Da Dumi Dumi

Shugaban Kamfanin Air Peace ya musanta zargin da Amurka ke masa

Mista Allen Onyema
Mista Allen Onyema

Shugaban Kamfanin Jiragen Sama na Air Peace Mista Alle Onyeama ya musanta zargin da kasar Amurka take  masa na almundahanar Dala miliyan 20.

Allen Onyeama a kwanakin baya tauraronsa ya kara haskaka lokacin da ya kwaso ’yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu a jiragensa kyauta lokacin da rikicin kyamar baki ya yi zafi a kasar.

A sanarwar da Amurka ta fitar, ta ce tana zargin Onyeama da fitar da kudi daga Najeriya zuwa wani bankin Amurka ta amfani da takardun karya domin sayo jiragen. Sannan sanarwar ta ce Onyeama ya bude asusun ajiya a Amurka da dama, sannan ya tura Dala miliyan 44.9 a wani asusun ajiyarsa da ke Jihar Atlanta. Kuma tare da taimakon Misis Eghagha sun sake tura Dala miliyan 20 a asusun ajiyar.

A farkon bana ne Kamfani Air Peace ya sayo sababbin jirage kirar Embraer 195-E2 guda 10 daga kasar Brazil a kan Dala miliyan 212.6.

Da yake jawabi kan lamarin, Allen Onyeama ya musanta zargin, inda ya ce a shirye yake ya kare kansa kan zargin almundahanar kudi a Amurka.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, “Ba ni da laifi a duk abubuwan da ake zargina a Amurka. Tun asalina ba na harkokin kasuwanci a boye ko cuwa-cuwa. Don haka a shirye nake in kare kaina daga duk abin da ake zargina.”

A kwanakin baya ne Majalisar Wakilai ta gayyaci Allen Onyeama, inda ta girmama shi saboda kokarin da ya yi wajen kwaso ’yan Najeriya da suke kasar Afirka ta Kudu, girmamawar da ya ce ba zai taba mantawa ba.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya