✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Majalisa ya zama Mukaddashin Gwamnan Kaduna

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Alhaji Aminu Shagali ya zama Mukaddashin Gwamnan Jihar, sakamakon hutu da Gwamna Nasir El-Rufa’i da Mataimakiyarsa Hajiya Hadiza Balarabe ke…

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Alhaji Aminu Shagali ya zama Mukaddashin Gwamnan Jihar, sakamakon hutu da Gwamna Nasir El-Rufa’i da Mataimakiyarsa Hajiya Hadiza Balarabe ke yi.

Gwamna Nasir El-Rufa’i da Mataimakiyarsa sun fara hutun karshen shekara wanda hakan ya sa suka fice daga kasar nan.

Majiyarmu a Gidan Gwamnati ta ce Gwamna ya dawo kasar ne makon jiya domin ya halarci bikin auren ’yar Mataimakiyarsa da aka yi a ranar Asabar da ta wuce.

Bayan bikin ya sake ficewa daga kasar inda ita ma Mataimakiyarsa aka ce ta fice daga kasar domin zuwa hutu.

Sakamakon haka ne suka mika mulkin jihar ga Shugaban Majalisar Jihar kamar yadda dokar ta tanada.

“Bayan an daura auren ne ya sake ficewa daga kasar ita ma Mataimakiyarsa ta tafi hutun karshen shekara.Mukaddashin Gwamnan Jihar ya fara aikinsa ne a ranar Litinin da ta gabata, inda ya tarbi ayarin wadanda za su wakirci jihar a gasar Musabaka ta Kasa a Gidan Gwamnati,” inji majiyar.

Majiyar ta ce  Shagali ne zai rika wakiltar Gwamnan tare da tarbar baki har zuwa lokacin da Gwamnan ko Mataimakiyarsa za su kammala hutunsu.

Kakakin Gwamnan, Muyiwa Adeleke ya ce Gwamnan ya mika mulkin ne ga Shugaban Majalisar kamar yadda doka ta tanada. “Hakan ya taba faruwa a farkon zangon mulkin Malam El-Rufa’i,” inji shi.