✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban gwamnatin riko na Sudan ya sauka

Ministan tsaro Awad Ibn Auf ne ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin a tashar talabijin ta gwamnatin Sudan, ya kuma bayyana Laftana Janar Abdel…

Ministan tsaro Awad Ibn Auf ne ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin a tashar talabijin ta gwamnatin Sudan, ya kuma bayyana Laftana Janar Abdel Fattah Abdelrahman Burhan a matsayin wanda zai gaje shi, kamar yadda BBC ta kalato

Wannan matakin ya biyo bayan turjiyar da masu zanga-zanga a kasar suke nunawa ne na kin amincewa da sabbin shugabannin, inda suke tuhumarsu da hannu cikin rikicin da ya dabaibaye kasar.

Sojojin Sudan sun yi alkawarin shirya zabe kuma su mika mulki bayan shekara biyu ga sabuwar gwamnati ta fararen hula.

Tsohon shugaba Omar al-Bashir ya rasa mukaminsa ne bayan da aka shafe watanni ana zanga-zangar nuna kiyayya ga mulkinsa. Akalla mutum 38 ne suka rasa rayukansu a lokacin zanga-zangar da aka yi a fadin kasar.

Shi kuma Awad ibn Auf ya rike mukamin kwamandan sojojin masu leken asiri na cikin gida a lokacin yakin da aka yi a yankin Darfur a shekarun 2000, kuma Amurka ta kakaba masa takunkumi a 2007.

Kotun manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ke birnin Hague ta tuhumi Mista al-Bashir da laifukan yaki da kuma laifukan cin zarafin bil Adama a dalilin wancan rikicin na Darfur.