✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kaduna ya lashe zabe a karo na biyu

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kaduna Sharrif Abdullahi Kassim ya sake lashe zaben shugabancin hukumar bayan ya kada abokin takararsa, Sani Abdullahi. Zaben, wanda…

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kaduna Sharrif Abdullahi Kassim ya sake lashe zaben shugabancin hukumar bayan ya kada abokin takararsa, Sani Abdullahi.

Zaben, wanda aka gudanar a Otel din Wonderland da ke  Kafanchan a ranar Asabar da ta gabata, Sharif Kassim ya samu kuri’a 16 yayinda abokin fafatawarsa ya samu kuri’a 11.

Sauran mukaman da aka fafata sun hada da na mataimakin shugaba, inda Magaji Alhassan ya yi nasarar lashewa da kuri’a daya kacal inda ya samu kuri’a 14 yayin da Abdullahi Balarabe ya zo na biyu da kuri’a 13.

Yayin da yake jawabi bayan bayyana nasararsa, Sharif Abdullahi ya gode wa wakilan da damar da suka sake ba shi inda ya yi alkawarin cicciba hukumar zuwa mataki na gaba tare da alwashin tafiya da kowa a cikin hukumar don samun nasara.

Sannan ya yi kira ga sauran membobin da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a jihar da hada hannu don tallafawa harkar wasan kwallo a jihar.

Yayin da yake gabatar da nasa jawabin tun da farko, wakilin shugaban hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF), Mista Emmanuel Adesanya ya bukaci wakilai masu zabe da su nuna halin dattaku a lokacin da kuma bayan kammala zabukan.

Daga cikin wadanda suka halarci zaben akwai Alhaji Ahmed Yusuf (Fresh) da Alhaji Muhammed Alkali da shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Filato, Sunday Longbab da kuma tsohon Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kaduna Honorabul Daniel Dan Auta.