✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Kungiyar asiri mai ido daya ya shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun tayi nasarar kame wani matashi mai ido daya da ake zargi da kasancewa jagoran kungiyar asiri ta Eiye a yankin…

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun tayi nasarar kame wani matashi mai ido daya da ake zargi da kasancewa jagoran kungiyar asiri ta Eiye a yankin Ikenne a jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan a jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa, wanda ake zargin mai suna Sunday Paul da ake yi wa lakabi da Reza kasurgumin dan kungiyar asiri ne da ya hallaka sama da mutum 15.

Ya ce, bai jima da fito wa daga gidan yari ba, bayan an kama shi aka kai shi kotu inda aka tuhume shi da laifukan da suke da nasaba da kisan kai, “A binciken da muka kayi a kan sa ya shaida mana cewa shi ne ya kashe wani abokin hamayyar sa mai suna Kabiru wanda shima dan kungiyar asiri da basa ga maciji da juna, al’ummar garin Ikenne sun yi ta son ganin yadda jami’an mu suka kame kasurgumin dan kungiyar asirin a ranar 21 ga watan jiya domin ya addabe su.” in ji shi.

Ya ce, ana ci gaba da bincike kafin daga bisani a gurfanar da shi a kotu.