Da Dumi Dumi

Shin ya kamata Majalisar Dattawa ta kashe Naira biliyan 5.5 domin sayo motocin hawa?

Ya kamata a saya musu –Shehu Abbas Katsina
Ya kamata a saya musu –Shehu Abbas Katsina

Majalisar Dattawa ta amince da kashe Naira biliyan biyar da rabi don saya wa mambobinta motocin hawa samfurin SUB da kowacce ta kai kusan Naira miliyan 46. Duk da dokar kasa ta ba su damar yin haka, amma wadansu mutane na ganin yin hakan nuna rashin jin tausayin talakawan kasar nan ne. Wakilanmu sun jiyo mana ra’ayoyin jama’a kamar haka:

Ya dace a saya musu idan… Malam Bukar Kachalla

Daga Tijjani Usman Bello, Maiduguri

Eh, ya dace a saya musu idan har za su yi mana wakilci mai kyau domin ba mu san irin wahalhalun da za su sha kafin su aiwatar da aikin da muka zabe su dominsa ba. Duk da cewa barnar dukiyar kasa ce kawai, to amma yana da kyau mutum ya karrama wakilinsa a ko’ina ne, sannan wadannan wakilan namu su ne za su mika bukatunmu ga gwamnati har a kai ga biyan bukata. Zai iya kasancewa a ce a cikin ’yan majalisar akwai masu tausayi da sanin ya kamata na cewa tunda gwamnati ta yi mana, dole ne sai ta yi wa mutanenta da ake wakilta a bangare kaza. To ka ga a sanadin gwamnati ta yi masa sai ya ji dadin mika bukatun mutanen yankinsa kuma a yi musu,wannan shi ne dalilin da ya sa na goyi bayan saya musu motocin.

Gaskiya bai dace ba –Abubakar Babangida

ADVERTISEMENT

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Ni a nawa ra’ayin bai dace ba, domin kashe irin wannan makudan kudade don sayo wa ’yan Majalisar Dattawa motocin hawa sam bai kamata ba, lura da halin da al’ummar kasar nan suke ciki. Don haka ina ganin gara a yi wa jama’ar da suka zabi sanatocin ayyukan raya kasa maimakon sayo motocin hawa da kusan kowace kudinta ya kai Naira miliyan 46. Gaskiya duk da dokar kasa ta ba su damar yin haka, amma su tausaya wa talaka su hakura da wadanda suke da su, a yi wa talakawa aiki.

Yin hakan ba daidai ba ne – Sadiya Ibrahim Umar

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

Sayen motocin tamkar almubazaranci ne lura da yanayin rayuwa da talakawa suke ciki. Maimakon a kashe biliyan biyar da miliyan 500 wajen saya wa sanatoci motocin hawa kamata ya yi majalisar ta tsananta tsaro a kasar nan ta sauke farashin kayan abinci ta sauke farashin man fetur saboda a samu saukin rayuwa.

Amma wannan abin mamaki kamar su ’yan siyasar kasar nan ba su damu da halin da talakawa suke ciki ba, burinsu shi ne motoci masu tsada, sun manta cewa suna da talakawan da suke wakilta kuma mu ne muka zabe su ana biyansu da dukiyarmu.

Bai Kamata ba – Malam Manu Muhammad

Daga Tijjani Usman Bello, Maiduguri

Wannan ba wani abin da talaka zai goyi baya ba ne, domin talakawa da dama suna kwana da yunwa ba inda za su samu abinci, sai ga shi an ware makudan kudi don a saya musu motoci. Mutanen da talakan shi ne ya zabe su don su wakilce shi, maimakon haka ba gara a yi wa talaka aiki ba, a samar da ababen more rayuwa da kudaden da za a saya masu motocin. Gaskiyar magana talaka yana cikin wani mummunan yanayin rayuwa, to ina motocinsu da suke da su, idan kuma aka ce a’a na aiki ne to ai an saya wa wadansu wakilan a baya me ya sa da za su tafi, ba za su bari ba tunda na ofishi ne. Wannan ba karamar cutar talaka ake yi a kasar nan ba, ni dai ban goyi baya ba.

Ya kamata a saya musu –Shehu Abbas Katsina

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya ya kamata a saya musu wadannan motoci, domin su ne ’yan majalisar da suke tsara doka don ci gaban kasa, don haka akwai bukatar a ba su duk wata kula da ta kamata. Kuma a matsayinsu na ’yan Majalisar Dattawa ba su duk wata kula ta dace, domin a siyasa idan babu majalisa babu dimokuraddiya, kuma mu dimokuraddiyar nan mun riga mun fara ta. Don haka ya kamata a tabbatar an saya musu duk wani abu da zai kare mutuncinsu. Don Haka ina goyon bayan sayen wadannan motoci da Majalisar Dattawa za ta yi.

Bai kamata a saya ba – Sadauki Ibrahim Dutse

Daga Umar Akailu Majeri, Dutse

Kashe Naira biliyan biyar da rabi a saya wa ’yan Majalisar Dokokin Najeriya motocin hawa bai dace ba. Duk da dokar kasa ta amince da haka amma ya saba wa hankali.

A gaskiya yin hakan bai kamata ba duk wanda yake da bukatar abin hawa ya saya da kudinsa

Me ya sa komai sai dai gwamnati ta yi musu a saya masu motoci, amma ba sa kare hakkin talakawan da suke wakilta, ba sa taimaka wa Shugaban Kasa wajen ganin an yi wa talakawa abin da za su amfana sai dai kullum burinsu su gina kansu?

Share