✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban kungiyar asiri ta ‘EFCC Boys’ ya shiga hannu

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame shugaban kungiyar asiri ta ‘Eiye Confraternity’ da ke kiran kansu ‘EFCC Boys’, mai suna Olumide Ogbor, wadanda ake…

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kame shugaban kungiyar asiri ta ‘Eiye Confraternity’ da ke kiran kansu ‘EFCC Boys’, mai suna Olumide Ogbor, wadanda ake zarginsu da kashe jama’a da kuma lalata dukiyoyi masu yawa a unguwar Somolu da Bariga da kuma Akoka a jihar  ta Legas.
Aminiya ta gano cewa a ranar 9 ga watan Afrilun da ya gabata, gungun matasan sun kona motoci fiye da 100, sannan sun yi wa da dama rauni lokacin da suka kai harin ramuwar gayya unguwar Akoka da Pedro da ke karamar Hukumar Somolu.
Haka nan a watan jiya sun kai hari unguwar Sele da Oshodi da Mushin da kuma Mil-2, inda suka farfasa motoci tare da yin harbin kan mai-uwa-da-wabi.
Rahotannin sun nuna cewa mutane da dama sun ji munanan raunuka sakamakon harin da suka kai a wasu layuka da ke cikin karamar hukumar ta Mushin.
Wata majiya ta bayyana cewa ana zargin Olumide da kashe wasu matasa a wurin wani bikin a unguwar Onipan tare da yi wa da dama rauni, kuma tun daga lokacin ’yan sanda suke nemansa ruwa-a-jallo.
Majiyar ta ce an kama Ogbor a ranar Lahadi a yayin da yake kokarin yi wa wasu jerin motoci fashi a unguwar Onipanu.
Mai magana da yawun rundunar tsaro ta musamman (FEDSRARS), Lekan Ogundare, wanda ya tabbatar da kamun ga manema labarai, ya ce suna gudanar da binciken zargin fashi da kuma kisa, kuma za su mika shi gaba da zarar sun kammala bincike, ba tare da bata lokaci ba.