Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shugaban Majalisar Dattawa ya yi karin haske akan nadin Ministoci

Ahmad-Lawan Shugaban Majlisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, a yau Laraba ya bayyanawa zauren majalisar cewa, akwai yi yuwar zauren majalisar ya karbi jerin sunayen wadanda Shugaba Buhari zai nada mukaman Ministoci, kafin karshen wannan makon da muke ciki.

Lawan, din a sa’ailin da yake jawabi bayan da Sanata Albert Bassey Akpan daga jihar Akwa Ibom, ya ja hankalin zauren majalisar a kan wannan batun, ya ce bangaren na zartarwa na aiki tukuru wajen fito da sunayen sabbin Ministocin.

ADVERTISEMENT

Sanata Akpan ya bayyana bukatar cewa, kamata ya yi shugaba Buharin ya aike da sunayen Ministocin ba tare da bata lokaci ba, saboda a cewarsa, nan ba da jimawa ba, za su fara hutunsu na shekara.

Sai dai shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya ce a bisa bayanan da ya samu daga wasu manyan jami’an gwamnatin, jerin sunayen mutanen da za a nada ministocin zai samu kafin karshen makon nan da mu ke ciki ne.

ADVERTISEMENT