✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kasa ya sallami Shugabar Ma’aikata ta Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba Shugabar Ma’aikata ta Kasa, Misis Winfred Ekanen Oyo-Ita umarnin ta tafi hutun dole, sannan ya umarci Babbar Sakatariya a…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba Shugabar Ma’aikata ta Kasa, Misis Winfred Ekanen Oyo-Ita umarnin ta tafi hutun dole, sannan ya umarci Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Man Fetur, Dokta Yemi-Esan ta rike mukaminta.

Haka kuma Shugaba Buhari ya amince da karin wa’adi ga manyan sakatarori guda bakwai da ya kamata su yi ritaya zuwa shekara daya.

A  takarda da Daraktar Labarai a Ofisin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Willie Bassey ya sanya wa hannu, ta ce an cire  tura Shugabar Ma’aikatan hutu ne domin a ba Hukumar EFCC dama ta yi binciken da take yi a kanta.

Tsohuwar Shugabar Ma’aikata Oyo-Ita ana binciken ta ce kan zargin kwangilar Naira biliyan 3.

Kwanakin baya Hukumar EFCC ta gayyace ta,  inda aka yi mata tambayoyi sannan aka bayar da belinta saboda matsayin da take rike da shi.