✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Buhari da neman a sake zabarsa

Bisa ga tsarin jadawalin zabubbukan shekara mai zuwa (2019) in Allah Ya kaimu da Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, ta tsara,…

Bisa ga tsarin jadawalin zabubbukan shekara mai zuwa (2019) in Allah Ya kaimu da Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC, ta tsara, ranar Lahadin da ta gabata wato 18 ga wannan watan na Nuwamba ita ce ranar da Hukumar ta INEC ta sahalewa dukkan ’yan takarar neman shugabancin kasa da na Majalisun Dokoki na kasa (Majalisar Dattawa da ta Wakilai) da su fara yakin neman zaben, ma’ana shiga lungu da sakon kasar nan ko aikawa da sakonni ta fannonin kafofin yada labarai ne ko saduwa da jama`a kai tsaye da ma dai dukkan wasu hanyoyin da za su ba su dama wajen baza manufofinsu, ga magoyo baya da sauran ’yan kasa da suka cancanci kada kuri`a don su amince da su har su zabe su. A zaben na shekara mai zuwa da a yau ya rage kwanaki 85, daga cikin jam`iyyun siyasa 91, da za su shige shi, zuwa yanzu 79 daga cikinsu suka tsayar da ’yan takarar neman shugabancin kasa.

Wannan shi ne karon farko da ake samun ’yan takara mafi yawa tun da aka fara wannan janhuriyar a shekarar 1999, ba wai a kan masu neman shugabancin kasa ba, a’a har a kan sauran mikamai irin nasu ’yan Majalisun Dokoki na kasa da na jihohi da ma na gwamnonin jihohi, hakan bai rasa nasaba a kan karin jam`iyyun siyasa na Hukumar ta INEC ta yi wa rijista tsakanin zaben shekarar 2015, zuwa yanzu

Sahalewar Hukumar ta INEC ta sanya, tun a ranar Lahadin da ta gabatan shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC mai mulki, a fadar shugaban da ke Abuja ya jagoranci wasu ayarin Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da wasu Ministoci da shugabannin jam’iyyarsa da wasu gwamnonin jihohi, kai har da mai dakinsa Hajiya A’isha Buhari, wajen kaddamar da gangamin neman sake zabensa mai taken “Mataki na gaba.” Shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar kuma dan takarar neman shugabancin kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, washegari, wato Litinin 19-11-18, a Abuja, ya jagoranci shugabanni da dubun dubatar magoya bayan jam`iyyarsu ta PDP wajen kaddamar da nasa gangamin neman kuri`un, mai taken “Shirin da nake da shi don sake dawo da Najeriya a kan hanya.”

A makalar wannan makon cikin yardar Allah na  mayar da hankali ne a kan kundin shugaba Buhari, in kuma Allah Ya rayar da mu a makon gobe da rai da lafiya, zan dubi na tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar. Da ma dai na kusa da shugaba Buharin sun ba da tabbacin cewa Kundin gangamin neman sake zaben na sa zai mayar da hankali ne a kan irin kalubalen da shugaba Buhari ya tarar a gwamnatinsa da kuma wadanda ya yi alkawarin aiwatarwa da matsayin da suke a yanzu da kuma in da zai dora idan Allah Ya sa ’yan kasa sun sake ba shi amincewarsu, kamar yadda a takaice ya kira kundin wato “Mataki na gaba.”

Tun farko a cikin jawabinsa na kaddamar da Kundin, shugaba Buhari ya roki ’yan siyasar kasar nan da kar su yi amfani da zabubbukan na shekara mai zuwa, a zaman wani abu na a mutu ko a yi rai wajen haddasa rudani da tashin hankali, da ka iya jefa kasar cikin wani mawuyacin hali. Yana mai tunatar da masu kwadayin su mulki kasar nan da cewa ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya. Shugaba Buhari ya fadi cewa shekaru 4, da suka gabata, mun yi wa ’yan kasa alkawarin canji na hakika a cikin dukkan abun da za mu yi da yadda za mu yi shi. ’Yan kasa kuma sun aika da bayyanan nan sako a zaben da ya gabata kuma ta dandalin mu aka samar da wani shirin sabon buri da zai kubutar da kasar nan kan mawuyacin halin da take kuma ta zama ta fita daga matsalar cin hanci da rashawa, in ji shugaba Buhari.

Shugaban ya ci gaba da gaya wa ’yan kasa cewa “mun yi aiki tukuru wajen ganin cika alkawurran da muka dauka, duk kuwa da yake hanyar cike take da matsaloli a cikin shekaru 3 da rabin da muka yi, amma duk da haka mun  shinfida harsasan da za su inganta kasar nan da mafi yawan mutanenta.” Da ma ita gwamnatin Muhammadu Buhari abu 3 ta yi alkawarin yi, wato yaki da cin hanci da rashawa da rashin zaman lafiya musamman rikici irin na ’yan kungiyar Boko Haram da sai da ya game kusan dukkan sassan kasar nan, har ma ya tsallaka kasashen makwabta da kuma batun farfado da tattalin arzikin kasa. Bisa ga wadannan alkawura 3, masu nazarin siyasar kasar nan suke ganin duk wanda zai auna mulkin shugaba Buhari to ya auna shi da wadannan abubuwa guda 3.

Shi ma a cikin nasa jawabin Ministan Ayyuka da Makamashi da Gidaje Babatunde Raji Fashola, cewa ya yi a yanzu maganar da ake akwai ayyukan gina hanyoyi daban-daban har 360, da ake gudanar da su a lokaci guda a dukkan jihohi 36 da Abuja babban birnin tarayya. Ya kara da cewa 244 daga cikinsu gwamnatin Buharin gadarsu ta yi daga gwamnatocin da suka gabata, yayin da ita kuma ta fara 121, a cikin wannan shekaru 3 da rabi da take kan mulki.

Kazalika Minista Fashola ya fadi cewa a kokarin da gwamnatin take yi na cikasa gibin karancin gidajen da ake da su a kasar nan, gwamnatin ta dukufa wajen gina gidaje a jihohi 34. Shi ma Ministan Sufuri Cif Rotimi Amaechi ya fada wa taron cewa lokacin da shugaba Buhari ya nada shi Minista a shekarar 2015, babban abin da ya gargade shi, shi ne lalle kar ya kuskura ya fara sabon aiki a ma’aikatar, har sai ya kammala raya kasar da ya gada daga gwamnatocin baya.

A wajen taron dai an nuna wani takaitattacen majigi da ya kunshi wasu daga cikin ayyukan raya kasar da shugaba Buhari ya gudanar, da suka hada da gina hanyoyi da tallafi don inganta rayuwar jama’a da aikin gona da na yakin cin hanci da rashawa kai har ma da na tsaro.

Kamar yadda na ambata a sama a zaben na badi akwai ’yan takarar neman shugabancin kasa har 79, amma ’yan kasa baki daya sun fi mayar da hankali a kan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da kuma ta dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP wato tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, wadanda bayan kasancewarsu ’yan arewa ne Hausa/Fulani, kuma musulmi, hakazalika kowanennsu ya yi aikin damara, ba ko shakka zai rage tunanin masu tunani daga kowane bangare na kasar nan a kan wa za a zaba. Amma dai babban abin la’akari da kuma fatan da wannan fili yake da shi, ’yan kasa su tsaya su yi kyakkyawan nazari tare da rokon Allah Ya ba su ikon zaben wanda zai fid da kasar da muatenta daga irin mawuyacin halin rayuwar da ake ciki.