✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shinkafar gida ta cika kasuwannin Jihar Katsina

Sama da mako biyu ke nan da shinkafar gida ta mamaye wasu kasuwannin Jihar Katsina a dalilin nomata da yawa da manoma suka yi, inda…

Sama da mako biyu ke nan da shinkafar gida ta mamaye wasu kasuwannin Jihar Katsina a dalilin nomata da yawa da manoma suka yi, inda hakan ya janyo saukar farashi da kuma karancin masu sayenta. In za a tuna an samu faduwar farashin masara a daminar bara tare da hauhawar farashin takin zamani, hakan ya sa mafiya yawan manoman suka mayar da hankali wajen noman shinkafa a bana.

Wani babban manomi mai suna Alhaji Usman ya ce, manoman shinkafar sun tashi haikan wajen habaka nomanta don ta yawaita a dalilin samun wadataccen ruwan sama a bana. “Yawan shinkafar da aka noma a bana a Jihar Katsina ya fi na bara. Tun daga Karamar Hukumar Danmusa zuwa Karamar Hukumar Sabuwa gonakin shinkafa ne za ka yi ta gani. Kuma Allah cikin rahamarSa Ya albarkace mu da samun ruwan sama a bana. Saboda haka, yawaitar nomanta ne ya sa kake ganin abin da ka gani a kasuwar, wannan somin tabi ne kawai a cikin jihar,” inji shi.

Alhaji Usman ya kara da cewa, “Faduwar farashin shinkafa a bana, ba wani abu ne da za a kawo damuwa a kansa ba, saboda babu wata matsalar da ta haifar wa manomanta samun kudaden shigarsu. Sannan in aka lura tun daga bara farashin kayan amfanin gona suka fara yin kasa saboda yawaitarsu a kasuwa.”

Shi kuwa Malam Muhammadu Ashiru, daya daga cikin masu dillancin shinkafa a Kasuwar Dandume cewa ya yi, “A yanzu babu masaya shinkafar a kasuwa saboda yanzu ne take cikin danyantakarta, su kuma kamfanonin sun fi bukatar wadda ta bushe. Kadan daga cikin masayan da suka fito daga Jihar Sakkwato da masu amfanin yau da kullum ne ke sayenta a yanzu. Su kuma kamfanonin da ke gyaranta sai ta bushe nan gaba za su fara saye.” Ashiru ya ci gaba da cewa, akwai dan bambancin farashi a yanzu in aka kwatanta da bara, saboda yawaita nomanta da ake yi. Ya ce, bara kamar yanzu ana sayar da buhun shinkafar da ba a casa ba a kan Naira dubu takwas zuwa 10. Amma yanzu farashin ya dawo daga Naira dubu biyar zuwa takwas. Akwai ma launin da ake kira ‘Jar Naira’ ana sayar da ita a kan Naira dubu takwas da dubu shida. Sauran kuwa ba su wuce Naira dubu biyar. Amma duk da haka, farashin bai cutar da manoman ba saboda yadda suka kara nomanta.

Yahuza Muhammad, wani manomin daga Karamar Hukumar Dandume ya ce, an fara girbin shinkafar da wuri jim kadan bayan Babbar Sallah, kuma hakan ya faru ne saboda an noma ta da yawa. Kuma za a dauki lokaci ana girbinta kafin ta kare saboda akwai ta iri-iri. “A lokacin da muke girbin wannan, a can kuma ana kokarin shuka wata, haka abin yake tafiya har zuwa farkon watan Oktoba, domin za a rika girbinta ne daki-daki,” inji shi.

Ya ce, yanzu hankulan manoma sun fi kwanciya wajen noman shinkafa fiye da na masara, saboda ta fi kawo yabanya da kuma riba. Shi ma Shu’aibu Sani Kadawa daga Dandume ya ce, manoman na fara girbin tun kwana biyu kafin ranar kasuwa. Ya ce, “Saboda tana danya a yanzu ya sa ba za mu iya ajiye ta ba, dole mu kai kasuwa. Wadda za a iya ajiyewa ita ce wadda ake girbi a tsakanin watan Satumba da Oktoba.” Ya ce duk wata hidimar aiki da za a yi da ta hada da girbi da bakace da sauransu, manomi na kashe akalla Naira 900 a kan kowane buhu mai nauyin kilo 100.