✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shin yaya kuke ganin jinkirin nada kwamishinoni a jihohi?

Bayan da aka rantsar da gwamnonin jihohin kasar nan a ranar 29 ga Mayun bana, har zuwa yau kusan wata uku akasarin gwamnonin jihohin ba…

Bayan da aka rantsar da gwamnonin jihohin kasar nan a ranar 29 ga Mayun bana, har zuwa yau kusan wata uku akasarin gwamnonin jihohin ba su nada kwamishinoni ba, in ban da ’yan kalilan. Hakan a cewar jama’a na iya kawo koma-baya ga ci gaban wadannan jihohi. Wadansu kuma na ganin gwamnonin na yin haka ne, domin wata bukata tasu. Wakilanmu sun jiyo ta bakin wadansu mutane a kan wannan jinkiri kuma ga abin da suke cewa:

 

Koma baya ne– Ali Mu’azu Garu Dutse

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

Matsalar kin nada kwamashinoni koma-baya ne Kuma tamkar tauye ci gaban jihohi ne. Saboda in ba a nada kwamashinoni ba, ba zai yiwu gwamnonin su aiwatar da ayyukan raya kasa ba. Kamar mu a nan Jigawa muna kira da Gwamna Badaru Abubakar ya yi kokari ya nada kwamashinoni saboda lokaci yana kurewa. Ba za mu gaji da bai wa Gwamna shawara ba don bayar da tamu gudunmawar ta hanyar da ta dace. Amma dai nada kwamishinonin nan shi ne mafita ga ci gaban jihohi.

 

Akwai kuskure rashin yin haka – Garba Salisu

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya akwai kuskure, ya kamata a ce sun nada, domin hakan ne zai taimaka wa su gwamnonin tunda dole kwamishinonin su ne masu ba su shawarwari a kan akasarin ayyukan da ya jibanci ci gaban kasa.

Kuma babu yadda za a yi Gwamna shi kadai a ce shi ne zai rika tafiyar da komai a jiharsa ba tare da taimakon kwamishinoni ko masu ba shi shawara ba. Ni dai a nawa ra’ayin ya kamata duk jihohin da ba su nada kwamishinonin ba su hamzarta yin hakan domin ci gaban al’umma.

 

Salon mulkin Buhari ne suke kwaikwayo – Abubakar Abdullahi Jikan Liman

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

A fahimtata mafi yawansu suna jan kafa ce domin su sababbin gwamnoni ne suna son sai sun natsu su zakulo wadanda aka yi wahala da su kuma wadanda ba su yi wa tafiyarsu tafiyar hawainiya ya zama a gaba za su munafunce su, gudun kada su shigo da munafukansu yana iya sa su wannan jan kafar. Akwai maganar tattalin arziki sun samu jihohinsu da dimbin bashi na wadanda suka gada. Kwamishinoni na cin kudi su ma, ganin halin da ake ciki ya sanya su dan saurara. Salon mulkin Buhari ne suke kwaikwayo wadansu daga cikinsu, don ko a yanzu da bai samu matsin lamba ba da ba zai yi ministocin ba ganin yadda yake jan kafa a wurin nada ministocin ne suke kwaikwayonsa, duk da mu ’yan kasa ba mu san alfanun yin haka ba.

 

Ba daidai ba ne– Usman Sani Tela Wudil

Daga Muhammad Aminu Ahmad

Gaskiya ni ra’ayina gwamnonin da ba su nada kwamishinoni ba,wannan ba daidai ba ne. Saboda rashin nadawar da wuri zai kawo koma-baya ta kowane fanni, ya kamata kowane Gwamna a ce ya nada kwamishinoninsa a kan lokaci domin su ne za su ba shi gudunmawa wajen kula da wasu al’amura musamman a ma’aikatun gwamnati. Don haka rashin nada kwamishinonin ba alheri ba ne ga ci gaban jiha, don za ka ga yanzu-yanzu shekara hudu za su yi.

 

Suna yi ne don kwadayi cin albashin kwamishinonin– Sirajo Ibrahim

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Gwamnoni suna wannan tafiyar ce ta kin yin kwamishinoni da wuri  domin son cin kudin kwamishinoni, suna yi ne don kwadayin albashin kwamishinoni kafin a rantsar da su, su rika amfana da kudinsu wanda idan akwai su dole a ba su abinsu ba halin cinyewa. Kuma cinkoson ’yan siyasa a jam’iyyar da ta samu nasara ma yana hana yin kwamishinoni domin kowane mutum yana son a zabe shi ko ya bayar da wanda za a nada hakan na kawo tsaikon nada kwamishinonin.

 

Rashin nada kwamashinoni matsalace babba – Obinna

Daga Umar Akilu Majeri, Dutse

Rashin nada kwamashinoni da gwamnonin wasu jihohi suka yi a jihohinsu ba karamar cikas ba ce. Kuma hakan na iya sa wa a samu koma-baya wajen gudanar da ayyukan raya kasa.

Wadansu gwamnonin sun ki nada kwamashinoni ne saboda son ransu suna tunanin za su yi amfani da kudaden da za su ba su wajen azurta kansu ko kuma su yi wasu muhimman ayyukan raya kasa da kudin maimakon kashe wa kwamashinoni.