✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin yana da alfanu ’yan takara su yi muhawara kafin zabe?

Salon yakin neman zabe ya zo da wasu sauye-sauye, inda abubuwan da a da ba a cika damuwa da su ba, bana aka yi ta…

Salon yakin neman zabe ya zo da wasu sauye-sauye, inda abubuwan da a da ba a cika damuwa da su ba, bana aka yi ta tafka muhawara a kansu. Daya daga ciki shi ne yadda aka yi ta muhawara kan yadda manyan ’yan takarar Shugaban Kasa ba su yi muhawara a tsakaninsu ba a bana. Domin haka ne wakilan Aminiya suka zagaya domin jin ra’ayoyin mutane a kan alfanun yin muhawara a tsakanin ’yan takara kuma ga abin da suke cewa:

 

Ya dace kwarai da gaske – Alhaji Danjuma Yakubu

Kabir Yayo Ali, Ibadan

Alhaji Danjuma Yakubu: “Ya dace kwarai da gaske a rika yin muhawara a tsakanin ’yan takara kafin zabe kamar yadda al’ummar Najeriya suka so a yi tsakanin ’yan takara biyu masu neman zama Shugaban Kasa wanda hakan bai yiwu ba. Hujjar da zan bayar a kan hakan ita ce, daga tambayoyin da aka yi wa ’yan takara da amsar da suka bayar ne jama’a za su iya gane wanda ya san irin ayyukan da suke bukata a mazabarsu da irin alkawarin da zai yi musu. A nan ne jama’a za su fahimci ainihin mai alamar kwatanta gaskiya a tsakaninsu da ya fara karantawa a gaban jama’a wanda tun a wannan wuri ne za su fara nuna masa goyon baya su yi watsi da wanda bai san bukatunsu ba. Ni ban ga wata illa ga shirya irin wannan muhawara ba.”

 

Ba ta da amfani – Rukayya Musa

Daga Amina Abdullahi, Yola

Rukayya Musa: “Ba na ganin ya kamata ’yan siyasa su sanya kansu wajen yin muhawara. Dalilina shi ne, wannan muhawara ba ta da amfani illa haddasa tashin hankali a tsakanin mabiyansu. Domin mafi yawancinsu raddi suke wa ’yan adawa. Ga matasa shaye-shaye ya yi yawa hakan sai ya haddasa tashin hankali a tsakanin ’ya’yan talakawa domin sai sun gama muhawararsu sai su koma su shirya da juna kuma a bar talaka da wahala. Uwa-uba ma ba wani maki ba ne da za a bayar ba, wanda za iya kara wa kuri’ar mutum. To ina dalili?”

 

Bata lokaci ne – Jamila Musa Abubakar

Daga Amina Abdullahi, Yola

Jamila Musa Abubakar: “A ra’ayina bai kamata ’yan siyasa su rika yin muhawara a tsakaninsu ba. Dalilina shi ne, wannan duk bata wa juna lokaci ne. Idan an yi muhawara dan siyasa ya fadi zaben bayan muhawarar ya ji kunya. Duk wannan bai dace ba. Domin duk wanda aka ga yana shugabantar al’umma, ya san me yake yi har ya kai ga wannan matsayi. Koda mutum yana son zama shugaba ne wanda ba ya adalci ai ya fi kowa sanin kansa a kan ba ya adalcin kuma ya san yana abin da bai dace ba wajen take sani. Shi ya sa nake ganin babu amfani. Domin duk wanda ka ga ya tsaya takara, ya san wadanne irin ayyuka da yake yi wadanda suka sanya ya yi sha’awar tsayawa takara.”

 

Tana da amfani kwarai da gaske – Ibrahim Sule Zabi

Daga Jamilu Adamu

Ibrahim Sule Zabi: “Muhawarar tana da amfani kwarai da gaske. Dalilina  shi ne idan ka dubi kasashen da suka ci gaba, za ka ga suna ba muhawara muhimmanci sosai, ta hanyar muhawara za ka iya gane wanda zai samu nasara kafin zaben. Muhawara na sa dan takara ya bayyana kudirorinsa idan ya samu nasara. Ta sanadin muhawara masu kada kuri’a ke sanin wanda ya kamata su zaba, sakamakon bayyana kudirorinsa. Ina ba ’yan takararmu shawara su rika bayyana wa mabiyansu kudirorinsu ta hanyar muhawara domin masu kada kuri’a, su san wadanda za su zaba.”

 

Amfanin muhawarar na da yawa – Yakubu Masoyi

Kabir Yayo Ali, Ibadan

Yakubu Masoyi: “Amfanin yin muhawara tsakanin ’yan takarar mukaman siyasa kafin ranar zabe yana da yawa. Sai dai irin yadda ’yan siyasa a Najeriya suke gudanar da al’amuransu yana iya janyo tarnaki a wasu wurare. Daya daga cikin amfanin muhawarar shi ne, zai zama manuniya ga irin alkawarin da suka yi ga mutane. Tun a wajen muhawarar mutane za su iya fahimtar gaskiyar za su iya cika musu wadannan alkawurra ko a’a. Amma kuma illar yin haka zai iya haifar da gabar siyasa tsakaninsu da za su rika yi wa juna yarfe. Gaskiyar ra’ayina shi ne amfaninsa ya fi illarsa yawa.”

 

Ban ga amfanin yin muhawara ba – Nuraddeen Muhammad Bala

Daga Jamilu Adamu

Nuraddeen Muhammad Bala: “Muhawarar ba ta da wani amfani sakamakon har yanzu ba mu samu ci gaban da muhawara za ta yi tasiri a kasar nan ba, hasalim a muhawarar hanya ce ta yaudara a wannan kasa. Sai mun samu ci gaba ta hanyar ilimi, wutar lantarki, hanyoyi da sauransu kafin muhawara ta yi tasiri a wannan kasa. Sau da yawa za ka ga mutun mai surutu amma mayaudari ne sannan za ka iya samun mutum mara surutu amma ka same shi da rikon amana. A karshe ina son in tabbatar muku da cewa surutu ba shi ne shugabanci ba, rikon amana da aiki shi ne shugabanci.”