✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin APPEALS zai tallafa wa manoma dubu 10 a Jihar Kaduna

Shugaban shirin nan na hadin gwiwa a tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da Bankin Duniya kan tallafa wa manoma, mai  suna APPEALS  na Jihar…

Shugaban shirin nan na hadin gwiwa a tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da Bankin Duniya kan tallafa wa manoma, mai  suna APPEALS  na Jihar Kaduna, Dokta Yahaya Aminu ya ce, shirin zai tallafa wa  matasa da mata manoman masara da citta da  kiwon shanu su dubu 10 da kudade a Jihar, domin su sayi kayayyakin sarrafa amfanin gonar da suke nomawa. Dokta Yahaya Aminu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga kungiyoyin manoma a garin Saminaka.

Ya ce, an kirkiro shirin ne, domin inganta harkokin aikin noma da kiwo, don samar da madara da sarrafa kayayyakin amfanin gona. Saboda matsalolin da manoma suke fuskanta wajen kasa sarrafa kayayyakin amfanin gonar da suka noma, har su kai ga lalacewa.

Dokta Yahaya Aminu, wanda jami’in sashin noman citta da masara da kiwon shanu na shirin, Dokta Adamu Yakubu ya wakilta, ya ce, shirin yana son a tanadi tsarin da manoma za su noma kayayyakin amfanin gona, sannan  su sarrafa su.  Kuma shirin yana son ya tanadar wa matasa da mata ayyukan yi, saboda guje wa zaman banza.

Dokta Yahaya, ya ce, a wannan shiri a Jihar Kaduna an zabi noman masara da citta da kiwon shanu don samar da madara da za a  bayar da wannan tallafi. Ya ce za a yi amfani da kungiyoyin manoma ne wajen gudanar da shirin.

Ya ce, za a bai wa manoman tallafin ne ta hanyar asusun ajiyarsu a bankuna. Kuma shirin zai tallafa wa matasa  da mata wajen samar musu da ayyukan yi a Jihar Kaduna.

“Mun fito ne domin mu wayar wa jama’a  kai kan wannan shiri. Domin jama’a su samu damar cin gajiyar shirin, saboda dukkan tallafin da za a bayar kyauta ne,” inji shi.