, domin yanzu inda zaka yi tafiya kana cikin tashin hankali, bawai kai kanka ba, hatta iyalanka da sauran ‘yan uwa ma haka.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya