✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin sulhu a zamfara: Kwalliya tana biyan kudin sabulu

Shirin sulhu da ’yan bindiga da mahukuntan Jihar Zamfara suke yi a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Alhaji Bello Matawalle abu ne da za a yi…

Shirin sulhu da ’yan bindiga da mahukuntan Jihar Zamfara suke yi a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Alhaji Bello Matawalle abu ne da za a yi sam barka. Domin kuwa jama’ar Jihar Zamfara sun gani a kasa, ta yadda aka samu raguwar hare-haren  ’yan bindiga a sassan jihar, tare da komawar jama’a da dama kauyukansu da zama sakamakon tattaunawar da mahukuntan jihar da jami’an tsaro da kuma shugabannin al’ummomi  suke yi da maharan kai-tsaye. Hakan ya haifar da sake kulla dadaddiyar alaka ta zumunci da makwabtaka da take a tsakanin al’ummar Fulani da Hausawa mazauna yankunan da abin ya shafa.

Yunkurin dinke babbar barakar da ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa a wannan jiha, kwalliya tana biyan kudin sabulu ganin yadda aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya wacce a sakamakonta jami’an tsaro da na ’yan sa-kai suka saki gwamman Fulani maza da mata da suke rike da su tare da tsagaita farautar maharan. Yayin da su kuma a nasu bangaren maharan sun saki da dama daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Abin sha’awa shi ne duk wannan ya samu ne ta hanyar tattaunawa a kan teburi ba da yin karfin bindiga ba. Don haka tilas a yaba wa Gwamnan Jihar  Zamfara Bello Matawalle wanda ya jajijrce ba dare ba rana ya kai gwauro ya kai mari don tabbatar da ya sauke nauyin da ke a kansa. Ta kai sai da ya yi wa idonsa tozali da barkono wajen tumbuke wasu sarakuna daga kan karagarsu saboda zarginsu da ake yi da hannu a cikin wannan mummunan lamari.

Duk da yake an samu wannan kyakkyawan ci gaba na kawo zama lafiya, har yanzu akwai sauran aiki a gaba mahukuntan jihar da kuma su kansu jami’an tsaro na tabbatar da ci gaba da aiwatar da shirin ba tare da an sanya siyasa ko son zuciya a ciki ba. Haka kuma ya zama wajibi mahukunta tare da hadin gwiwar shugabannin al’ummomin  Fulani da Hausawa su sanya ido don ganin dukkan bangarorin sun girmama tare da aiwatar yarjejeniyar da aka cimma ba tare da yin zagon kasa ko sari-ka-noke ba.

Sannan ya kamata a samar da wani kwamiti a kowace shiyya wanda zai rika karbar koke-koke daga kowane bangare don ganin an yi maganin duk wata wuta da ka iya ruruwa tun tana karama ta hanyar tattaunawa da juna. Haka ya zama wajibi gwamnati ta farfado da wasu hanyoyi na inganta rayuwar makiyaya da kuma ilimantar da su. Sannan a tabbatar da hukunta duk wanda aka samu da yi wa wannan shiri na zaman lafiya karan-tsaye da tona asirin masu hannu a ciki ko haddasa shi.

A bangaren jami’an tsaro suna da muhimmin aiki a gabansu musamman na gano masu safarar makamai zuwa wannan yanki tare da karbar makaman da suke hannun jama’a. Kuma su hada gwiwa da tsofaffin maharan wajen ganin sun samu sahihan bayanai game da wadanda suka zabi kangare wa wannan shiri na zama lafiya don a ga bayansu.

Su kuma jama’ a gari da sauran Fulani ya zama wajibi su yafe wa juna tare da mantawa da abin da ya faru a baya don dinke barakar da ta riga ta faru. Haka ya kamata su rungumi tsofaffin ’yan bindigar ba tare da nuna kyama ko bambanci ba. Su ma a nasu bangaren tsofaffin ’yan bindigar ya kamata su yi nadamar abin da suka aikata tare guje wa duk wani abu da zai sanya su koma cikin wancan mummunan hali.

Duk da yake tabbatar da tsaro yana hannun mahukunta da kuma jami’an tsaro, amma a fili yake cewa ba za su iya sauke wannan nauyi da ke a kansu ba in jama’a ba su taimaka musu da sahihan bayanai na sirri da za su taimaka don kau da batagari da kuma yada manufofin gwamnati na kawo dauwamammen zaman lafiya a Jihar Zamfara ba. Muna fata irin wannan yunkuri da wadansu gwamnonin jihohin Arewa suke yi musamman gwamnonin jihohin Katsina da Sakkwato ya samu irin wannan karbuwa da nasara da aka samu a Jihar Zamfara don samun cikakken zama lafiya a wannan yanki namu mai albarka. Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya, amin.

Iro Surajo,  ya aiko wannan rubutu ne daga Abuja

0816343 9197