Da Dumi Dumi

Shirin samar da masu tsaron sa-kai na al’umma

Kusan tun  kafin  a fara mulkin wannan jamhuriyya a 1999, aka shiga muhawara kan cancanta da rashin cancantar samar da ’yan sandan jihohi a kasar nan da niyyar shawo kan tabarbarewar tsaro irin na yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sace-sacen shanu da rikicin Fulani makiyaya da manoma da fadace-fadace masu kama da addini da kabilanci da fasa bututun man fetur da fashi da makami da sauran miyagun laifuffuka da suka game kasar nan, ta yadda kowace jiha ko shiyya a yau, tana da nata matsalar ko matsalolin na tabarbarewar tsaro.

Wata ko wasu matsalolin sun kebanta ne da wasu jihohi ko shiyoyyi ne, amma yanzu sun game kasa, kamar fadan Fulani makiyaya da manoma ko yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da muka dade da shi a kasar nan.

Da muhawarar ta kasaita an samu rarrabuwar kawuna kai-tsaye a tsakanin gwamnonin jihohin Kudancin kasar nan, lokacin da dukkan gwamnonin Kudu suka nuna amincewarsu ta a kirkiro ’yan sandan jihohin, yayin da gwamnonin jihohin Arewa (in ban da Gwamnan Jihar Filato na wancan lokacin Mista Jonah Jang), suka ja daga a kan ba sa bukata.

Hanzarin da kowannensu ke bayarwa a wancan lokacin ya sha bamban. Yayin da na Kudu ke cewa samar da ’yan sandan jihohin zai taimaka wajen samun ingantuwar tsaro a jihohinsu, saboda wadanda za a dauka ’yan asalin jihar ne kuma a yankunansu za su yi aiki.

Su kuwa gwamnonin jihohin Arewa cewa suke duk da ’yan sandan kasar nan da yawansu bai kai dubu 400 ba sun yi kadan, amma samar da ’yan sandan jihohin zai iya haddasa husuma irin ta siyasa da kara kawo tabarbarewar tsaro da ake son ingantuwarsa idan aka yi la’akari da yadda gwamnonin jihohi kan yi amfani da ’yan sandan wajen biyan bukatarsu a kan abokan hamayya, ko a tsakanin ’yan sandan jihohin da na kasa baki daya.

ADVERTISEMENT

Yanzu maganar da ake kai, ita ce, bakin gwamnonin jihohin kasar nan 36 ya hadu a kan lallai a samar da ’yan sandan al’umma (da za su rika kula da tsaro a yankunansu na asali, ba lallai da sunan ’yan sandan jiha ba).

A kwanakin baya an ji Gwamnan Jihar Ekiti kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin kasar nan, bayan wata ganawa da ya yi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar Shugaban Kasar, yana fada wa manema labarai cewa  akwai shirin da gwamnonin suke kai na yin amfani da matasa a shirin samar da ayyukan yi ga matasan kasar nan (N-Power,) kimanin dubu 500  a zaman ’yan sa-kai don a samar da tsaro.

Shi ma Babban Mataimaki Na-Musamman ga Shugaban Kasa a kan kirkiro da samar da ayyukan yi ga matasa Mista Afolabi Imoukuede, an ji shi yana fada wa wani taron manema labarai a Abuja cewa tuni sun samar da bayanai ga gwamnonin jihohi da Sufeto Janar na ’Yan sanda Alhaji Mohammed Adamu a kan matasa dubu 500 da za a dauka a matsayin ’yan sa-kai da za su yi aikin samar da tsaron a yakunansu.

Mista Afolabi, ya ce an raba matasan gida biyu, ya ci gaba da cewa “Mun san irin kalubalen tsaron da muke ciki. Muna kuma sane da irin kalubalen da ’yan sanda suke ciki, da irin abin da za su iya yi. Mun san suna son su dauki karin ’yan sanda dubu 10 amma gwamnoni a matsayinsu na shugabannin tsaro a jihohin sun sun san cewa karin ’yan sanda dubu 10, a fadin kasar nan ya yi kadan kuma nawa za a ba kowace jiha?”

Kodayake Gwamnan Ekiti da shi kansa Mista Afolabi ba su tsayar da takamaimiyar rana ba da shirin na matasa ’yan sa-kai a kan tsaro a dukkan kananan hukumomin kasar nan 774, da ake da su ba, amma sun tabbatar akwai matasan da za su ci gajiyar shirin da kuma kudaden da za a rika biyansu alawus na wata-wata da ya kai Naira dubu 30, wanda yanzu shi ne mafi karancin albashi.

Ko shakka babu, gaggauta samar da shirin na matasa masu tsaro ’yan sa-kai yana da matukar fa’ida ga jama’ar kasar nan idan aka yi la’akari da irin sukurkucewar tsaro da ake fama da shi a wannan lokaci, kamar yadda na fada a sama, cewa kowane bangare na jiha ko na kasar nan yana da irin wanda yake fuskanta, a birni da karkara.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ya kamata Sufeto Janar na ’Yan sanda a ce da su za a tantance tare da bayar da horo ga matasa ’yan sa-kan.   Su sanya tsoron Allah da kishin kasa wajen tantancewar.

Ba don komai na yi wannan kira ba, sai don sanin da na yi cewa akasarin wadanda ake zargi da aikata kowane irin ta’addancin da kasar nan take fuskanta a yau matasa ne. Ko dai za ka tarar suna cikin kungiyoyin asiri na matsafa (musamman matasan Kudu), ko kuma mu nan Arewa da muke fama da matasa masu aikata daba da Sara-Suka da Kalare da Kauraye da sauran sunaye da ake kiransu daga jiha zuwa jiha, baya ga masu aikata sababbin ayyukan ta’addanci da ake fama da su yanzu. Hakazalika akwai bukatar a sa matasan ’yan sa-kan a karkashin kular rundunonin ’yan sanda na jihohi, ta yadda aikin tsaro zai zama a karkashin kulawar hukuma daya, don kwalliya ta rika biyan kudin sabulu, sabanin a yi musu hukumarsu ta daban da hakan zai rika haddasa isa da jiji-da-kai, da rashin samar da bayanan sirri ga hukuma daya balle a ce za a yi aiki tare, kamar dai yadda aka dade ana zargin jami’an tsaron  da kasa yin hakan a junansu, ya sa yaki da yan ta’adda yake gagararsu.

 

Share