✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shirin Trader Moni salon sayen kuri’a ne – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya soki tsarin raba kudi ga kananan ’yan kasuwa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi ana kusa da fara…

Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, ya soki tsarin raba kudi ga kananan ’yan kasuwa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi ana kusa da fara zabe, inda ya ce sayen kuri’a ne ba tallafin lamuni ne ga kananan ’yan kasuwa ba.

Yakubu Dogara ya fadi haka ne a lokacin da Kwamitin Hadin-Gwiwa na Majalisar Dokoki kan INEC da Jam’iyyun Siyasa ke tattauna batun sayen kuri’a da kuma yadda za a inganta tsarin zabe a Najeriya.

Dogara ya ce kowace irin kyakkyawar niyya za a yi tunanin kafa tsarin, shirin raba kudin ya koma sayen kuri’a da kuma ribatar jama’a a kan wanda ake so su zaba, kuma rashawa ce karara.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi irin wannan korafin tare da zargi Gwamnatin Tarayya, inda ya ce tana amfani da tsarin Trader Moni a fakaice tana sayen kuri’un mutane ne domin zaben 2019.

Yakubu Dogara ya ce shirin da bai kankama ba sai yanzu da zabe ya karato ya saba wa sashe na 124 (1) a, b, c da kuma sashe na (124) (2), (4), (5) da sashe na 130 na dokar zabe.

Shirin wanda Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar a da dama daga cikin jihohin kasar nan karkashin wani shirin gwamnati na samar da ayyukan yi da agaza wa ’yan kasuwa masu karamin jari, an ware masa wani adadin kudi a kasafin kudin bangaren zartawa na farko bayan hawa madafun iko.

A jawabin, Mai ba Mataimakin Shugaban Kasar Shawara ta Musamman a kan Kafofin Watsa Labarai, Hafiz Ibrahim ya ce an faro shirin na Trader Moni  ne tun kafin karatowar zabe, kuma ya ce babu wata manufa ta tilasta wa wadanda suka amfana da shirin su zabi Shugaba Buhari.

Hafiz Ibrahim ya ce shirin bai damu da sanin ko dan wace jam’iyya ce ya ci gajiyarsa ba, kuma bai damu da bibiyar wacce jam’iyya za su zaba yayin zaben na 2019 ba.

Ya alakanta zarge-zargen na Bukola Saraki da Yakubu Dogara a matsayin farfagandar siyasa don wasa da hankalin al’ummar kasa.