✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Hukumar kula da Shirya Fina-finai ta kasa ya ziyarci Kano

A makon jiya ne sabon Shugaban Hukumar Shirya Fina-finai ta Najeriya (Nigeria Film Corporation) Mista. danjuma W. Dadu ya kawo ziyarar aiki ta kwana daya…

A makon jiya ne sabon Shugaban Hukumar Shirya Fina-finai ta Najeriya (Nigeria Film Corporation) Mista. danjuma W. Dadu ya kawo ziyarar aiki ta kwana daya Kano, inda ya gana da masu sana’ar shirya finan-finan Hausa.
Ya ce, makasudin ziyarar shi ne don ya gabatar da kansa ga masu wannan sana’a a Kano a matsayin sabon shugaban hukumar masu shirya fina-finai ta Najeriya.
Ya ce: “Daga nan zan kai irin wannan ziyara Legas da Enugu, amma na soma da Kano ne saboda irin rawar da fina-finan Hausa suke takawa a kasar nan.”
‘Yan fim sun gabatar da korafinsu hade da ba da shawarwari don ciyar da sana’ar gaba.
Mista Dadu ne ya canji Mista Afolabi Afolayan ne wanda ya kammala wa’adinsa. Mr. Dadu dai, injiniya ne, kuma malamin jami’a ne a fannin gine-gine a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.