Search
Subscribe
Shugaban Gabon ya bayyana bayan shekara da shanyewar barayin jikinsa

Shugaban Gabon ya bayyana bayan shekara da shanyewar barayin jikinsa

…Ya nemi a sake zabensa a 2023

Shugaban kasar Gabon, Ali Omar Bongo ya bayyana a bainar jama’a bayan shanyewar bangaren jiki da ya yi fama da ita a watannin baya.

Bongo wanda ya halarci babban filin wasa na Nzeng Ayong da ke Librebille, babban birnin kasar, ya nemi cincirindon jama’ar da suka taru su sake ba shi damar ci gaba da mulkar kasar zuwa shekarar 2023.

Bongo wanda ya karbi mulki daga mahaifinsa Shugaba  Omar Bongo, wanda ya mulki kasar na tsawon shekara 42 (1967 – 2009), yanzu ya shafe shekara 10 kan karaga kuma yana neman ci gaba da rike madafun iko a kasar mai arzikin man fetur – duk da rashin lafiyar da yake fama da ita.

Shugaban mai shekara  60, yana fama da matsalar furta magana da ta tafiya, sai dai  a ranar Asabar da ya bayyana – jami’an tsaro ne suka kewaye shi kuma sun kasance su ne masu tallafe da shi. Sai dai bangaren ’yan hamayya a kasar sun bayyana Shugaba Bongo a zaman wanda ba zai iya aiwatar da ayyukan ofishin Shugaban Kasar ba, idan dai har ya sake samun damar mulkar kasar.

Wata kotu a kasar na sauraren karar da aka shigar game da hakan. Kamar dai yadda kafar labarai ta Bloomberg ta ruwaito.

“Ya Ali”, “Ali, mai girma,” kamar dai yadda magoya bayansa suka rika fada a cikin filin wasan inda shi kuma ya amsa da “Ga ni a nan, ina nan ne dominku, kuma zan ci gaba da kasancewa nan dominku a kullum.” Ya ci gaba da cewa, “Kuma ba za ku iya fahimtar irin farin cikin da nake ji kasancewa  tare da ku ba.”

A yayin da Shugaban ya nuna alamun gazawa da tafiyar da mulkin kasar, a daya hannun kuma Shugaban Majalisar Ministocinsa ne yake kara-kaina wajen tafiyar da iko a larduna tara na kasar a madadin Shugaba Bongo.

Shugaba Bongo ya yi fama da shanyewar bangaren jiki a ranar 24 ga Oktoban 2018, yayin da yake halartar wani taro a kasar Saudiyya. Ya shafe watanni yana jinya a kasar Moroko; inda ya samu kulawa ta farko gabanin  ya koma gida, Gabon.

Idan dai za a iya tunawa ko a shekarar 2013, Shugaban Kasar Aljeriya na wancan lokaci Abdelaziz Bouteflika, ya yi fama da kwatankwacin haka; inda duk  da da shanyewar bangaren jikin da ya yi, ya nemi da a sake zabarsa karo na biyar. Sai dai hadin gwiwar ’yan adawar kasar da kuma na rundunar sojin Aljeriya sun tilasta masa sauka daga mulki.

Makonnin da aka shafe anata gudanar da  zanga-zanga kan titunan kasar ya haifar da nasarar korar Shugaba Bouteflika mai shekara 82, wanda ya shafe shekara 20 a kan karaga.

Mista Bouteflika ya ci gaba da zama Shugaban Kasar na tsawon shekara shida duk da matsalar shanyewar bangaren jikinsa. Sai dai ya kaurace  wa fitowa bainar jama’a. Masu lura da al’amura na ganin watakila hakan ne yake ingiza Shugaba Bongo; sai dai bisa alama akwai yiyuwar a kwata irin abin da ya faru a kasar ta Aljeriya.

Dama a bisa tsarin zaben kasar, ana zabar Shugaban Kasa ne ta hanyar zaben kai tsaye – na wanda ya fi samun kuri’u mafiya rinjaye – kuma zai yi mulkin shekara bakwai rigis.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin