✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Buhari ya bude titin Naira biliyan 3.3 a Jihar Katsina

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bude wani titi mai tsawon kilomita 32 da Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta gina…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bude wani titi mai tsawon kilomita 32 da Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta gina domin saukaka safarar jama’a da  kayayyakin amfanin gona a jihar.

Hanyar wadda ta tashi daga  Shinkafi zuwa ’Yandaki zuwa Gafia da Abdallawa da Dankaba, ta ratsa ta kauyuka 15 a kananan hukumomin Katsina da Kaita da ke jihar.

Mazauna yankunan karkarar sun halarci lokacin da aka kaddamar da fara aikin gina hanyar, wanda aka yi a watan Oktoban 2017, sannan aka kammala a Afrilun bana.

A tsokacinsa lokacin da yake bude hanyar, Shugaba Buhari ya jinjina wa Gwamnatin Jihar Katsina game da gudanar da aikin wanda ya ce ya yi daidai da muradun gwamnatinsa na kawo sauyi a kasar nan.

Ya ce baya ga saukaka zirga-zirgar jama’a, hanyar za ta kuma inganta rayuwar al’umommin yankin.

Da yake mayar da jawabi a yayin bude hanyar, Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce Shugaba Buhari zai kuma bude wasu hanyoyin biyu da gwamnatin ta gina.

Gwamna Masari ya ce gwamnatinsa ta kammala gina tituna 13 da ta gada daga tsohuwar gwamnati, kana tana kan gina wasu sababbi guda 44.

“Aikin gina hanyar mai tsawon kilomita 32, ya lashe Naira biliyan 3 da miliyan 362 da dubu 292 da 219 da kwabo 25. Haka kuma aikin hanyar Fargo zuwa Katsayal zuwa Kwasarawa da Jirdede da Koza mai tsawon kilomita 38 da kuma na Kwanar Sabke zuwa Dan’aunai da Ruwan Kaya mai nisan kilomita 22 sun lashe Naira biliyan 1 da miliyan 909 da dubu 827 da 28 da kuma Naira biliyan 2 da miliyan 601 da dubu 552 da 756. Wadannan tituna biyu, su ma Mai girma Shugaban Kasa ne zai bude mana su cikin yardar Allah,” inji Gwamna Masari.