Da Dumi Dumi

Shirin ‘Anchor Borrowers’ ya yi tasiri ga manoma a Jihar Kebbi

A shekarar 2015 ne Gwamnatin Tarayya ta fito da shirin tallafa wa manoman shinkafa da alkama da kuma waken soya ta yadda aka kudurta za a samar da shinkafa da za ta iya ciyar da al’ummar Najeriya da zai samar da ton miliyan biyu ga al’ummar kasar nan, a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu. Ana tsammanin a shekara 2016, 2018, Jihar Kebbi ta samar da Shinkafa da ta zarce ton Miliyan biyar.

A ranar 17 ga Watan Nuwamba na 2015 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tattaki zuwa garin Zauro a karamar hukumar Birnin-Kebbi a Jihar Kebbi, domin kaddamar da shirin noman Shinkafa da Alkama da kuma Waken Suya na rani da damina a garin Zauro a Jihar Kebbi.

Shirin da Shugaban ya kaddamar wancan lokacin, shiri ne na musamman tare da hadin gwuiwar Babban Bankin Najeriya a shirin wanda ake kira (ANCHOR BORROWERS) domin bayar da tallafin noma da kuma rage zaman kashe wando ga marasa aikin yi kasar nan.

Gwamnatin tarayya ta fito da wannan shirin ne domin ta farfado da arzikin dake cikin noma a kasar nan, musamman bisa la’akari da tabarbarewar arzikin kasa tare da gujewa dogaro da arzikin man fetur.

Ganin irin amfani da cigaban da aka samu akan noman Shinkafa, Alkama, da kuma Waken Suya a Jihar Kebbi, Shugaban Buhari ya baiwa Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, matsayin Shugaban kwamitin gudanar da sha’anin noman Shinkafa da Alkama a Najeriya.

ADVERTISEMENT

Saboda haka gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancin Abubakar Atiku Bagudu ta ga cewa ya zama wajibi ta fito da wannan tsarin noma domin maido da arzikin noma a Jihohin Najeriya. Daga nan kuma ta bukaci Babban Bankin Nijeriya, CBN, da cewar ya shigo cikin wannan shirin kamar yadda Shugaban Kasa ya bada umurni tun daga farko, don bayar da tasu gudunmuwa ta hanyar bayar da tallafin kudi da kayan noman ga manoman Jihar Kebbi.

Kwamitin da Shugaban Kasar ya nada akan sha’anin noman Shinkafa da Alkama a karkashin gwamnan tun a wancan lokaci kwamishinansa ya ziyarci Jihohin dake noman Shinkafa da Alkama domin ganin irin yadda za su iya bayar da tallafi ga jihohin don kara bunkasa aikin noma a Najeriya. Hasali ma ya fito fili ya bayyana cewar “Burina shine na ga ana sayar da Shinkafar Kebbi a gidajen cin abinci a New York da Japan.’’

Ganin irin kokarin gwamnatin jihar ke yi wurin ganin cewa arzikin noma ya bunkasa a jihar ta Kebbi da ma kasa baki daya, wasu gidajen Jaridun kasar nan suka ga ya dace su karrama shi da lambar yabo wanda shi ne dalilin da yasa Jaridar Banguard da Leadership suka bashi lambar yabo a matsayin gwamnan da ya fi jajircewa wajen bunkasa noma a kasar nan. Bugu da kari kuma kamfanin Jaridun Media Trust, wanda ke buga Jaridar Daily Trust da Aminiya, ya shirya nuna amfanin gona na hadin gwuiwa da ma’aikatar aikin gona ta Jihar Kebbi, inda kamfanoni da dama suka sami halartar gaggarumin nuna amfanin gonan wanda akayi a wancan lokacin a Kebbi.

Yaci gaba da cewa mu dai manoma a Jihar Kebbi mun cigaba domin a shekarun baya idan kayi noma sai ka rasa wanda zai zo ya saya. Amma yanzu don ka noma Shinkafar Naira Milian 100, Kamfanin Labana zai saye ta nan take cikin sa’o’i hudu kudi sun shiga hannun ka.

Daya daga cikin cigaban da harkar noma ta samu a Jihar Kebbi shine hadin  gwuiwa tsakanin Jihar Kebbi da ta Legas inda gwamnan Jihar Kebbin ya yanke shawarar jawo daya daga cikin jihohin kasar an don yin shiri na musamman kan hada  kai domin kulla huldar kasuwanci akan amfanin gona. Daga bisani jihohin biyu suka amince da yin kawancen noman Shinkafa ta yadda a ranar 23 ga Maris, 2016. Gwamnan na Jihar Kebbi da Gwamnan Legas Ambode suka rattaba hannu akan yarjejeniyar.

Wannan yarjejeniyar wata fitila ce aka haska ga sauran Jihohin Nijeriya akan maida hankalin su wajen kasuwanci kan amfanin gona da ake nomawa a cikin kasar nan tare kuma da samar da ayyukan yi ga maras aikin yi, a kuma rage zaman kashe wando ga wasu matasan kasar nan.

Harwayau kawancen wata hanyace aka fito da ita don karawa kasuwanci kwarin gwuiwa da kuma kara samar da hanyoyin walwala da jin dadin al’ummar Jihohin biyu da kuma farfado da arzikin kasa ta hanyar noma abincin da zai wadatar da mutanen kasar nan baki daya. Wannan hadin gwuiwar tsakanin Jihar Legas ta samar da Shinkafa a babban kasuwar nan ta Legas da ake cewa (LAKE RICE).

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya taba kaddamar da wani gagarumin aiki a Jihar Kebbi. Aikin da aka kaddamar kuwa shi ne na bude kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a yankin Afrika ta yamma, a karamar hukumar Argungu dake Jihar Kebbi mai suna “WACOT RICE MILLS.” A jawabinsa na kaddamar a kamfanin mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace noma da ma’adanai za su kasance daya daga cikin abin da Gwamnatin tarayya za ta baiwa fifiko har ta gama tsawon nata mulki domin noma da ma’adanai babu abin da ya fi su ta fuskar samun tattalin arziki.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya