✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Gabon ya koma gida

Rahotanni sun ce  Shugaban Kasar Gabon Ali Bongo wanda ya bar kasar tun ranar 24 ga Oktoban bara saboda rashin lafiya ya koma kasarsa domin…

Rahotanni sun ce  Shugaban Kasar Gabon Ali Bongo wanda ya bar kasar tun ranar 24 ga Oktoban bara saboda rashin lafiya ya koma kasarsa domin ci gaba da mulki.

Kafafen watsa labarai na  kasar Gabon suka ruwaito haka.  Sakamakon zabubbukan da aka gudanar a ranakun 6 da 27 ga watan Oktoba, Shugaba Bongo ya nada Julien Nkonghe Bekele a matsayin Firayi Ministan kasar.

Bayan nadin Bekale an kuma nada Babban Sakataren Jam’iyyar Democratic Party da ke mulkin kasar  Faustin Boukoubi a matsayin Shugaban Majalisa.

Bongo wanda ke jan ragamar kasar tun watan Oktoban shekarar 2009 ya fada hadu da rashin lafiya bayan ya ziyarci wani taro da aka gudanar a Saudiyya a ranar 24 ga watan Oktoba, inda aka kwantar da shi a asibiti.

Jim kadan sai aka samu labarin cewa ya samu bugun zuciya, sannan an yi masa aiki ya kuma kwanta a asibiti na  kwanaki daga bisani Sarkin Moroko Muhammed na Shida ya gayyace shi inda ya ziyarci Rabat a ranar 29 ga watan Nuwamba.

An sallami Bongo ne daga asibiti a ranar 6 ga watan Disamba, amma sai ya zabi  ya kasance a Rabat babban birnin Moroko.

Idan ba a manta ba, mun kawo muku yunkurin kifar da gwamnatinsa a kwanakin baya, duk da cewa matasan da suka yi wannan yunkuri sun gaza, domin an kama su, an kashe wadansu daga cikinsu kan cin amanar kasa.

Sannan ana tunanin zai yi wuya a kifar da gwamnatinsa ganin cewa yawancin jami’an tsaron kasar da manyan masu rika da madafun iko kusan ’yan uwa ne ko kuma na kusa da iyalan gidan Bango, wadanda suka mulkin kasar na kusan shekara 50 a jere.