✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin NECAS ba shi muka ba manoma ba kyauta ba – Gado-Da-Masun Dukku

Shugaban Kungiyar Bada Rancen Noma na Shiyyar Arewa Maso Gabas, (North East Commodity Association Society – NECAS), Alhaji Ahmed Muhammad Dukku, Gado-Da-Masun Dukku ya ce…

Shugaban Kungiyar Bada Rancen Noma na Shiyyar Arewa Maso Gabas, (North East Commodity Association Society – NECAS), Alhaji Ahmed Muhammad Dukku, Gado-Da-Masun Dukku ya ce manoman da suka samu rancen noma su sani bashi ne aka ba su ba kyauta ba.

Alhaji Ahmed Muhammad Dukku, wanda har ila yau shi ne Sakataren Kungiyar NECAS ta Kasa ya ce bayan NECAS ta bai wa manomi bashi idan ya noma kuma ita za ta saya a farashi mai kyau ko da darajar amfanin ya karye a kasuwa.

Ya ce bayan sun bada bashin akwai manoman da ruwa ya share musu gonaki baki daya wadannan Kamfanin Inshora ya biya musu bashin.

“Kamar yadda wadansu suke ganin kyauta ne wadannan kayayyakin noma da idan aka ba su har suke sayarwa suna fantamawarsu, to su kwana da sanin bashi ne kuma za su biya, amma wajen biyan na farko kashi 40 cikin 100 za su biya na biyu da na uku nan kuma za su biya kashi 30 sau biyu; amma sai wadansu suke ganin kyauta ne suke holewar su da shi,” inji shi.

A cewarsa kudin da suke bayarwar yana fitowa ne daga Babban Bankin Najeriya (CBN), ya bi ta Bankin Manoma, sa’annan ya shigo hannun Kungiyar NECAS su kuma su bai wa manoma. Hakan ne ya sa Bankin CBN da jami’an tsaro suke kula don tabbatar da komai ya tafi daidai.

Sakataren na NECAS ya nuna fushinsa kan yadda wadanda suka yi rajista da sunan manoma alhali ba manoma ba ne suke sayar da kayayyakin da aka ba su ga ’yan kasuwa a araha bayan kuma za su biya daga baya.

Ya kara da cewa sun bullo da wani tsari da nan gaba za su tabbatar da manoman asali masu gonaki ba manoman bogi ba ne za su amfana da shirin.

Ya ce sun samu masana harkar kwamfuta da za su je gonaki da na’urori don yi wa manoma rajista. Ya ce kwamfutar ba za ta bar wadanda ba su da gona su yi amfani da gonakin wadansu da aka yi wa rajista don a yi musu ba, na’urar ba za ta yarda da rajista sau biyu ba.

Alhaji Ahmed Dukku, ya koka kan yadda mutanen Karamar Hukumar Gombe suke wahalar da su fiye da  sauran kananan hukumomin jihar wajen ba da kayayyakin. Ya ce don ganin Shiyyar Arewa maso Gabas ta amfana da shirin noman a makon jiya sun raba taraktocin huda 50 cikin 150 da suka kawo jihar.

Daga nan sai ya ce tunda shirin na Gwamnatin Tarayya ce da suke kula da shi; in Allah Ya yarda yadda shirin ya karbu ko bayan gama mukin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, shirin zai dore.