✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Faransa na samun matsin lamba kan badakalar abokiyar zamansa

Shugaba Francois Hollande na kasar Faransa, ya bayyana cewa yana cikin wani mawuyacin hali, ganin yadda ake bibiyar harkokin rayuwarsa, inda wasu ke ganin yana…

Shugaba Francois Hollande na kasar Faransa, ya bayyana cewa yana cikin wani mawuyacin hali, ganin yadda ake bibiyar harkokin rayuwarsa, inda wasu ke ganin yana da abokiyar zama, kuma yana da farka. Don haka abokan huldar siyasarsa suka bukaci kan lallai ya warware wannan badakala, ko da ta kama a samu Uwargida da faraka, a muhalli daban-daban.
Abokiyasr zaman Shugaba Hollande, wadda ’yar jarida ce, mai suna balerie Trierweiler, ta kamu da rashin lafiya har an kwntar da ita a asibiti, bayan da wata mujalla ta buga hoton shugaban da wata farkarsa, Julie Gayet, ‘yar fim.
Bayan ya kammala jawabi kan tsare-tsaren tattalin arzikinsa, a ranar Talatar da ta wuce, wata mujalla ta ruwaito cewa an tambayi Hollande kan lallai ya tantance kowace ce uwargidansa, tsakanin wadannan mata biyu da yake hulda da su, sai ya bayar da amsar cewa, kowacensu ta shi ce, kuma duk rayuwarsu na cikin wani mawuyacin hali, “wannan shi ne halin da muka samu kanmu a ciki.”Inji shi.
Hollande ya ce damuwarsa, a kan rahoton shi ne “yadda ake ’yanci.” Ya ki kuma bayyana sahihancin rahoton.
Shugaba Hollande ya yi alkawarin warware badakalar, don a san kowacce ce uwargida mai daraja ta daya, nan da ranar 11 ga fabrairun bana, kafin ya kai ziyarar aiki zuwa kasar Amurka.
Francois Rebsamen, wani dan jam’iyyar gurguzu a majalisar kasar Faransa, wanda kuma na hannun damar Shugaba Hollande ne, ya bayyana cewa batun uwargidan shugaban kasa, wani abu ne da ya kamata a ce an yi watsi da shi tuni.
Dominikue Moisi, masanin siyasar Faransa, ya bayyana cewa Shugaba Hollande ya zama shugaban kasar Faransa mara farin jini, domin a wannan zamani na ci gaba, ya jawo wa kansa ana ta bibiyar rayuwarsa.